← Book details Heart Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 29

Sashe 4

Heart Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kina so in zubar damu a motar nan ko?” Ta girgiza kai, ita tafi kowa sanin yadda Zayyan baya son kukanta don fitar dashi yake a hayyacinsa. Amma yau dole tayi kuka a gabansa. Ashe-ashe itace mai matsalar! Kukan nata ya karu, fiyeda na baya. Ba shiri Zayyan ya faka motar a gefen titi. “Sophie, so kike ki daga min hankali akan abinda banida ikon baki shi ko? So kike in dorawa kaina damuwar gazawata da kasawata ga baki farin cikin da kike so?” Safiyyah ta girgiza kai tana share wasu hawayen da suka kawo mata caffa da gefen gyalenta, tace “ba haka bane Habiby, inaso ne ko yaya ne nima in ga dan kaina, wanda zai zama fruit to our love. Nima in zama UWA inyi experiencing abinda ake ji a motherhood. Shekaruna kullum gaba suke yi, har gashi ina neman dosar shekaru talatin banida Da ko daya. Kuruciyarmu kullum karewa take yi, ba baya take komawa ba. In ban haihu yanzu ba sai yaushe Habiby? Sai na kai menopause? Banida sanyin idaniyar da kowa ke alfahari dashi wato DA. Banida bakin da zan kira kaina Maman wane ko Maman wance. Kaima da kanka Zayyan watarana zaka tsaneni, tunda na kasa maida kai UBA. Ta hanyar ajiye maka abinda kowanne uba ke fatan samu”. Karo na farko da yaji Safiyyah ta kirashi da suna ZAYYAN wanda ya nuna tashin hankalinta a fili yake, bata ma san ta fada ba, a kwanakinnan ya fahimci Safiyyah ta zama desperate ga son haihuwa kadai. Zayyan ya rungumo Safiyyah sosai a jikinsa, ya ma manta a kan hanya suke, ya sumbaci saman goshinta zuwa karan hancinta, ya ja birki yayi togaciya a lips dinta, inda yayi mata kykkyawar sumba mai zurfi. Yace “Sophie ni ba abinda zaisa na tsaneki, haba Safiyyah, haba Sophie na, nifa Safiyyah na aura ita kadai bada tunanin zata haihu min ko bazata haihumin ba. Ta yaya kuma don baki haihu ba sai in tsaneki akan lalura, bayan daidai gwargwado nasan cewa Allah ke bada haihuwar nan? Kada ki kara wannan shirmen tunanin bana so, abinda ni Zayyan na yarda dashi shine haihuwa ta Allah ce, da ya bamu da bai bamu ba you will forever remain my alter ego!” Da haka yayi ta lallashinta har ya samu tayi shiru tana ajiyar zuciya a kan kirjinsa. Can kuma tace “Habiby, babbar damuwata itace PCOS dinnan yanada magani ne ko a’ah, ni da ace ma tace unexplained infertility kadai ne, sai inga kamar zan fi samun sauki a raina fiye da ace mun PCOS gareni. Ni ban gamsu da binciken wannan likiciyar ba, don a tarihin zuri’ar gidanmu kaf! Babu mai PCOS”. Zayyan yace da karfafawa “to hell with PCOS and whatever! Ni Zayyan Sophie kawai nake so, haihuwa in Allah ya kawo ina maraba da ita, haka in bai bamu ba, muna cikin godiyarsa as well. Ya hada hannuwansa biyu yana rokonta. “Chapter closed, don Allah Sophie. Bana son kara jin zancen haihuwa a bakinki daga yau. Kuma kada ki kara kai mu gaban Likita”. Amma ina! Safiyyah bata hakura ba saida tayi bincike ta hanyar tuntubar wadanda ta sani akan kwararriyar likiciyar matan da tafi kowa kwarewa a Arewa, nan aka bata labarin Dr. Hadiza Shehu Galadanci, ta jihar