Sashe 15
Heart 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
bayan istikharar da zan bata, sannan za’ayi daurin auren”. Malam yasa murya ya kira Safiyyah, ta zo ta tsugunna gwiwa bibbiyu a gabansa tace “gani Allah gafarta Mallam!”. Yace “zo nan mu raba dare nida ke akan sha’anin aurenki”. Nan ya bata istikhara yace tayi a daren yau, tayi addu’a sosai, shima zai yi duk su nemi zabin Allah akan aurenta. Washegari Lahadi Zayyan yazo Dandume zance wajen Safiyyah, a yau ne suka taba tattaunawa extensively akan rayuwar kowannensu, Zayyan ya baima Safiyyah tarihinshi dana iyayenshi kaf, itama ta bashi nasu in detail, basu taba yin hira mai zurfi da tsayi akan junansu irin yau ba, yanayin neman auren Zayyan da Safiyyah cikin dattaku kamar na mutanen da, sabida koyarwar gidansu Safiyyah da suka dora soyayyar tasu akai, har sunan su Hatoon yau ya gaya mata, da su Yaya Zubaida, sai yau Safiyyah ta san adadin ‘yan gidansu, da hotunansu cikin wayarsa, ita kuma ta kira kyawawan kannenta uku mata duk yau tayi introducing dinsu ga Zayyan wato Sabah, Rayha da Rayyah suka zo suka gaida Zayyan daya bayan daya. Daga shi har Safiyyah farin shiga ne a sha’anin soyayya, they are all novice. Don haka soyayyarsu a lokacin mai sanyi ce kuma mai tsabta, ba irin ta zamanin nan ba dake cike da sabon Allah, Zayyan bai taba son wata yarinya ba, bai kuma taba sha’awar yin aure nan kusa ba, kai shi bai san ma shi namiji bane mai bukatar mace sai bayan haduwarsa da Safiyyah Usman Dandume. **** **** **** A DISTANT BROTHER Safiyyah ta wayi gari yau da farin ciki, da tsayuwar zuciyarta wuri guda akan aurenta da Zayyan Bello, bayan kammala istikharar da Malam ya bata, ta jinan duniya ba wanda take so sai Zayyan. Da hantsi ya dubi ludayi, Yaya Sheikh ya fado mata a rai, kawai sai ta kira wayarsa. A kokarinta na son shaqa masa takaici irin wandayake shaqa mata duk sanda yace bata iya gayu ba babu saurayin da zai kwasheta. Kwana biyu tayi kewar Yaya Sheikh don ya dade bai kirata a waya ba, ana I gobe daurin aurenta da Zayyan tana ciki wani irin madaukakin farin ciki, tayi mamaki da ko Allah ya sanya alkhairi Yaya Sheikh bai bugo ya ce mata ba, sai ta yi kundumbala ita ta kira shi. Ridhwan Abubakar Dandume (Sheikh) yad aga wayara Safiyyah, ko gaisawa bata bari sun yi ba cikin tsokana take gaya masa; “Yaya Sheikh ko kasan? I have finally found my Soulmate, a cikin HIJABI! (A karshe dai gashi ta samu abokin rayuwa cikin sutturarta ta hijabi), da yake Yaya Sheikh kullum baya rabo da yi mata gorin bata da mashinshini ne saboda bata gayu irin na ‘yammatan yanzu, sai fama da Hijabi, shi ko a kafa aka daura masa ita zai kwance ya yar, ya zura da gudu saboda rashin iya gayunta. Ya kan yawan ce mata, shi in ya tashi aures ai mace sai mai kyalli da daukar ido da iya daukar jambaki, gazal da jagira da iya saka suttura kadai zai aura. Wadda I ta shigo wuri sai an san ta bayyana. Wadda in ya ganta zai ji sanyi daga duk wani bacin rai saboda haduwarta da iya gayunta. Kullum abinda yake fada mata kenan in yaso tsokana da son kular da ita. Kai kace ‘yar mace da dan namiji suke ba ‘yan maza zar ba. Don haka da dariya sosai yau itama take ramawa inda, take gaya masa Zayyan dinta ya fishi komai, ya fishi kyau Ba-Rumeh ne, kuma Uwa Uba yana matukar sonta a hakan da take cikin Hijabin, gashi ya fishi iya gayu da iya daukar wankan da yake mata gori…..ya-yan-yan”. Safiyyah sai ji tayi shuuuu! Kamar an katse wayar, kuma daga ranar bata kara samun Yayan nata Ridhwan a waya ba, sannan bai kara kiranta ba ko da wasa. Wannan abu ya bata mamaki, don ita wasa take masa, at least yaji inda dadi irin gori da cin fuskar da yake mata kullum. Koyaushe ta kira wayarshi bata shiga, but to her utmost surprise (ga babban mamakinta) sai taji yana hira dasu Ammi lokaci-lokaci akan shirin auren nata. Har Ammi ta gaya mata cewa ya aiko da gudunmuwar kudi mau kauri yace a hada ayi mata kayan daki. Abin ya sosa mata rai, me Yaya Shaikh ke nufi da yanke alaqarsu kuma bazai mata ko fatan alkhairi tsakaninta da shi ba? Kenan ita blocking dinta yayi daga wasa ko me? Itama daga ranar sai kawai tayi zuciya ta rabu dashi, bata kara gwada kiran Yaya Sheikh a waya ba. **** **** ****