← Book details Heart 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 31

Sashe 17

Heart 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau Zayyan ya zo ya samu Mama a falonta, ya zauna gefenta yana sosa kai, ta harareshi ta ce “Baffana, tunda aka daura maka aure ka daina zama muyi hira ko? Ka daina samun lokacin hira dani da kannenka, bini-bini kullum kana hanyar Dandume, Dandume dai, ina ka fito Dandume, Ina zaka, Dandume. Ni ko dana ga Safiyyar nan a hoto, yadda ta gigitaka ta tafi da imaninka haka na dauka zata fi haka cika ido da daukar ido don kwalisa, sai naga abu ‘yar firit, fuska salalam ido ba ko tozali, sai dogon hanci da manyan idanu kwala-kwala kamar na mage, in ce ko sune kadai suka burgeka? Gaka Baffana masha Allah katoto da kai (giant), amma sai ka dauko mace ‘yar firit, siririya kamar karan raken takanda. Ai da ka nemo mai dan kumari kamarka da yafi”. Shi abinma sai ya bashi tsoro, don dai shi, Lillahi wa Rasulihi bai ga makusa tattare da halittar Safiyyah ba in ka cire rashin kwalliyarta kuma wannan ra’ayi ne, shima yanason kwalliya amma yasa a ransa a matsayinsa na namiji, shi zaiyi shaping mace a gidansa yadda yakeso ta mike amma hakan sai a hankali in akayi la’akari da irin background dinda ta fito, ya kan rasa gane ina Mama ta dosa kullum akan maganar Safiyyah, bata taba yabawa ba! Kullum sai ta samu abun kushewa a aurenta take barinsa ya bar dakinta, bata taba godewa halarcin Safiyyah gareshi ba na yarda da tayi ta aureshi yana dalibi, itama daliba, ba ko tunanin aikin me zaiyi ya ciyar da ita, shi ko da wannan aka barshi Safiyyah ta gama masa komai, tunda ta aureshi bisa yarda da soyayya tun bai zama abinda ya zama yau ba. Safiyyah matar sirri ce, abokiyar rufin asirinsa. Yadda take tashen kyawunnan da kuruciyar nan da kokari a karatu a ABU, da irin maneman da ya kasa a kanta, manyan mutane masu zuwa wurin mahaifinta, shi ya san mutum ko shine hasidin iza hasad, ba zai ce Safiyyah bata da kyau ba sai Mama Gwanin na Iya, wai 'yar firit ba kumari, to dambe zasu ke yi da zai dauko dirkekiya? Don haka ya kan rasa gane ta ina Mama zata yabi wani abu akan auro Safiyyah da yayi, wanda shi yasan daga shi har mahaifinsa basu saka son zuciya cikin al’marin ba sai kwadayinsu da asalinta (nasaba) da training dinda ta samu. Yace “amma Mama kinsan ba kullum nake zuwa Dandumennan ba, ko bayan daurin aure sau biyu kawai naje, mahaifinta mai ka'idane, baya son zaryar maza a gidansa, ni kuma ina kiyayewa. Ban daina zama hira daku ba Mama. Na maida hankalina wajen hattama (project work) dina don na samu na yi submitting a sallameni, shiyasa bana iya zaman hirar yanzu, kullum ina library fa Mama, itama Sophie ba son tarewar take yi ba”. Ya karasa maganar cikin damuwa da jin tausayin kansa. Mama ta yarda, don ta san Zayyan a dabi’arsa baya karya, baya munafurci ko nunkufurci, in yanason abu yana so kawai, sannan rawar kafarshi akan Safiyyah ita ta san gaskiya da sauki akan ta mazan da suka yi sabon aure, ko don bai san me auren ya kunsa bane at all sabon shiga ne? Tunda har ya bar matarsa sama da sati biyu da daurin aure a gidan iyayenta ba zancen tarewa wai tana jarrabawa, itama jan magana ne