Kano. Ta samu labarin Dr. Galadanci ne ta hanyar Anti Dije, ta kudire in ta samu Zayyan ya kaita Zaria bikin Ni’iman Anti Dije sai ta biya Kano ta ga Dr. Galadanci tunda kwana uku zata yi a Zaria. Watakila Dr. Shinkafi bata san aikinta ba, ita a zuri’ar su Ammi ba mai PCOS, kuma ance shi mostly gado akeyi. Hakan ce ta faru. Lokacin bikin diyar Anti Dije Safiyyah ta samu Zayyan ya kaita har Zaria, daga nan sukayi sallama shikuma ya wuce Katsina gun su Mama, a can zaiyi hutun karshen mako, ita kuma ta ci biki a cikin ‘yan uwanta, duk da bata da walwala, ga kannenta duka sun zo suma daga Dandume. Biki yayi biki gida ya cika da dangi da abokan arzikin su Anti Dije, ita da su Sabah daki daya suka kwana, washegarin saukarta a Zaria Safiyyah sai ta zare jiki ta tafi Kano ita kadai ba tareda Zayyan ko wani nata ya sani ba, ta hau motar Kanoline daga Zaria, daga nan ta nufi asibitin Standard da Anti Dije ta bata labarin a can aka yi mata maganin barin ciki data yi ta yi shekarun baya . Da tambaya da taimakon wayewar kanta sai ga Safiyyah akan layin mata masu son ganin Dr. Galadanci. Bata sha wahalar samun asibitin Standard ba, saboda babban asibitin kudine da yayi kaurin suna ga matan Kano. Duk da Sophie bata taba zuwa Kano ba sai wannan karon. Hakan bai sa ta rikice ba. Mai Keke Napep ta dauka drop tace ya kaita Standard na Tarauni. Shikuma da yake ya riga yasan asibitin nan da nan ya kaita ya zabga mata kudi. Safiyyah ta bude file ta biya duk abinda aka cajeta na ganin Prof. Dr. Galadanchi, kasancewar Safiyyah sammako tayi bana wasa ba, daga Zaria zuwa Kano, yasa karfe goma na safe ma tana cikin garin Kano. Aka dorata akan layin da mata uku ne kacal a gabanta. Ta samu kujera ta zauna a waiting lounge na ganin likiciyar, bata dade da zama ba wata farar mata da ba zata fice tsararta ba itama tazo ta zauna a kusa da ita, bayan tayi wa Safiyyah sallama. Sai zuba kamshin Humra matar take. Suna nan zaune matar na amsa waya lokaci-lokaci, can kuma ta jefa wayar a kyakkyawar Jakarta, cike da shishshigi ta dubi Sophie, don taga kalar hutu sosai a jikinta itama, ita kuma dama da irin kalar wadanda take kawance kenan, sai ta hau jan Sophie da hira kadan-kadan babu alamu na bakunta, ko irin yau ta fara ganinta dinnan. “Baiwar Allah sannu fah. Na ce sannu fah. Halan kema matsalar rashin haihuwa ce ta kawo ki ganin Dr. Galadanchi?” Safiyyah sai da taji gabanta ya fadi, matar tayi murmushi ganin irin kallon da Sophie tayi mata na mamaki, sai tace, “yo meye abin mamaki don na canki matsalarki? Ai daidakun mata ne ne da sukazo Standard da ba matsalar data kawo su kenan ba, musamman masu fama da lalurar (PCOS)”. Sophie ta bita da kallo kawai, don bata ma san menene ‘PCOS’ din ba ita har yau, bata taba jinsa ba, sai a bakin Dr. Muwadda Shinkafi. Ta ce a ranta, “wasu matan dai Allah ya zuba musu surutu da shiga sharo ba shanu!”