← Book details Heart 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 31

Sashe 12

Heart 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a yarinya mai shegen ji da kai da tsokanar ‘yan uwanta, ga yawan shagwaba da yawan raini ga Yayyenta, da rashin jin maganar kowa har Maman kuwa, Baba kadai take shakka a gidan sa Yaya Baffa, sabida Mama ta daure mata gindi, kowa yazo da korafi akan auta yanzu zata tare mata fadan ta ara ta yafa. Mai dan dama-dama a hankali da cikar tarbiyyah cikin ‘ya’yan Mama Fatu mata to Yayarshi Zubaina ce, Zubaina ta kan dade bata zo gida Rafindadi ba, don mijin ta irin mazan nan ne masu mugun kulle ga matansu, suka kuma isa dasu. In ka cire Zubaina kafatanin duka ‘yammatan Mama halayenta suka debo. Yaya Zubaida kuwa ai makwafin Mama kenan a halayya da dabi’a. Zubaina ce kadai mai hangen nesa cikinsu saboda mijin data aura malamin makaranta ne duk ya canza halin Zubaina zuwa irin wanda yakeso bayan ya aureta. Mama ana yawan zugata da cewa ‘ya’yanta mata ai jarin ta ne, tunda Allah ya bata su kyawawa tamkar ita ta kera abinta don kyawun sura, wannan yasa Mama ta dora buri sosai a kansu, da zuwan aurensu Zahrah, burinta kadai suyi auren hutu a inda zasu huta itama ta karu, ba irin auren da Baba Bello yayima Zubaidah da Zubaina ba, suma kuma su Zahran saboda yawan hudubobin Mama na kada su sake su kawo mata dan (I love you) ko mai fama da alli yasa suka tashi da burin sai wanda ya kama kasa ya tsaya da kafafunsa zasu aura, wannan yasa har gobe ‘yammatan Mama babu suna nan zube a gabanta, babu mai tsayayyen saurayi, kowa yazo Mama zata ce bai isa ba, me yaci balle ya basu? Gashi dai har Zaitoon da Zahra sun fara jarrabawar shiga aji na uku a jami’a yanzu babu tsayayye. Mama da ganin ta ka san an zuba kyau a zamanin ‘yammatanci an kuma yi ruwan idon samari kafina tsaya akan Bello Rafindadi, kuma har yanzu in ka dubi Mama zaka ganta da kyanta da gayunta, ga koshin lafiya da kuzari, gata da ingarman jiki, saboda samun kyakkyawar cima da take yi da kulawa daga Baba Bello, wanda zai iya kwana da yunwa ita ya bata, kyawun surarta bai buya ba har yanzu, duk da a halin yanzu Mama ta baiwa 60 baya. Mama tayi aikin koyarwa na lokaci mai tsaho a babbar makarantar ‘yammata ta gwamnatin jihar Katsina, bayan ta haifi auta Hatoon sai ta bar aikin, ta karkata kan kasuwancin atamfofi da lesika da mayafai na matan zamani, kuma kasuwancin sai ya karbi Mama sosai fiyeda koyarwar. Don a karshe daga shagon cikin gida har ta kai ga bude shago a kasuwa, na atamfofi da lesika, inda take harkokin kasuwanci bisa kulawar ma’aikatanta. Shi dai ya san babban nakasun Mamansu Hajiya Fatu, wanda Babansu ya sha gaya masa baya so, a matsayinsa na da daya namiji garesu sai ya zama babban aboki ga Baba wanda yake tattaunawa dashi akan komai da ya dameshi, Baba ya sha gaya masa abinda baya so a tareda Mama shine halinta na raini da take nunawa ga na kasa da ita, in har ta fika arziki to kuwa dole zata rainaka, ko daga kalaminta. Bazata taba hada kafada da kai ba, wada ‘ya’yanta mata kusan duk sun dau wannan halin, basu da mai tsawatar musu su ji sai Baba Bello da kansa. Ko