Sashe 9
Heart 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
THE STAMMERER Y au karo na biyu kenan da ganinsa da “Stammerer” (sunan da yaji malamin labiraren ya kirata kenan rannan bayan wucewarta), yau ma tazo dakin karatun kamar yadda ta saba, ta shige can kuryar da take zama, ya riga ya gane yanayin maganarta na halitta kenan (stammering) tun daga ranar farko da ya fara ganinta, wanda bazai gaji da cewa shi yafi komai daukar hankalinsa a kanta ba, fiye da kyawun surarta, ya kuma zame mata symbol a wurinsa, wanda duk inda yaji sautinta nan da nan yake gane itace, ko in yaji mai irinsa ya tuno ta, ya kuma fahimci cewa a tsangayar da yake ta ‘Architecture’ itama take karatu, saidai undergraduate student ce ba kamar shi da yake postgraduate student ba, ya gane hakan ne daga wannan littafin da tasa aka dauko mata rannan. Kullum yana shiga library ne don yin research da rubutu, baya son karatu cikin hayaniya sam, idan ya shiga yana samun can wata corner ne shima a can karshen dakin ya zauna inda ba’a iya ko hango shi sosai, baya son idan yana karatu a katse shi, shiyasa baya yin karatu a (tutorial) da ‘yan ajinsu. Hakan ya maida shi ‘regular visitor’ na library din, saboda a lokacin yana bincike yana rubutun (final project) dinsa na kammala digirinsa na biyu. Yana matukar shiri da Librarians da sauran ma’aikatan dakin karatun, idan ya shiga karatu sallah kadai ke fito dashi, wani lokacin zaka samu har gyangyadinsa yake yi in ya gaji da karatun a corner dinsa, duk da Zayyan mutum ne mara yawan sakin fuska ga mutane da karancin far’a, amma fuskarsa wani lokacin da walwala, ko babu far’a, hakan kuma baya nufin shi miskili ne, a’ah, kamewa ce kawai ta halitta da rashin son daukar wargi, duk da haka in dai zai ga ma’aikatan library din sai ya gaisa dasu cikin sakin fuska, wannan ne yasa duk suka saba da shi ya zama shima kamar ma’aikaci ne a cikinsu ba dalibi ba. Yanzu ya lura da wani abu, duk sanda ya shigo library ya zauna a corner din zamansa, yana yawan ganin wani (pink travel mug) a desk din da yake gaban nasa, mamallakiyar wannan ‘travel mug’ din itama ya lura ‘regular visitor’ ce kamar shi. Bayanta kawai yake iya hange kullum tana sanye da Hijab ko jilbaab. Har a ransa ya saka mata suna ‘Hijabie’ domin ya fuskanci ma’abociyar suturta jikinta cikin Hijabi ce, kullum cikin kyawawan Jilbaabs ko Hijabs yake ganinta, wata shiga da kannensa su Zahra sam basa yin kwatankwacinta. Kuma shigar ba karamin kyau take yi mata ba (a idonsa). Ba koyaushe yake ganinta ba amma dai tana yawan zuwa, idan ya hangi (pink travel mug dinnan) ya san ta zo kenan, koda bata wajen, to ta dan tashi zuwa sallah ne. Da alama shayi ko coffee ne mai zafi a ciki, kuma idan ta saka littafinta a gaba to ko juyowa bata yi. Ba ruwanta da duk abinda ke wakana a cikin library din. Sai ya kasance shikuma a rayuwarsa he’s in love with such kind of serious and decent charcter, shiyasa take burgeshi deep down inside him, yake girmamata a kasan ransa, ba tare da ya san kamannin fuskarta ba. Watarana ya shiga research kamar yadda ya saba, sai ya ga seat din ‘Hijabie’ babu kowa, sai ko ‘Pink Travel Mug’ dinta na gado ajiye a wurin. Sai yaji idanunsa na kewar