← Book details Heart 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 31

Sashe 19

Heart 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

saranda Sophie! Na yarda ni Zayyan mijin Ustaziyyah ne, to yaya zanyi da ustaziyya ta? Daina borin haka kinji! Na hakura na bar miki abinki, ince ko shikenan zance ya kare?". Ita kanta Safiyyah sai da ya bata dariya, yadda ya biye mata hadda saranda. Ta lura da yadda jikin sa ke dan rawa a lokacin, amma bata fassara hakan da komai ba, amma fa Zayyan yau an shiga yanayi, gabadaya ta lura yau Zayyan wani kallonta yake so inviting with great admiration. Yayi kuta yace, “Amma ba komai kiyi lokacinki ne, nima nawa lokacin na zuwa, kowa da ranarsa, tawa ranar na nan tafe. Ranar da bazan saurari wannan shagwabar ba nima, balle in yi la’akari da ustazancinki, kaina kawai zan taimaka. Kaina zan so nima a ranar, zaki ce na gaya miki. Kiyi shagwabarki da ustazancinki ki gama su a Dandume, tunda gidan Malam ne ba nawa ba, don haka banida ‘say’ sai abinda kikace kika kuma zaba mana, tunda ni na biyo ki gidanku yanzu dole ne in bi duk abinda kika gindaya min". Ya karasa da muryar da dole Safiyyah taji tausayinsa. Safiyyah ta hau dariya tana cewa "au abin haka ne? In da kara ga Malam ai kaima nan gidanku ne “Habiby!". Ya ji wani irin tashin tsigar jiki, ya dai daure yace "ba wani Habiby, tunda guduna kike a gidanku Safiyyah, da gidana ne kin isa ince ki cire min hijabi kice a’ah ba’ayi yakin duniya na uku ba???” Safiyyah sai dariya take har hakan yasa Zayyan ya shagala cikin kallonta, ‘she looks so cute’ in tana dariyar in’inarta. “Mu bar zancen wasa Sophie, yau zuwa nayi inji gaskiyar yaushe zaki tare a gidanki? Hatta Mama ta magantu, tunda har tayimin magana cikin kosawa akan batun tarewarki. For God’s sake kince “exams” kuma na tabbata an gama. Safiyyah kince rashin lafiya, kuma gashi kin murmure, for God’s sake yaya kikeso inyi da raina da tunanin Safiyyah tana Dandume, ni ina Zaria nikadai, sai faman rungumar pillow da tumurmusar katifa nake, alhalin na san inada Safiyyah ta kuma zama mallakina?” A yadda yayi maganar idanunsa kai tsaye suna kallon nata saida ya bata kunya sosai, da tausayi kuma duka a lokaci guda, domin damuwarsa ta fito karara a sautin nasa, sannan cikin lallashi da ban baki yake maganar. Abinki da So, koko ince soyayyah ta hakika mai saurin karya zuciyar mace, Zayyan ne fa! Wani mutum guda daya da ta fara sanin so a kansa, batare da ta san ma menene son ba, kawai ta samu kanta da sabo dashi farat daya, ya shige ranta sukuf! Duk a lokacin da bata yi tsammani ko taba hakaitowa ba. Itama tasan ba wai bata son Zayyan bane, ba kuma ta daina son sa bane bayan an daura musu aure, kawai Anti Dije ta tsoratata da aure ne gabadaya. Safiyyah sai ta samu kanta da yin saranda, ta hanyar cewa “Shikenan na daina, duk lokacin da iyaye suka sake sakawa bazan kara musawa ba, kayi hakuri, ka ji Habiby?”