Sashe 2
Heart 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
KAWAR ZUCIYA ( Littafi na 1) MATASHIYA G arin Abuja, kamar yadda kowa ya sani, gari ne da ya tara kerarru da kuma shahararrun unguwanni (Estates) na gani a bada labari, a matsayinta na babban birnin tarayyar kasar Nijeriya, gari ne daya mallaki manyan uguwanni kala-kala. Saidai duk yadda kowanne Estate a garin ya kai ga tsaruwa da girma, hadi da burge idanun mai kallonsa ko maziyarcinsa, har yau ba’a samu shiryayyen Estate da ya amsa sunansa kamar “Sunset Estate” dake nan a tsakiyar unguwar Guzape ba. “Asokoro Extension” wadda aka fi sani da unguwar “Guzape”, wasu na yi mata kirari da (Beverly Hills of Nigeria) saboda tsaruwarta da kyawun fasalin unguwanni da gidajen cikinta, sannan da kawatattun dogayen gine-ginenta da suke akan tudu. Kamar yadda mazauna wurin suka sani, ita Guzape kacokam dinta a kan hayi (hills) wato (tuddai) take tsugunne. Kana dumfaro Guzape, Sunset Estate zaka fara hangowa sabida tsayin gate dinsa, ya zamanto shine ‘landmark’ din da ya fito da unguwar Guzape, dogon kyakkyawan gini ne wanda aka yi shi a tsakiyar (Guzape main). Zai yi wuya farat daya ka yarda cikin kasarmu ta gado ne wannan kyakkyawar unguwa ta Sunset Estate take, musamman idan a hoto ko a faifan bidiyo kaga Estate din, wato dai idan ya kasance ba gani na zahiri kayi ma Estate din ba. To balle kuma idan aka ce maka fasahar wani dan asalin kasar ce ta samar da zanen taswirar, wato in akace da kai dan asalin kabilar hausa/fulani ne ya zana, ya kuma tsara Sunset Estate. Ya kasance daya daga cikin daidaikun matasa ‘yan baiwa na kabilar hausa-fulani akan ilmin zane, sannan product din Arewa ne gabansa da bayansa; kyankyasar daya daga zaqaquran jami’o’in da kasar Najeriya ke alfahari dasu. Wanda a tarihin rayuwarsa kaf! Tun daga haihuwa har girmansa, da tarihin ilminsa, bai taba fita ko (filin jirgin sama) da sunan yin karatunsa na ilmin kimiyyar Zanen gidaje da tsara Estates din birane ba. Anyi ittifakin nagartar Ilminsa na Zane ba wai ya samo asali daga shiga aji bane; a’ah wata baiwa ce da hikima na musamman, da Allah Subhana ya huwwace masa. Hakika Allah yayi masa baiwa da fasahar iya Zanen taswirar gidaje, da kirkirar zanen kowanne irin abu ya durfafi zanawa (yayi niyyar) zanawa. Abokan karatunsa na jami’a da yawa kan masa kirari da “rainon Zaha Hadid” saboda iya zanensa. Wato (British-Iraqi Architect) dinnan da sunanta yayi ficce a duniya akan ilmin fasahar Zane, suna kwatanta shi da rainon ita “Zaha Hadid” ne saboda iya sarrafa alkalaminsa wajen Zanen taswira. Ta yadda zaiyi wuya idan ka ganshi a zahiri (a fili) ra’ayal ayni ka yarda tashin farko in aka ce da kai shine wanda ya zauna ya zana “Sunset Estate”, ya fidda ‘features’ na zubin ginin yadda ya dade yana ‘imagining’ kasantuwarsa. Akalla ya kwashe shekaru sama da uku yana zanawa tareda sabunta ideas dinsa, yadda zasu tafi da zamanin da ake ciki da imaginations dinsa na kwararren fasihin ‘Architect’ akan Estate dinnan. Duk da cewa, kowa ya san ya dade ana damawa dashi a harkar Zanen gidajen zamani da Estates na birnin tarayyah da kewayenta, abin nufi, har a sauran jihohin kasar Najeriya an san da zamansa akan harkar kwangilar Zane, a kalla a kowanne satin Allah yana samun kwangilar Zanen Estate dana tsara gidaje a ko’ina cikin kasar Nijeriya. Har a