Sashe 20
Heart 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
barcinta cikin nutsuwa. Da gaske da akace wai wasu matan, sun fi kyau idan suna barci, ya yarda da hakan yau akan ‘Sophie’, wato Safiyyah is a sleeping beauty”. Yayi ta jinjinawa kansa yana sarawa kansa da kansa tareda kissimawa a ransa, ko yaya akayi ya iya yima Sophie wannan bajintar? A dai wannan daren mai dumbin tarihi da ya dade yana jiran isowarsa, wato a darensu na farko? Ya jure bai kusanceta ba duk karfin sonsa gareta, da dokinsa na zuwan wannan ranar?! Shi da kansa sai ya baiwa kansa amsa da cewa saboda sonta da kaunarta da yakeyi sun rinjayi sha’awar. Kasancewarta cikin kwanciyar hankali rana ta farko a gidansa zai fiye masa duk wani pleasure da zai samu a cikin daren. Bai auri Safiyyah don biyan bukatar gangar jikinsa ba, kaunarta yake yi har cikin bargonsa, wata irin kauna mai yawa, don haka son farin cikinta tareda shi a zaman aurensu ya rinjayi komai. Kuma yana so ya zama mai fada da cikawa a gareta. Wato in yace zaiyi abu, ya tsaya ya tabbatar yayi, in yace bazai yi ba, kada ya canza. Kwanciyar hankalinta dashi yana gaba da komai. Washegari daga shi har ita, a ranar sai suka zamewa juna kamar wasu bakin juna, ta kasa hada ido dashi tana ji a jikinta kamar tayi masa laifi data ganshi kwance akan carpet, wato ya bar mata gadon ta kwana ita kadai cikin sakewa. Tare sukayi girkin breakfast, Zayyan na firar dankali Safiya na juye Ruwan zafi a tea flask, tana masa dariyar wai ya iya firar dankali, yace “meye abin mamaki? Wai baki san ni kanin mata bane, kuma Yayan mata ba? In kawayen Mama suka zo gidanmu ce min suke na mata-na matan Mama. Don haka ki daina mamaki don kin samu kwararren mai firar Dankali a gidanki, ba abinda ban iya ba na kitchen, in gaya miki. Kafin a yiwa su Yaya Zubaida aure duk makyuyata ne. Mama tafi sakani tayata aikin kitchen fiye dasu”. Nan ya shiga bata labarin halayen ‘yanmatan gidansu daya bayan daya, cewa Zaitoon da Zahra sun fi baiwa gayu da kwalliya muhimmanci fiyeda aikin gida, Hatoon kuwa auta ce sangartacciyar Mama, da irin kyuyar Yaya Zubaida akan aikin gida, yanzu zata kirkiro ciwon ciki na karya don Mama tace ya karba ya mata aikin, don haka duk wani aikin kitchen na Yaya Zubaida kusan shi yake yiwa Mama Fatu. Yace Yaya Zubaina ce kadai ke dan tabukawa, kafin a aurar dasu, itama sai in baya nan”. A haka suka soya dankalin turawa (irish) da kwai, suka dafa shayinsu yaji kayan kamshin gargajiya kanumfari da citta, suka juye komai a plate guda, suka dauka zuwa falo, yana sakale da ita a kugunsa tanata jin kunya. A plate daya suke ci, Zayyan ya cako irish da fork ya kai bakin Safiyyah “ha’an, bude nan in baki a baki!” Kunya sosai ta kamata, ta rufe ido tana ‘yar dariya ta rashin sabo, wani abu da wani namiji bai taba yi mata ba, bayan Yayanta Yaya Sheikh, wato bata abinci a baki. Shima Yaya Sheikh din tun tana ‘yar kankanuwa ne, sanda tana junior secondary, Yaya Sheikh na yawan bata abinci a baki, kuma a gaban Ammi, musamman in tana fushi, ko Ammi ta bata mata rai. Zayyan ya lura ta tafi tunani, yace. "Sophie tunanin me kike haka? Bude idonki ki