shi Zayyan din in yayi yunkurin ladabtar da kannensa nan da nan Mama zata taka masa burki. Zayyan ya sake juyawa wani irin juyi mara dadi akan makeken ni’imtaccen gadonsa, sai ya ja numfashi ya sauke a hankali cikin tunanin sha’anin gidansu, ya kuma kara da lumshe idanunsa yana mai fuskantar ceiling. Baya son tuno duk abinda ya shafi Baba Bello yanzu, domin yana yi masa fami akan warkakkeen gyambon rashinsa dake ransa ne, amma ya zama dole yake tuna Baba da rayuwarshi tare dasu bakidaya, su kuma dinga dawowa cikin tunaninsa lokaci zuwa lokaci saboda Baba Uba ne da babu irinsa a wannan zamanin. Daga nan Zayyan ya kara nausawa cikin tunanin da ya samu kansa, duk a kokarinsa na son nemo adalci ga kansa, da maidakinsa Nana Safiyyah a daren yau ta hanyar yiwa kansa (self-judgement and self-evaluation), bayan tuni aikin gama ya rigada ya gama, ko yace bakin alkalami ya gama bushewa. **** **** **** A Ranar, abinda ya faru bayan ya dawo daga Dandume shine, ya dawo gida da farin cikin amincewar iznin neman auren Safiyya da mahaifinta Mallam Usman ya bashi, kai tsaye bai tsaya ko’ina ba sai falon Mamanshi Haj. Fatu. Yana saka kafa a falon Mama, bakinsa dauke da sallama cikin doki da kaikayin baki, da kafafun Hatoon ya fara cin uban karo a bakin kofa, suka tadiye shi har suka kusa fadar dashi a kasa. Haushi ya kama shi. Ya juya ya kalleta da manyan idanunsa, tayi shame-shame a bakin kofa wai ita tana azumin ramuwa, lokacin ana gab da shan ruwa, autar Mama ta kai makura wajen galabaita, don kuwa azumin ma saida taji wa’azi a radio na hukuncin marasa ramashi sannan ta fara ramawa lokacin azumin bana saura kadan ya kama. Hatoon ta kusa kayar dashi a kasa sosai, a fusace yasa kafa ya shureta da karfi, nan da nan Hatoon ta saka karar kiran Mama, tace da karfi “Mama kizo. Yaya Baffa na dukana!” Sai ga Mama ta fito daga daki da sauri jin sautin kukan Hatoon, kamar wadda aketa duka, shurinta kawai yayi da kafarsa, amma ta bare baki tana kukanta na sangarta mai ban haushi, Mama tana ganin sa a gaban Hatoon ta ce. “Ha’an! Tunda naji kukan Hatoon alhalin tana azuminnan da sanyin yammacinnan na san anci zalinta da mangaribar fari, kuma ba kowa bane sai kai Baffana, to juya ka bar min falo, tunda bani na kiraka ba”. Zayyan bai damu da fadan da Mama ta rufeshi dashi ba, don inda sabo sun saba, haka bai ji gargadinta na ya koma inda ya fito bata gayyatoshi ba, sai ya shigo falon ya zauna ya harde kafafunsa yana hararar Hatoon, yace “zaki tashi daga wannan banzar kwanciyar a bakin kofa, ko sai na babballaki in yaso kiyimin ihu da hujja? Yanzun don Allah da kin kayar dani fa?” Mama tace “a’ah fa. Baffa ka san Allah, tunda dai bamu kira ka ba, kuma ba maganar arziki ce ta kawo ka ba, to ka koma inda ka fito ka saurarama Hatoon, bana son diban albarka akan yarana ka sani daga kowa har su da kansu kuwa, me ta tare maka haka kake neman cinyeta? Ina dalilin wannan tsangwama? Azumi fa take yi, in baka tausaya mata ba, ai baka hantareta ka hau shurinta daga shigowarka ba”. Ba don Mama bace take maganar nan, tabbas da ya kaiwa bakin Hatoon kyakkyawar mahangurbar da zata kumbura mata bakin, don yana