karshen shekara ta dubu biyu da da ‘yan kai, Allah ya bashi ikon kammala zanen taswirar ginin ‘Sunset Estate’, bayan kwashe tsayin lokacin yana sarrafashi yadda yake so da alkalaminsa, tsarin ginin da komai dake cikinsa ya fito sak! Yadda yayi hasashensa cikin kintace da tunaninsa. Zaka kara mamaki kwarai in kayi la’akari da karancin shekarunsa a lokacin zanen Sunset Estate da lokacin gininsa. Abun zai matukar kara burgeka ne in kaji cewa yayi zanen ne cikin shekarun kuruciyarsa in his early thirties. Shi da kansa idan ya tuna cewa fasaharsa ce ta samar ta kuma ajiye gidajen ‘Sunset Estate’ a muhallinsu, baya sanin sanda yake yiwa Ubangijinsa tasbihi kan wannan exceptional baiwa da yayi masa, yana jin tarin alfaharin hakan a kasan ransa; yana burge kansa da kansa shima, yana godewa Ubangijin fasaha mai kyauta da kari a gareshi. Har wani lokacin yaji tafin hannunsa sun tafi da kansu…, suna masu haduwa da juna…., wato yaji hannunsa na motsawa cikin tafawa kansa da kansa……. Duk da cewa sanin kowa ne shi dan na gada ne ta fannin ilmin Zane…. ba dan taka haye bane, abin nufi gadon fasahar ilmin zanen yayi, sannan ya zauna a aji ya karanta shi. Kenan “Zaha Hadid” bata haifeshi ba balle ta raineshi amma shima gado yayi, ya gada ne daga nasa mahaifin, marigayi Arch. Bello, wanda shima wani shahararren tsohon (Architect Guru) ne. **** **** **** SUNSET ESTATE Estate din zagaye yake da wasu dogayen shuke-shuke, bishiyoyi ne masu tsayi suka yi masa rumfa, irin dogayen bishiyun da aka fi sani da suna ‘palm trees’. Idan dare yayi ko’ina ka juya hasken fitilu ne na kayatattun kwayayen lantarki, masu bada launi da kaloli daban-daban, su maida Estate din kamar rana. A yawancin lokuta musamman da maghriba yanayin hasken fitilun Estate din komawa yake tamkar wani yanki ko wani bangare na ‘Sharm El-Shaikh’ din kasar Misra. Saboda babu yawan zafin rana sosai a Estate din, sakamakon dogayen shukoki dake lullube dashi. Idan kuwa a lokacin damuna ne bishiyun Estate din sun fi zama korra sharr, da tashin kamshin furanni iri-iri. Kofofin shiga ‘gate’ din wasu manyan kofofi ne na jan karfe masu budewa da rufewa da kansu (automatic gate), ko’ina na jikin katangar ginin Estate din, an katange shi da (electric fence). A daidai tsakanin kofar shiga data fita wato tsakanin kofar hagu da kofar dama, an rubuta sunan Estate din da kalar ruwan gold daga can samansa, inda aka maqala shi a jikin wani farin bangon gilas mai garai-garai da daukar ido, an rubuta shi rada-rada da manyan baki kamar haka; “Sunset Estate”. Idan aka shigo akwai ‘lanes’ biyu na shiga da na fita, an kawata ko’ina da ‘solar lights’ da ‘security lights’ da ‘street lights’. An shimfida bakar kwalta sambal a gabakidaya titin da zai shigar da kai cikin ainahin Estate din, da wanda zai fito da kai wajensa. Akwai gidaje kala-kala a ciki, kama daga (blocks of flats), da (terraces), wanda a ciki akwai (semi detached da fully detached houses). Kowane street/close na cikin Estate din an saka mishi suna da ‘sign board’ mai dauke da sunan sa, kuma wani abin burgewa shine kowanne close/street ya samo asalin sunanshi ne daga Local Governments din jihar Katsina, saboda ainihin wanda ya zana kuma mai Estate din dan asalin jihar Katsinan Dikko ne. Kishin jiha irin nasa yasa kana shigowa zaka fara cin karo da local street names da ba’a saba gani ba