dubeni, wannan kunyar fa dole ki ajiyemin ita a gefe zuwa sanda zan bukaceta, amma ba na bukatarta yanzu sam. Ta yi min yawa. Yanzu so nake in zama ke ki zama ni, mu gina trust a tsakaninmu, mu zama confident din junanmu, muyi rayuwa ta shakuwa, fahimtar juna, amana da soyayya. Sophie kin san daga jiya na zama naki kin zama tawa? To kiyi wa Allah ki daina yimin rowar kyawawan idanunki in muna tare, kina wannan boye sun, domin su nafi son gani koyaushe, inta tozali da (silverish eye ball) dinki. Daga su sai in’inar (stammering), su nafi so fiyeda komai naki. So open your eyes and look straight into my eyes ko naji dadi, ki kuma bude min dan bakin nan ina so in ciyar dake yau da hannuna, ki kuma yimin ‘yar in’inar ko kadan ce inji mana?". Ai bata san sanda tasa dariya ba. Shi kuma daman hakan yake so, ya dawo da attention dinta gareshi, don ta tafi tunani, sam ta manta yana wurin, sai ya cigaba da kambama dadin in’inar tata, wadda yace tafi masa duk wata muryar zabiyoyin larabawan da ya sani dadi (Arab musicians) su Nancy Agram. Dariya take yi sosai, ta shagaltu da dariyar shima ta shagaltar dashi cikin kallonta da shaukinta, tace “wannan kuma “C” ce Malam, don ka san bazan iya waka bane kake mun ba’a”. Da rana ma tare suka yi girkinsu inda sukayi lunch mai saukin girkawa, jollof din shinkafa tayi musu da taji daddawa da naman saniya. Tun anan Zayyan ya fara gane kwarewar Safiyyah a girkin hausawa ne, ba girkin turawa ba, tunda har tasa daudawa a jollof. Sai ya bashi wani irin aroma da dandano, da bai saba ji ba, kuma ya masa dadi, Ammi ta musu wannan horon bakidayansu ita da kannenta su Rayyah, sau da dama Ammi in suna gida basa makaranta sam bata shiga kitchen. Su take barwa komai na girkin gidansu da hidimar tsaftar gidansu. Tun Safiyyah na dar-dar da angon nata Zayyan Bello Rafindadi, har ta gama sakankancewa Zayyan dai baya neman komai daga gareta sai sabo, shakuwa da soyayyah, wato so yake su saba a wannan lokacin, kwanciyar hankalinta da sakin jikinta dashi yafi bukata fiyeda gangar jikinta. Soyayyar da bai nuna mata kafin aurensu ba, ita yake nuna mata yanzu gangariya, a halin yanzu baya jin kunyar ya zauna daga shi sai (shorts) a gabanta, tayi ta jin kunya kamar tace kasar ta tsage ta shige ta kuma kasa sakewa, fitsarar Da namiji da bai nuna mata a makaranta ba yake zuba mata gangariyarta yanzu, a tsakar gidansu cikin dakin aurensu. Misali yace ta zo ta cuda shi a wanka, ko sai sun yi wanka tare, amma sai ta gudu ta buya ko tace girki take zai kone in ta tafi. Tafi-tafi daga kwana bisa kilishi har suka koma kwana gado daya, ba tareda ta gano wani abu makamancin faruwar wannan tsoron nata daga Zayyan dinta ba. Gabadaya ta soma sakewa dashi yanzu, ta kuma sakankance ta saki jikinta sosai dashi dari bisa dari, ta yarda da angon nata, cewa shi daban yake, baya cikin layin irin mazan da Anti Dije ke lissafin Ustazai a waje, Devilish a cikin gida, ita mijinta bawan Allah ne mai son ta da yawan tausayinta, da gudun duk abinda zai wahalar da ita bazai iya wannan al’amarin da ita ba. Ke dai barshi da yawan tubewa a gabanta batareda yaji komai ba. Cikin sati