kawai don taji dadin bakinta, amma ta san ba Dandume yake zuwa ba. Yana Zaria can cikin makaranta kodayaushe, ya hada hankalinsa wuri guda ya kammala rubutunsa a wannan dan tsukin, don Baba Bello ma ya gaya mata kwatankwacin abinda Zayyan din ya gama fada mata yanzu, cewa Baban Safiyyah dan ka’ida ne, baya barin Zayyan zuwa zance barkatai. Ya kuma hana suyi mata lefe ko bikin bidi’o’in ‘yan boko. Koda aka daura auren ma yace shi in ba Safiyyah tarewa zata yi yanzun ba, to Zayyan kada ya dinga yi masa zarya ya cigaba da zuwa sati-sati bisa ka’idarsu yadda suka saba. Mama tace a ranta tabdijam! Baffa an debo aure gidan Alarammomi fiyeda haka ma za’a gani ne. Malam ya baiwa Ammi kudi masu yawa kasancewar yana noma yana fidda amfanin gona duk shekara, sannan yana kiwo, ga gudunmuwar da Sheikh ya aiko musamman don auren kanwarsa Safifi. To kacokam abinda Malam ya fidda wannan shekarar a kan kayan dakin Safiyya ya karar dashi. Ya hana Ammi sayar da filinta, yace ta ajiyewa kannenta suma ba jimawa zasu yi ba a gaban su, tunda duk suna sakandire yanzu. Ammi ta cigaba da shirye shiryen tarewar Safiyyah a hankali, ta sayi wannan ta sayi wancan ta adana, yayinda Safiyyah nata dokin ga tarewar kullum raguwa yake yi. Bata san meyasa ba, kawai taji bata son tarewar (not because she doesn’t love him). In da namiji daya data fara ji a ranta duk duniya to Zayyan Rafindadi ne, amma sam taji bata so ta tare a gidansa bayan an daura musu aure. Wasa-wasa saida aka share watanni biyu da daurin aure amma Safiyya taki ko zancen tarewar nan ayi mata. Duk wani uzuri na duniya Zayyan yayi mata a matsayinsa na sabon ango mai hakuri da iya controlling eager dinsa. Already Baba Bello ya kama musu dan gidan da zasu zauna a Zaria, kusa da makaranta, har su kammala, amma Safiyyah ta ki. Malam da Ammi tun basu damu ba, don suna ganin makon gida ne ke damunta da sabo da ‘yan uwanta, har abin ya fara damunsu suka sakawa Safiyyah ayar tambaya. Malam yace addu’a ya kamata suyi mata, watakila shaidan ya shiga lamarinta Ita kuma Safiyyah a karan-kanta ta san ba wani shadani akanta, ba komai ya hanata son tarewar ba face maganganun Anti Dije da suka tsoratata. Tun bayan da aka daura aure in suka zauna itada Antin a gidanta, ba abinda Anti Dije ke mata sai fadakarwa irin ta Aunties mata kawayen ‘ya’yansu, kuma shaqiyyan iyaye. Fadakarwar Antin akan daren farko ne, tace dare ne na musamman ga kowacce amarya, bla bla bla......ga ire-iren abubuwan da suke faruwa cikinsa. Anti Dije tace “akwai abubuwa masu ban tsoro da Sanya razani ga diya mace a cikinsa”. Tun bayan da aka daura aure Antin marikiyarta ta Zaria bata da aiki sai yi mata irin wannan hudubar akan shiga gidan aure, da koya mata abubuwan da ya kamata ta sani, a matsayinta na farin shiga, kuma sabuwar matar aure a halin yanzu, wadda ba jimawa zata bi sahun sauran iyaye mata, har Anti Dije tayi kuskuren fada mata yadda ake shan wahala a wannan daren ga budurwar da ta kai mutunci, wasu har sai an musu dinki ko ruwan zafi, sannan tace in ta warke kuma sai harka ta balle a koma soyayya, nan ta shiga koya mata salo-salo na shimfida da sauransu baro-baro. A matsayin ta na karamar uwarta mai shirin