Sashe 5
Heart 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
nutsu, sannan ya tantance, yayi kyakkyawan nazari akan rayuwarsu shi da Safiyyah. Babu wani doki ko farin ciki ko far’a a tare da Baffa, irin na kowanne sabon ango, wadanda dasu ya kamata ace ya shigo gidan. Idan ka lura sosai ma zaka gane idanun Baffa a rufe suke don tsabar damuwa, suna kara lumshe kansu da kansu wanda nature dinshi ne haka. Yazo zai shige sitting room dinsa kenan sai yaji tamkar motsin bude tagar Sophie ta falonta na sama. Saidai kuma hakan baisa ya juyo ko ya tsaya ba, saboda baya da kwarin guiwar yin ko dayansu, wato tsakanin tsayawar ko juyawar, saima cigaba yayi da tafiya harda kara sassarfa saboda ya buya daga idanun iyalin nasa. Yasa mukullin dake hannunsa ya bude kofar bangarensa ya shige, sannan ne ya samu ya saki ajiyar zuciya, tareda juyawa ya kulle kofar shigowa katafaren falonsa nasa. Baffa bai tsaya a falon ba, kai tsaye (masterbedroom) dinsa ya wuce, ya fada kan gadon dakin yayi dai-dai da kafafunsa akan makeken gadon na alfarma, bayan ya jefar da babbar rigarsa da jakar ‘laptop’ dinsa da ya riko a gefen gado. Ya juya ya sake gyara kwanciyarsa sosai, wannan karon rigingine ya koma, ko takalman kafarsa sau ciki da safar kafarsa bai iya ya ciresu daga kafafunsa ba, a haka ya kwanta. Zuciyarsa cike da taraddadin da ya ninka na baya, da ya tuna dole dai da safe zai ga Safiyyah ya fuskanceta, wai meyasa madadin ‘contentment’ irin na samun cikar buri daya kamata ya kasance a ciki sai taraddadi ya maye gurbi? Wadanda ba shi ya kamata ace ya kasance cikinsa ba yau, tunda dai gashi at long last, ya samo maslaha ga matsalarsu shida Safiyyah. A yau zai iya cewa ya ceci aurensa da “Safiyyah” daga tangal-tangal din da yakeyi, da kuma sauran matsalolinsu masu zaman kansu. At long last, ya ceci aurensu na tun tali-tali, aure mai tarin albarkar iyaye irin nashi da Safiyyah. Shi da Safiyyah are more than husband and wife, they are each others’ ALTER EGO, sun riga sun yarda sirrin juna ne sannan barin rayuwar junansu. To mai yasa zai shiga damuwa kuma akan hukuncinsa? Hukuncin da bisa yardarta ya aikata shi? Tunda kuwa ko babu komai, daga yau ya ceci wannan dadadden auren na tarihi da soyayyah daga rugujewa, da kuma duk wata barazanar dake hanasu kwanciyar hankali shi da Safiyyah? Akalla dai zai iya cewa daga yau yayi maganin duk wannnan bacin ran da tsangwamar da Safiyyah ke kwankwada dare da rana a gidansa. Kuma insha Allah zai tsaya yaga cewa ya cikama Safiyyah dukkan alkawuran da ya daukar mata. A tunaninsa yanzu kam ai za’a sakar ma Sophie mara, tayi fitsarinta peacefully, kamar kowacce mace mai iko a gidan mijinta, a saka mata rigar ‘yanci, da bata taba sakawa a idon Mama ba, shima kuma zai samu kwanciyar hankalin da ya rasa shekara da shekaru, a dalilin damuwar Safiyyah data Mamansa, tunda finally yayi abinda ake son yayi, kuma Safiyyah ta amince. Amma me??? Duk da yaqinin nan da yake dashi na samun maslaha da warwarar matsalolinsu na shekara da shekaru, ya rasa meyasa hankalinsa yaki kwanciya da al’amarin kuma, watau bayan tabbatuwarsa. A lokacin da bakin alqalami ya riga ya bushe. Duk juyin da Zayyan yayi a kan gadonsa ya rasa me yasa sai yaji rashin cikar kwalitin (ingancin) maslahar nan na mintsininsa ta ko’ina…. Yana fata da addu’ar Allah yasa maslahar da ya kawo din bai rikide ya koma biggest mistake of his life ba, madadin samo warwarar matsalarsu shi da Safiyyah. Bai san meyasa yake ji a ransa kamar wani babban al'amari ne ya tunkaroshi ba kuma, wanda zai canza musu tsarin rayuwa bakidaya, wato kamar ya ballo hadarin da zai dokeshi daga sama, wanda zai sake ‘worsening’ komai ya dagula al’amuran, maimakon kawo maslahar da ake nema. Don dai shi ya san Sophie itace SOUL dinshi (ruhinshi) bakidaya. Sophie itace soyayyar dake zuciyarshi gabadaya, tabbas kwanciyar hankalinsa yana cikin nata kwanciyar hankalin. Farin cikinsa har kullum, yana danganta shi ne da farin cikin Safiyyah. Sannan a kullum yana jingina sukunin ransa da nata sukunin ran. To amma anya Sophie na cikin sukunin rai yau? A wane hali take? A rayuwarsu ta aure kakaf! Basu taba raba shimfida ba in dai yana gidan. Anya maslahar nan da ya samo mai bullewa ce dasu duka? Kuma shin maslahar nan zata baima Safiyyah hakikanin farin ciki da ‘yancin da yake hango mata sanadinta? Sannan shin maslahar zata haifar da Da mai ido a garesu bakidaya??? A wannan gabar Zayyan ji yayi kansa ya kara yi masa nauyi, kamar yadda zuciyarsa ma tayi duhu, tayi nauyi cikin rashin sanin abinda ya dace yayi kuma. Domin tunanin halin da Safiyyah zata kasance a daren yau kadai ya jefa shi a rudani, wanda hakan ya jefashi a dogon tunani da dogon nazari irin mai nisan zango, irin wanda ya jima bai yi irinsa ba.. Daga wannan lokacin, a kwancen da yake bisa makeken gadonsa, cikin wani hali na kaka ni kayin zuciya da kwakwalwa, Arch. Zayyan Bello Rafindadi, ya rintse idanunsa ya shiga tunanin baya, komai ya soma tariyowa cikin idanunsa daga kwakwalwarsa, tamkar a majigin sinasinan cinema rayuwarsu ta baya ke wulgawa a idanunsa yanzu, tamkar wulgawar hotuna cikin faifan bidiyo, komai ya shiga dawo masa daki-daki tamkar a yanzu komai yake faruwa….. Zayyan ya tafi ‘down memory lane’ wato ya tafi ga tunani da tariyo dukkan rayuwarsu ta baya shi da Safiyyah, tun daga samartaka, dating dinsu, har zuwa maganar aurensu da iyaye maza sukayi uwa sukayi makarbiya, da abinda ya wakana cikin rayuwar auren. Watakila ta hakanne kadai zai samo hakikanin maslahar da yake laluben nemo musu, ta hanyar baiwa kansa assignment a tsayin daren yau bakidaya, mai karatu kuma yayi musu alkalanci na adalci shi da Safiyyah, ta hanyar tarawa da debewa tsakanin matsalarsu da maslahar da ya samo. Wadda har zuwa yanzu yake tantamar cikar ingancinta koko yace still, maslaha bata kai ga samuwa ba, in kuma aka ture komai aka ce maslaha ta samu gareshi, to ga ita Safiyyah din fa??? **** **** ****