. Matar bata san tunanin da Sophie ke yi a kanta ba, ta cigaba da cewa. “Alhalin basu san cewa wahalar da kansu kawai suke yi a banza ba. Ni dinnan da kike gani wane kalar asibitine banje neman haihuwa ba, kasashen duniya manya da kanana babu inda bamu taka don neman haihuwa ba nida maigida na. Mun zubar da dukiya da lokacinmu kamar me a yawon asibiti, duk a banza. A karshe dole nabi hanyar da ta bulle dani, yanzu haka yara na biyu. Wannan zuwan kuwa na zo ne likita ta rufe min bakin mahaifa in samu in huta da haihuwar haka ko na shekara biyu ne, yarana kuma su kara girma”. Safiyyah sakin baki tayi tana kallon matar, wadda ta laqawa suna “fadi ba’a tambayeki ba”. Hankalinta ya dan fara daukuwa ga abinda matar take labarta mata, amma bata gane zaurancen hanyar da take nufi ta bi, wadda ta bulle da ita din ba. Zata so taji wannan kowacce irin hanya ce, da har haihuwar tazo ta isheta tana neman dakatarwa, ko itama ta gwada, ko Allah zai sa ta dace. Safiyyah sai ta saki jiki da matar nan wadda tace sunanta Ammara, nan suka shiga hirar haihuwa, kamar sun dade da sanin juna, abinki da irin ka gamu da mai irin ciwonka, wanda ya rigaka samun waraka. Ammara tace “shekaruna ashirin da aure kafin na samu haihuwar yaran da nake dasu yanzu. Kema kinsan mun sha damuwa nida maigidan”. Safiyyah kuma tace “ita kuma shekara takwas kenan da aure, ko bari bata taba yi ba”. Sai hira ta kara mikawa tsakaninsu akan hakan. Ammara tace “haka kawai naji kin kwanta min a rai, gaki kyakkyawa ga kuruciya ga hankali, ga hutu, banda haka banida sakewa da bakin fuska sam. Naga damuwa baro-baro a tare dake, haka kawai yarinyar ki dake zaki bar ciwon damuwa ya kamaki a banza saboda haihuwar da samunta ruwan sha yafi ta saukin sha. ‘Yar uwa ki rabu da wani yawon asibiti ana cin kudinki a banza, kibi hanyar da zata bulle dake kawai. Rayuwar nan saida dan kaucewa sannan ake ganin daidai”. Ta kara saka Safiyyah a duhu, har ta kai da tambayarta “dan kaucewa kamar yaya shin? In ji dai ba kauce hanya ta addini ba?” Ammara tace “kusan hakane, amma ba sosai ba, zauna nan ‘yar uwa kiyita walagigin bin likitoci suna jagwalgwala miki mahaifa suna cika ki da surutan wofi, kuma basu da maganin da zasu baki ki haihun”. Nan ta bude wayarta ta nuna mata hotonta tare da maigidanta da kyawawan yaransu maza biyu kanana kamar haihuwar kwanika, nan ta kara brainwashing Safiyyah wadda a lokacin nan ba abinda ta dauka a matsayin farin ciki da kwanciyar hankalin dan adam sama da ‘ya’ya. Haka Ammara tayi ta kwance kan Sophie, tana kara zurmata ga bin irin hanyar data bi ta samu haihuwa. Wadda har zuwa lokacin ta ki fitowa fili ta fadeta sai indirectly take maganar. Allah sarki Sophie, ita da kanta bata san ta zama desperate ga son haihuwa ba sai yau. Ta yadda har ta dan rasa kyakkyawan tunaninta ta kuma kasa zurfafashi, tarbiyyar shekaru kusan 28 da ilmin addini da mahaifinta Malam ya bata basu sa ta yi tunanin meye ita wannan hanyar da ake ta muku-muku da ita ba’a fito da ita fili an gaya mata ba? Haka ilmin bokonta duk bai yi amfani a wannan lokacin ba. Biyan bukata kawai take nema. Ammara tayi nasarar yiwa Sophie famfo mai yawa a wannan danzaman nasu, har take ce mata ta rabu da zancen kawai na mijinta (Zayyan) da yake cewa shi bai damu ba, tace zance ne kawai na mazan da ke son kwanciyar hankalin matansu, karya yake yi yace wai bai damu da
Chapter 4 · 0% Book details