ganin bayanta da ya saba gani in tana karatu, kawai yaji sha’awar zama a wajen nata, sai ya zauna (for a change). Don shi dai a duniya yarinyar nan da yanayin sutturarta da decent nature dinta, duk suna matukar tafiya dashi. Yana tsaka da aikin gabanshi sai yaji kamar tsayuwa a bayan shi. Ta zo zama a gurinta, sai taga wani zaune a gun, bayan kuma tayi shaida a wajen da littafinta da Mug dinta, sai ta tsaya kyam, ya dago a hankali ya dubeta. Nan da nan ya ganeta ashe yarinyar nan ce mai in’ina, ita keda Pink Travel Mug. Yayi mata sallama hade da murmushi, yace “na zauna miki a wajenki ko? Sorry!” Yana dagowa dinnan nan take ta gane shi, (her speech interpreter)!. Itama sai tayi murmushi, da sasssarfar maganarta tace “so, it is you?” "Ashe baki da mantuwar fuska?” Ta sake yin murmushi tace “Ba sai ka tashi ba, tunda ai wajen na kowa ne, babu mai (permanent seat) a wajennan, kawai sabo ne yasa nake zama anan din, bakomai Mr, bari na juya na nemi wani wajen, Nagode”. Sai ya hau tattara takardunsa daga kan desk din, yace mata “ayi haka? Hijabie, zo kiyi zamanki. Mai waje ya zo mai tabarma sai ya nade ko? Kayan aro baya rufe katara”. 'Yar dariya Safiyyah tayi tace. "bafa sunana Hijabie ba Mr. Library. Sunana Safiyyah Usman Dandume" Zayyan yace "madallah da Nana Safiyyah, ni kuma Zayyan nake, sunana Zayyan Bello, ba Mr. Library ba". Sosai ya bata dariya ta kuma yi zaman ta a wajenta daman tafi son wajen, ta saba da seat din sosai. In bai manta ba, daga nan tushen alaqarsu ya samo asali tsakaninsa da Sophie. And in no time, sabo mai tsanani ya shiga tsakaninsa da Safiyyah, kowanne ya shiga yaki da halinsa akan dan uwansa; abun nufi, Safiyyah ta cirewa kanta rashin kula mutane da rashin son yin mu’amala dasu akan Zayyan, shikuma ya cirewa kansa fuskar rashin walwala da sakin fuska in dai yana tare da Safiyyah a makaranta, to kuwa zai nemo walwala duk inda take ya sakawa kyakkyawar fuskarsa, a haka har suka fara sabawa outside library. Kasancewar duk suna karkashin tsangaya guda hakan yasa suna yawan haduwa shi da ita a department dinsu, kuma gashi sun fito jiha daya, sai suka kara zama abokan juna, kuma abokan karatu na sosai ga junansu. Duk da haka Safiyyah na kaffa-kaffa bata bari wata hira ta hadasu bata karatun da ya kawota ba. Shima kuma Zayyan Bello haka. Kullum kara wayar mata da kwanya yake akan dabarun dake cikin ilmi Zane. Har aka zo gejin da tafi jin dadin koyarwar Zayyan, fiye data dukkan Mallamansu. Bata san ma ya akayi shi ta saki jiki dashi har haka ba, alfarmar da bata yiwa kowanne da namiji a fadin jami’ar nan ba. Kai har mata ‘yan uwanta, Safiyyah bata sakewa dasu, kamar yadda ta samu kanta dumu-dumu da sakewa da Zayyan Bello. Wadanda sun riga sun nada mata rawanin mai girman kai. Har wasu ‘yammatan masu kishin irin kyawun surar da Allah yayi matam, da yadda take jan attention din maza akanta cikin Hijabi, su kan yi gulmarta da cewa, ita ba ‘yar kowan kowa, ba sai kafirin girman kai. Rashin yawan far’arsa ko kadan baya damunta, don ta gane nature na halittarshi ne haka, ba kuma miskilanci bane, amma akwai shi da dadin mu’amala ga wanda zuciyarsa ta amincemawa yayi alaqa dashi kamar yadda ta amince da ita Safiyyah. Tarin