a wurare irin wadannan, irin su Batsari Close, Bindawa Close, Ingawa Close, Daura Close, Funtua close, Jibia Close, Dutsinma Close, Dandume Close, Bakori Close da sauransu. Mafi girman Street din cikin “Sunset Estate” shine Street na farko da zaka tadda da zarar ka shiga layin farko, wanda duk gidajen cikinsa (fully detached) ne, kuma sun fi sauran girma da kyau, yana dauke da sunan mahaifarsa ta ainahi watau “RAFINDADI Close”. A cikin Sunset Estate, har ila yau, akwai supermarket, akwai local market (kasuwar siyan kayan gwari/kayan miya dasu (veggies), akwai masallaci, akwai (pharmacy) sannan akwai saloon na maza dana mata. Daga can karshen Estate din akwai wani katon dutse da ake hangowa daga ko’ina kake cikin Estate din, irin duwatsun Guzape Hills, anyi ‘park’ na shakatawa a gurin, mazauna Estate din na zuwa da yamma don hutawa da ishadi, suna kallon faduwar rana. Gurin ba karamin kyan daukan hoto yake yi da yammaci ba, musamman idan rana ta tafi zata fadi. Kwarai zaka so daukar hoto a Sunset Estate, a irin wannan lokacin da rana ta tafi zata fadi. Yanayi ne mai ban sha’awa dake afkuwa kusan kullum a cikin Estate din, kamar yanayin kasashen ketare (daya daga cikin manyan dalilan da yasa ya zabi sakawa ‘Estate’ din suna Sunset Estate kenan). A can wani gefe na park din, akwai gurin wasan yara da aka kawata da kayan wasa da liluna iri-iri na jin dadin kananan yara. Kai daga ganin tsari da zubin ‘Sunset Estate’ kasan mamallakinsa kuma wanda ya kirkireshi ya kashe dukiya da kwarewarsa ta fitaccen mai ilmin zane (Architect) wajen zana shi da tsara shi da gina shi, da gani kuma zaka tabbatar da cewa Estate ne da masu kambun susa kadai, ko masu babban mukami a gwamnati zasu iya mallakar muhallin zama ko na shiga haya a cikinsa. **** **** **** SHIMFIDAR LABARIN “My Co-Architect!”. Sunan da yake kiranta dashi kenan, a duk lokacin da yake cikin shaukin begenta, da lokutan da kewarta da tunaninta suka addabeshi, ko in yana magana da wani a kanta ko ‘yan jarida in dai zai ambaceta to in sha Allahu zaka ji yace “My co-architect”. Wannan ya faru ne (bayan barinta rayuwarsa) sai wannan inkiyar daya bata ta zame masa abin ambatonta dashi, abin tunawa da ita, idan yana zancenta, baya ambatar sunanta na hakika saidai “My co-architect”. Sau tari kuma ya kan ambaceta da wannan sunan ne a duk lokacin da tunanin gwagwarmayarsu tare a rayuwa yazo masa, cikin fadi tashin neman ilmi, soyayyar kuruciya (wadda ta kaisu ga aure), neman na kai cikin aikin koyarwa da yayi a jami’a, ko idan ya tuno ranar aurensu mai kyakkyawan tarihi, aurensu mai asali da tushe mai kyau, wanda aka yi tun cikin shekarunsu na kuruciya, tun mahaifinsa na raye a can baya. A rayuwarsa bai iya manta alherin mutum ba, to balle alherin mutum mafi kusanci dashi wato ita matarsa. Shiyasa ko sau daya bai taba manta gudunmuwarta ga nasarar samuwar gina “Sunset Estate” ba, dama sauran nasarori masu girma data taimaka masa (koda da shawara ne) ya cimma a rayuwarsa. Duk wata daukaka da tazo masa ya kn ce ya sameta ne tare da ita, har bayan tafiyarta daga rayuwarsa yana tuna ta da wannan kimar, ya kara jin ninkin so da kaunarta. Hakika ita wani ginshiki ce na dukkan cigabansa, da kafuwarsa, da tsayuwarsa kan tsinin kafafuwansa. Bayan canzawar dukkan kaddarorinsu, bai daina kallon komai na nasarar Estate din a matsayin nasu