kaita dakin miji, Anti Dije da karambani irin nata taga ya kamata ta koyar da diyar tata duk wannan. Kada ta barta a dukunkune taje ta rasa yadda zata yi. Don ta tabbata Safiyya banda text books dinta na Architecture bata karanta littafan soyayya koda na turanci ne. Kuma ta san Ammi bazata taba yin irin wannan hirar da itaba. Amma ga Safiyyah diyar Ammi da Anti Dije, maimakon hakan yayi amfanin da ake zato, wato ya zama karin ilmi a gareta da wayar da kai, sai ya zama akasin haka, duk Aunty Dije ta hargitsa mata tunani akan aure. Ta koma anticipating ranar first night dinta shine kwatankwacin ranar mutuwarta. Domin daga hudubobin Anti Dije Safiyya ta fahimci ai wata sabuwar rayuwar ce ke jiranta daban da wadda suke yi da Zayyan kafin aure, Anti Dije ta yi instilling tsoro mai yawa a Safiyyah, don sai ta kai ta kawo ko cewa akayi Zayyan ya zo sai gabanta ya yanke ya fadi, sai kuma taji bacin rai wanda har a fuskarta sai ya nuna. Tayi ta tambayar kanta ta yaya ma za’ayi ace abubuwan da Aunty Dije ke fadi zasu faru tsakaninta da abokinta Zayyan, ai akwai kunya, kasancewar hirar soyayya da kauna data karatu ce blah… blah… kawai tafi gudana a tsakaninsu (very pure gist) koyaushe Zayyan bai taba wuce limit dinsa ba. A takaice Aunty Dije ta gama nuna mata cikin rashin hikimar zance akwai muhimmin abinda ke jiranta duk ranar data tare daga salihin mijinta dan mutanen Rafindadi, wanda take yiwa kallon aboki, masoyi, amini. Bayan daurin auren har wasu magunguna ta soma bata masu dadin ci na “Bojuwa Herbals” wato kayan gyaran auren nan na musamman na kawarta (Aunty Surayyah Halin Yau 08032773332) tace rayuwa ce zasu fara wadda sai an kai zuciya nesa, saboda nauyinta. Tace mata wannan shine zahirin auren hakikaninsa, asalin abinda ya saka mata tsoron tarewar gabadaya. Duk da Zayyan bai taba nuna mata wani abu daban mai nuna hakan ba, tun kafin ayi auren da bayan an daura shi, bayan an daura ma rage zuwa yayi, amma Anti Dije tasa mata tsorata dashi sosai kamar mala’ikan da ke jiran ta shiga gidansa ya dau ranta, da take gaya mata abubuwa kuru-kuru, abinda Ammi bata taba zama ta gaya mata ba, saboda kunya da fulatanci irin na iyayen da, kuma ita bata kawaye bata kuma karance-karancennan na zamani da ire-irensu. Antin nata Dije tayi mata (sensitization) ne na kai tsaye (ba cikin hikima ba). Kamar ace Anti Dije irin matan nan ne masu barin zance da rashin sakaya shi cikin hikimar harshe, har cewa take da Safiyyah idan ta nuna bata son hirar. “To nifa ban gane ba Safifin Ammi, wai kina nufin shi Zayyan din bai taba nuna miki yana bukatar komai daga gareki bane tun daurin aurennan ko yaya ne? To idan yazo Dandumen haka kuke wuni baya komai a gabanki sai zuba zance kamar lalataccen famfon I love you na fatar baki? Safiyyah ta dukunkuna fuska tace “Anti meyasa kike min haka ne? ni Zayyan bai taba yimin irin wadannan zantukan na rashin kunya da kike min ba”. Anti Dije ta kai mata dundu tace “nice mara kunyar? To ko dai baida lafiya? Koda yake fa irin shi in sun samu wuri, sun fi kowa jarabar matansu, tunda Ustazi ne, to ke wai kin dauka in kun tare ma haka zaku cigaba da zama cikin ustazancin kamar
Chapter 17 · 0% Book details