nutsuwarsa da yawan kokarinsa a karatu, sun taimaka gaya wajen sakewar Safiyyah dashi, don ta tsani alaqa da miskilin mutum ko dakikin dalibi. Wani abu a halayyar Safiyyah shine; in dai kana da kokarin da zata amfana dashi a karatu, to kowanne irin hali gareka zata iya tafiya tareda kai salin-alin. To hakan ce ta faru tsakaninta da Zayyan Bello, Zayyan bashi da far’a, baida walwalar fuska ko kankani, babu kuma fuskar wasa a tare dashi, amma akwai tsantsar kokari da fasaha a ilminsu na Architecture, da ba duk dalibai keda su ba, ga yawan kamewarsa daga kule-kulen ‘yammata da abokai barkatai shima, wadannan sune manyan dabi’unsa da ke burgeta dashi, suka kuma bashi (100% acceptance) a wurinta. Dama an ce sai hali yazo daya ake abota. Ya zamana Zayyan na taimaka mata sosai a harkar karatunta, a matsayinsa na gaba da ita a shekaru da matakin karatu a lokacin. To shi dai Zayyan daga karshe bai tsaya batawa kansa lokaci ba, ko yaudarar kansa na tsayin lokaci, kamar yadda Safiyyah ke yaudarar kanta da cewa abokantaka ce ta karatu a tsakaninsu, ya tara hankalinsa waje daya ya gayawa kansa gaskiyar cewa ainahin son Safiyyah Dandume zuciyarsa ke yi, so tsantsa kuma na zallar soyayyar Da namiji ga ‘ya macen data dace da duka burikansa, babu wani friendship ko makamancinsa a zuciyarsa gameda Safiyyah, bayan So na sahihiyar soyayya a ransa. Da yaga zai Takura, da tunanin ta yadda zai bullowa Safiyyah, saboda ba fuskar hakan a wurinta, tunda har ta kai shi ga kasa karatu yanzu da raba dare cikin tunanin Safiyyah Dandume, haka zai kwana yana juyi a kan gadonsa cikin shakkar yadda zai tunkareta da zancen SO. Kwarjinin da Safiyyah ke masa ba kadan bane, ya yarda Hijabi sutturah ne kuma kamala ne da Karin mutunci ga diya mace, da ke saya mata martaba da kwarjini a idon maza, in dai don Allah take saka shi, daga lokacin ya fahimci cewa lallai son Safiyyah azimun ne a ransa, kullum kuma son nata karuwa yake yi cikin ransa. Safiyyah ce kadai burinsa a halin yanzu, kuma wani babban kuduri da yake son cimmawa a rayuwa yanzu shine aurenta. A zahiri, wani abu da bai taba planning dinsa nan kusa ba shine “aure”, tunda ko a makaranta yake har yanzu bai ko kammala rubuta final project dinsa ba, balle ayi batun neman aiki dana abun rike iyali, wanda kullum Mama Fatu ke kwakwazon sai ya samesu wato sai ya tsaya da kafafunsa kafin ta samo masa matar aure daidai da ra’ayinta. Amma duk Safiyyah ta canza komai yanzu, ta birkita lissafinsa ta yi katsalandan cikin kowanne irin tunanin hankali daya mallaka, da kutsowar cikin zuciyarsa da rayuwarsa. Don haka bai wani tsaya jinkirin da zai zama batawa kansa lokaci ba, ya yanke mai fishsheshi ba tareda ya nemi shawarar kowa ba. Yaga gara ya badawa idonsa toka kawai ya cire shayin Safiyyah da kwarjininta ke saka masa daga idanunsa, ya furta mata zahirin abinda ke zuciyarsa in yaso duk yadda Safiyyah ta karbi al’amarin zai jure ya iya karba. A washegarin ranar da ya yanke wannan shawarar da zuciyarsa suna tafe shi da Safiyyah a hanyar zuwa tsangayarsu bayan sun fito daga library, labarin kannenta take bashi da suka zana jarrabawar (jsce) a yau wato Sabah da Rayha, Zayyan ya dubeta admiringly ko yadda take