← Book details Heart 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 31

Sashe 7

Heart 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

kamar yadda Ubangiji ya jarrabci AnnabinSa Musa (A.S). Sautin nata mai tashi ne da rangwamen amo, kuma cike da zakin murya irinna ganiyar ‘yammatanci, irin dai na budurwar dake ji da kuruciyar ‘yammatancinta, (in her teens), hakika Safiyyah ta yi nasarar shiga jami’a da wuri, su ake kira JJC (Johnny just come). Don a lokacin Safiyyah bata fice shekaru goma sha takwas a duniya ba, inma ta kai din. Ranar da ya fara ganinta, tun kafin ya ga fuskarta shi in’inar ya fara ji, shine abu na farko da ya ja hankalinsa tamkar maganadisun mayen karfe zuwa gareta a ranar, saboda (peculiarity) din dake cikinsa, ‘yar gargadar maganarta ta masa dadin ji. Inda yaji tana maimaitawa Librarian din dake kula da (reserve section) cikin tukewa da kokarin shanye fushinta, saboda cewa da yayi wai shi baya gane me take cewa. Kamar zata yi kuka ta sake cewa taqarqarewa tana fizgo maganar da kyar, ta ce cikin in’inarta…. “Malam…, nace-nace maka…. “Architecture, Form, Space, and Order (Frank Ching, 1979)” zaka dauko min. “Me kike cewa ne?” “Kayi hak-kuri….ni…ni… stammerer ce, I don’t feel repeating it again”. Zayyan sai ya samu kansa da yin murmushi daga kwancen da yake a rigingine, yana iya hango fuskarta cikin damuwa a lokacin cikin wani sako na kwakwalwarsa, kamar a lokacin Sophie take furtawa librarian din bazata maimaita ba. Exactly over a decade now da faruwar hakan amma komai dawo masa yake tamkar a yanzu yake faruwa. Ya juya ya sake gyara kwanciyarsa, wannan karon akan ruwan cikinsa yayi folding hannayensa a saman kansa ta baya, ya kara nausawa cikin dogon tunanin nasa. In’inar kawai yake tunawa da bege da kewa mai yawa, kamar Safiyyah bata cikin gidan nasa a halin yanzu, bayan shine da kansa ya buyar mata cikin wani hali na rashin yarda da hukuncinsa. “She looks so naïve and innocent budurwa tun a lokacin, amma kuma tawayar tangardar harshen ya zame mata cikas ga cika “Classy Babe (hadaddiyar budurwa”. In ta fadi abu kuma aka ce ta maimaita ba’a gane ba, bayan hararar da zata zabga maka kamar idanunta zasu fado kasa, har kwallahr bakin ciki take yi mai zafi. Don me zaka ce baka gane ba? Ya fara son Safiyyah daga rana ta farko da ya fara haduwa da ita. Wani abu kaman dai “Love at First Sight” ko me? Wanda yayi ta ‘nurturing’ dinsa yana nunar dashi a kasan ransa shikadai, kuma har gobe bai gama rainon nasa ba, don kullum kara tsiro yake da fidda sabuwar yabanya, yana bude sabbin rassa da sababbin ganyaryaki sabbi gadagal! Na son Safiyyah a zuciyarsa. Musamman a halin yanzu da yake tantama kan ingancin abinda ya aikata mata, da sunan nema mata maslaha a zaman aurensu. Shi da kansa ya san bai san da kalmar da ya kamata ya suffanta ko ya kamanta ko ya kintatawa mai karatu girman matsayin soyayyar Safiyyah a zuciyarsa da cikin rayuwarsa gabadaya ba, koda harshen da zai iya bayyana girman son da yake yi mata ba yadda mai karatu zai gane, da girman matsayinta cikin rayuwarshi da duniyarshi tun daga ranar ba. Kawai ya san cewa duk wani so na gaskiya da duk wata