biyu kacal Zayyan da Safiyyah suka wani irin dinke tamkar sun shekara da aure. Sai ga Sophie har ta kan rabi jikinsa ta kwanta ba tareda ta san lokacin da tayi hakan ba, in hirar falo tayi dadi kenan. Shikuma ya fara amfani da wannan damar yace kitso zai yi mata, duk yabi ya cukurkude mata sassalkan gashinta ya cukuikuiyeshi da kalba. Ga Safiyyah Masha Allah da gashin Katsinawan Dikko. Suka manne da juna tamkar tube da tyre, sallah kadai ke rabasu, in zai tafi masallaci, shima sai taji wani iri kamar in ya fitan bazai dawo ba. In ya fita din kuma zuciyarta na kansa. Allah-Allah kawai take taji motsin taba kofarsa ya dawo gida. Tafi-tafi daga sanda suka samu kansu dumu-dumu cikin sumbatar juna ma su duka biyun basu ankare ba, sabida feeling irinna kowanne lafiyayyen dan adam da ya soma aiki a jikin kowannensu. Safiyyah bata farga data fara kamuwa a tarkon angon nata Zayyan ba, sai ranar da kiss mai zafi irin (hot kiss) ya ratsa a tsakaninsu…. Daga shi ya zarce da shafar sassan jikinta kota ina da kyar ta iya kwatar kanta a ranar. Wata ranar Asabar wani (accidental French kiss) ya faru tsakaninsu na wucin gadi. Hakan ya faru dasu ne ranar bisa dining area, ta kona mishi dan yatsa da ruwan zafi garin zuba mishi tea bata sani ba. Nan Malaminki Zayyan ya samu hanyar da ya dade yana neman samu bai samu ba, ya jangabe rike da hannunsa yace sai ta tsotse dan yatsan zai daina masa zafi, “zafi yake mun sosai kamar fatar ta daye Sophie”. Ai kuwa Safiyyah a rikice, ta taqarqare ta kai dan yatsan bakinta ta hau tsotson babban dan yatsan ba tareda ta san tarko ne ya dana mata ba, kiss din da ita ta fara jinsa a jikinta kafin shi, tasirinsa ya tafi abruptly ya ratsa har tsakiyar kwakwalwar Safiyyah data Zayyan din kansa. Lokacin da tsotson y afara yin tsotso, sai jikin kowannensu ya fara dauka, suka dubi juna a rikice, a gigice, idanuwa sun birkice da sha’awar juna, duk tayi arousing dinsu, kallon da yayi mata a lokacin da barauniyar rungumar da ya yi mata ba shiri, shi ya tayar da dukkan emotions dinta na diya mace, ta kasa koda wani kwakkwaran motsi na kwatar kai. Shi kuma haduwar fatar jikinsu wuri guda ya kara birkita shi, nan suka bige da sumbatar juna a urunce, a yunwace kuma a susuce…. A wannan ranar dai da kyar suka kwaci kawunansu a hannun juna, ba tareda komai ya wakana ba. Matsananciyar kunyar shi data biyo bayan hakan ta hanata sakat har wayewar gari. Daga ranar ta saki jiki aka soma shan zumar soyayyah, har Zayyan ya soma aika manyan sakonninsa kadan-kadan cikin dabara irin tasa. Soyayyar sa mai sanyi, wani lokacin zazzafa, ta tsayawa Safiyyah a rai, ta rike ran Sophie akan mijin nata, soyayyah ta wasannin ma’aurata (romancing) kawai yake gwada mata zallarta, mai tsayawa a ran diya mace, irin ta namijin da ya san kan love, ya kuma yarda da kansa da matsayinsa a zuciyar matarsa, cewa shi abin so ne ga matarshi, da kowacce irin mace data fada komarsa. A wannan dan tsakanin Zayyan ya nunawa Safiyyah cewa shi mai tsananin sonta ne, kuma yayi hakuri mai yawa da ba duk maza zasu iya kamarsa ba, tunda ya aureta yake tattalinta da gujewa tsoron nata, don duk halin da