. Zayyan ya ji wani irin dadi ya ratsa har ransa, sai kawai ya taso daga kishingidar da yayi cikin kujera ya dawo yayi zaman Rakuma dirshan a gabanta. Ya daga tafukan hannunta ya saka fuskarsa a tsakaninsu, santsin sajensa dake kwance gefe da gefe na kyakkyawar Barumiyar fuskarsa yasa saida tsigar jikinta ya tashi yarrr! Shikuma duk sai ya susuce, ya rikice irin na rashin sabo da kusantar jikin mace, tasowar wani sabon al’amari a tare dashi yasa ya kai tafin hannunta saman lips dinsa ya sumbata for the first time, idanunshi a lumshe yace. “baki bukatar bani hakuri, amarya ai bata laifi ko ta kashe dan masu gida, that’s my beloved Sophie, ni kadai na san irin tanadin soyayyar da nake mana, nagode Safiyyah kinji, once again nagode kuma in sha Allah bazaki taba nadamar hada rayuwa dani ba, nayi miki wannan alkawarin, in sha Allah Safiyyah". Tunda Zayyan ya samu wannan damar, yau sai ya dukufa lallashin 'yan kayansa da alkawura da kalamai masu dadi har Safiyyah ta fara kwantar da hankalinta a kan tarewarta, ta dan saki jikinta dashi kadan, hannunsa sarke cikin tausasan yatsunta suka shiga hira a hakan. Kai a karshe ma basu rabu ba a ranar, saida Zayyan ya san yadda yayi da dabara da hikima ya raba jikinsu wuri guda karo na farko a tarihin soyayyarsuda jikisa ya shiga cikin nata, ya rungume Safiyyah tsam-tsam a jikinsa lokacin da zai tafi, Safiyyah na iya jin yadda kirjin Zayyan ke bugawa ba sassauci yana gaya mata cikin kunnenta. “Saurara Sophie kiji irin bugun da kirjina ke yi, ba komai bane sonki da tsananin sha’awarki ne”. Ko daga yadda jikinsa ke bari cikin mararin samunta da yayi cikin jikinsa yau, ta yarda da abinda yake fadin. Zayyan ya samu gangara domin gabadaya Sophie ta saki jikita dashi yau, yayi kissing dinta sosai a kasan wuyanta, kafin ya gangara zuwa saman lips dinta, ya sumbaceta son ransa har cikin tsakiyar bakinta da wani launin (French kiss) da shi kansa bai san yadda ya aiwatar dashi ba, karo na farko a soyayyarsu. A ranar ya gaya mata ya san 'fear' dinta, “I obviously know your fear” don na karanceshi tsaf a tsakiyar idanunki, ko baki fada ba na gane tsoron daren farko kike ji, amma kullum Safiyyah kisa a ranki ni ba abinda yasa na aureki kenan ba, kuma soyayya ba cutarwa bace. Na aureki ne don ina sonki Sophie, ba don sha’awar wani abu a jikinki ba, ina so in rayu dake ne, daga nan har karshen rayuwata. Ina fatan ki zama uwar ‘ya’yana a duniya da lahira kuma matar dana ke so in rayu da ita har a aljannah. Da wannan nake so ki kwantar da hankalinki ki tare a gidanki kinji Safiyyah, nayi miki alkawarin bazanyi komai ba sai ranar da kika shirya karbata a matsayin mijinki, barin rayuwarki, kuma bisa amincewarki da yardarki da goyon bayanki kadai zan kusanceki”. Bayan kunya da taji yau kamar tace kasar ta tsage ta shige har da tausayinsa da karin soyayyarsa. Sukayi wata irin rabuwa mai sanyi a zuciyoyinsu, Zayyan yana kara kashe mata zuciya da kalamai masu sanyaya ruhi da Batasan ya iya bama. Ganin kwana biyu Safiyyah ta fara samuwa ta amince ta kwantar da hankalinta, sai iyayenta suka durfafi shirin kaita gidan mijinta a Zaria. Malam yace baya son bidi’a mara tushe. Don haka baya son taron biki. Zayyan zuwa lokacin ya maida hankalinsa ya kammala project dinsa yayi (defense, both internal and viva). Ya fito a sahu na farko cikin zakakuran dalibai da suka fita da (first class) su uku kacal a tsangayar Architecture, daga jami'ar Ahmadu Bello, don haka yana gamawa ABU suka daukeshi aiki sharp-sharp a matsayin Assistant Lecturer. Lecturing has been his