kauna ta hakika da Da namiji na kwarai irinsa zai iya yiwa diya mace, to shi Zayyan Bello, nashi son ya kare ne akan Safiyyah Usman Dandume. Saboda ya so ta ne a lokacin da zuciyarsa babu nauyin komai a cikinta sai zallar kuruciya, soyayyah ce ta samartaka zallah irinta isowar shekarun hankali wato cikakkun shekaru na cikar balaga, wadanda a su ne namiji ke fara gina matakan rayuwarsa, babu nauyin iyaye da ‘yan uwa da yazo ya hau kansa daga baya. Babu komai a ransa a lokacin sai katon fili fetal! Wanda zuciyarsa ta shimfida ma Safiyyah koriyar darduma akai, ta feshe dardumar da turaren nan na kauna da soyayya na “Sandalia” tayi mata maraba da sauka, gurbi ne dama wanda ya tanada ya ajiye musamman domin soyayyar iyalinsa kadai, amma bayan wannan babu nauyin kowa da komai a cikin zuciyarsa a daidai lokacin. ‘Yar mutanen Dandume, ta shigo rayuwar samartakarsa tun yana rubuta ‘final project’ dinsa a jami’a. Hakan ne yasa lokacin da Safiyyah ta iso rayuwarsa daga haduwarsu ranar nan a (University Library), nan da nan tayi maza ta shige sukuf! Cikin ransa, ta baje kolinta ta hanyar mamaye ko’ina ita kadai, bata bar masa kowanne kankanin sako da zai sanya tunanin komai bayan nata ba. Har wani lokacin ya kan kirata da suna (Cinye Du) a cikin ransa, don hakika duka zuciyarsa Safiyyah ta cinye, ta mamaye ko’ina ita kadai. Ba wadda zai iya kara so kuma, bayan so na farillah, wato na Mahaifiyarsa Mama Fatu, da kannensa uku da Yayyensa biyu duk mata. Uwa-Uba ka cire son da yake yiwa mahaifinsa (his beloved Baba Bello), wanda bazai shiga cikin kwatancen bama to duk sauran girbin dake zuciyarsa ‘yar mutanen Dandume ta cinye. Ya fara son Safiyyah ne tun mahaifinsa Arch. Bello yana raye, lokacin da shi kansa daukar nauyinsa akeyi da komai na karatunsa, wato Baba ke daukar takalihun komai nasa, tunda dan lelen cikin mata ne shi, abin nufi shikadai Mama Fatu ke da, a matsayin Da namiji, Yayyensa biyu mata ne haka kannensa uku duk mata ne, gashi da tarin da basira a karatu, Zayyan nada rawar kan kuruciyar samartaka ta samari ‘yan bana bakwai tsararrakinsa a wancan lokacin, zaka ganshi kullum cikin nutsuwarsa da tsafta da gayu, very reserved and smart dashi, dalibin shekarar karshe a karatun digiri na biyu a lokacin yana rubuta thesis dinsa. Dan kimanin shekaru ashirin da bakwai da haihuwa. Saboda irin gatan da Baba Bello ke gwada masa, tunda ya gama digirin farko ya saya masa wani lafiyayyen (Bike) na yayin samari, mostly 'yan gata na lokacin kadai ke iya hawa ‘Bike’ dinnan da ake kira (LIFAN), wanda dashi yake shanawarsa yana fantamawa da abokansa a tsakiyar ABU. Daga nesa in ka hango shi akan ‘bike’ dinnan yana zuga gudu a cikin harabar makarantar, iska na cika rigarsa, ko idan ya shigo farfajiyar tsangayarsu a kan babur din, sai ka so kara yi masa kallo na biyu, domin zaiyi maka matukar kama ne da jarumin wasan kwaikwayon nan na kasar Hindi; Bollywood actor, Abhishek Bachchan. Saidai ace Abishekh ya fishi zama jajawur ya fishi nannadadden gashin kai. Shi Zayyan Ba-katsine ne kuma Ba-rume, wanda ya tsotso nasa ussin kyawun da hasken fatar daga Rumawan jihar Katsina.
Chapter 7 · 0% Book details