kallonta tana gatsina baki irin dai wanda ta saba yiwa yayyenta in taji Mama na tare mata fada a wurinsu. Kwafa yayi, yayi shiru ya rabu da ita, don in ya sake ya tabata zai fuskanci fushin Mama, haka kawai tasa an gwasale masa farin cikin da ya zo a cikinsa. Don haka yace. “Mama kiyi hakuri, ni ba maganar wannan sakaryar ‘yar taki ce ta kawo ni ba, in fact, ko me zaki yimin yau a kan ta bazan ji haushi ba, bazan kuma wani damu ba, tunda ai na riga da nasan kinfi sonta a kaina, to na me zan damu don kin koreni a gabanta? Ni ranar yau daban take a wajena; ina cikin matsanancin farin cikin da sakarcin Hatoon yayi kadan yasa inyi fushi yau. Mama ta samu wuri ta zauna cikin rashin kulawa da zancen tace “to yaya akayi?” Yayi murmushi cikin ‘yar alkunya da sosa keya kafin yace. “Mama ni yau nayi gamon alkhairi fah, irin albarka, tsatson martaba, yau dai Allah ya nufa na isa ga gidansu “HIJABIE!!! Na kuma gabatar da kaina ga mahaifinta”. Mama na wani irin yamutsa fuska da baki cikin gatse tace “wacece haka? Wane irin suna ne Hijabie ni ‘ya su? Sunan yanka ne ko sunan rana ko hijab da ake sakawa aje masallaci yin sallah?” Ya sunkui da kai jin abubuwan da Mama ta zano, kafin yace “Mama Yarinyar nan mai hijabs da jilbaabs da nake yawan baki labari ina haduwa da ita a school Library? Kuma alhamdulillah mahaifinta ya bani damar fara saka kai ga neman auren ta”. Budar bakin Mama Fatu sai cewa tayi “lallai Baffa ka girma! Ni yau naga abinda ya girmeni, kai nan har wani aure ka isa Baffana? Nawa kake? Cewa nake ko 27 Baffa baka kai ga rufawa ba? Tukunnama, diyar waye a Katsina ita Hijabie din? Ina nufin WAYE UBANTA?” Tunda a halin yanzu me ka aje, me kuma kake dashi da zaka baiwa iyali, aikin me kake yi da zai rike maka aure?” Mama Fatu ta tambaya da accent dinta na Katsinawan Rumah. Cikin balbaleshi da fada da tada jijiyar wuya. Zayyan saida ya bari Mama ta kai aya, tunda yasan halin kayarsu, sai ya kwantar da murya don ya riga ya san halin Mama na saurin daukar zafi da izgili, cikin lallashi yace, “ba sunanta Hijabie ba Mama, nine na saka mata hakan sabida kyawun da Hijab da jilbab ke mata. Sunanta Safiyyah, diyar Malam Usman Dandume, mahaifinta babban Alaramma ne (Shaihun malamin addini) mai bada karatun addini ga magidanta da almajirai a garin Dandume”. Abinda shi bai fahimta ba tun a lokacin shine; wannan matsayin na mahaifin Safiyyah da shi yake ganin abin alfahari ne da bugun kirji wajen zaben abokiyar rayuwa da yayi, a wurin Mama Fatu shine first disappointment (sagewar guiwa na farko) data fara samu akan Safiyyahrsa, na kasancewarta ‘yar malamai, wanda ko kusa baya cikin tsarinta kuma bai zo cikin tunaninta ba, na irin surukan data ke burin hada zuri’a dasu, sannan gata ba ‘yar manyan ‘yan boko da sukayi shuhura a bokon ko wasu masu dukiya ba, domin nan take Mama cewa tayi tun kafin ya gama rufe bakinsa. “Hadin gambiza Baffa?! Wannan shi ake kira hadin gambiza. Me ya hada dan Furofesa da diyar alaramma na kan buzu kuma? Kai Baffana bana son rigima mai lasisi. Haka kawai inje a tattofe min kai da laqanquna a rubuceka a minjaye a shanye, a mallake
Chapter 12 · 0% Book details