dream career…. saboda a komai so yake ya gaji Babansa. Don haka ba bata lokaci ya karbi offer din da godiya. Dan madaidaicin gidan da Baba ya kama musu flat ne a Samaru daidai su. Two bedroom flat da parlour daya, sai kitchen da balcony da harabar adana mota guda daya. Akayi sa’a daga Zayyan har Safiyyah masu saukin tunani na rayuwa ne. Iya abinda mahaifinta yayi mata dashi taje gidan mijinta. Ba abinda Zayyan ya saka a gidan har ledar tsakar daki su suka saka abinsu. Safiyyah ta shigo gidan Zayyan da tsaftatacciyar zuciya, soyayyar su gwanin sha’awa, takamaimai in za’a dora mata wuka a makoshi, bazata ce ga abinda ya sata son Zayyan ba da bashi matsayin barin rayuwarta (miji) da gaggawa haka ba, cikin abinda bai gaza shekara ba, kawai tana son duka halayensa. A wannan lokacin kam shima da kansa ya san Sophie babu soyayyarsa irinta aure mai girma a ranta, sai ko halayensa da kamalarsa data ke so fiyeda komai nasa. Sai ya fara da koyawa Safiyyah yadda zata yi masa so na soyayyar aure gradually. Saboda aurensu yazo ne unexpectedly daga Allah, wato daga zuwa gabatarwa tsakanin iyaye sai Ubangiji ya aiwatar da kirarinsa na “kun fa ya kun” a kansu. Don haka da Safiyyah ta tare abu na farko da Zayyan ya fara yi shine ya fara da janta a jiki, ya maida kansa dan aikinta, komai tare sukeyi na ayyukan gida, suna yi suna hira yana bata dariya kamar ba shine mara far’ar nan a filin Allah ba. A hankali ya fara koya mata yanda zata zauna dashi cikin tarairayar abinda yake so da gujema wanda baya so, Zayyan ya koya mata sakin jiki dashi cikin launin soyayyahrsa mai shiga rai. Alal misali a ranar da Safiyyah ta tare da yake Zayyan ya riga ya lura da fear dinta akan first night. Sai ya hadiye duk wata zalamarsa irin ta kowanne sabon ango a wannan ranar, ya dinga lallaba Sophie da tatsuniya da labarin Magana Jari ce, saboda shi yayi karance-karance na adabin Hausa tun yana secondary school, ya bata labarin cewa yana cikin Hausa Club and Society har Debate na harshen Hausa ya sha zuwa ya wakilci makarantarsu. A haka labari ya kaiwa Sophie karo a ranar har tayi barci a jikinsa bata san lokacin da tayi ba. Hakika ta sara ma Zayyan wajen iya sadaukarwa, ga iya kalaman soyayya da lallashin mace, irin kalaman da ya baibayeta dasu da asubahin ranar bayan sun sallaci sallar asubah a jam’I su biyu. Suka koma gado suka kwanta idonta cike da barcin gajiya amma hankalinta bai kwanta ba, ganin shi bashi da niyyar yin barcin safen, sai ma yaja duvet ya rufe ta har zuwa kirjinta, ya sukuya saman kanta yana mata kalamai masu kwantar da hankali da nuna mata cewa shi bashi da matsalar komai yau a kan hakan. Bama ya jin sha’awar komai (he’s overwhelmed with happiness and excitedness) da shigowarta rayuwarsa, yace ta saki jikinta tayi barcinta ta huta Zayyan zai mata tausar kafar da zata sat aji dadin barci. Tun tana dar-dar da shi har ta yarda da gaske yake, ya soma yi mata tausar ta hanyar jan zara-zaran yatsun kafarta a hankali, tausar namiji na ratsa Safiyyah bata san yaushe barci ya soma fizgarta ba. Daga bisani da ya tabbatar tayi nisa a barcinta sai ya jefa pillow a kan kilishi ya koma can ya kwanta, yana kallon barcin Safiyyah da yadda take sauke numfashin
Chapter 19 · 0% Book details