Sashe 6
Heart 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
FARKON FARI Garin Dandume gari ne da Allah yayiwa albarkar noma da yalwar lafiyar kiwon dabbobi. Galiban al’ummar Dandume manoma ne da ‘yan kasuwar gona, sannan da makiyaya, Dandume tsohon gari ne dake cike da tubarrakin manyan malamai na addinin musulunci kamar dai mahaifin su Safiyyah. Safiyyah ta taba bashi labarin cewa ita FGGC Bakori tayi, kuma ta yi nasarar lashe jarrabawar JAMB da tayi a boye bada sanin mahaifinta ba, saboda ya sha alwashin shi aure yakeso zai yi mata da zarar ta gama karatun sakandire in dai miji ya bayyana, saboda shi Malami ne na kwarai, bazai lamunci komai ba sai tafiya gidan aure bautar ubangiji. Cikin ikon Allah kuma ta samu ta haye Jamb din, da yakkyawan maki mai burgewa. Tace hatta form din Jamb din, dan uwanta “Yaya Shaikh” ne ya saya mata a boye. Kasancewar ita da Yaya Sheikh kusan a komai bakinsu daya cikin gidansu, sun saba su kashe su rufe itada shi, ba tareda ko Malam da Ammi sun sani ba, sun kasance aminai ne bayan ‘yan uwantakar jini mafi kusanci dake tsakaninsu. Itada Yaya Sheikh (‘yan maza zar suke). Da mahaifinsa mai rasuwa Malam Abubakar da mahaifinta Malam Usman uwar su daya ubansu daya. Bayan rasuwar mahaifinsa ne Malam Usman ya dauke shi hannunsa, sai ya damka shi a hannun Ammi, wato mahaifiyarsu Safiyyah, kasancewar shikadai iyayensa suka haifa. Daga ita har Yaya Sheikh, duk suna da ra’ayin tayi karatu boko har zuwa jami’a, akan passion dinda take so tun tana karama, Safiyyah tana na yarinya ba abinda ta kware a kai a makaranta irin ‘Zane’, kasancewar Art class tayi, ba abunda bata iya zanawa yayi kyau ya bada suffa mai ma’ana ba, wanda yake sabanin ra’ayin mahaifinta, da suke kira “Malam” wanda kasurgumin Shaihun Malamin addini ne. Ya kan ce shi bai ga komai na amfani a cikin Zane-Zanen da take cika musu bango dasu ba. Safiyyah ta cigaba da bashi labarin cewa, “saboda haka sabanin sauran ‘yammata irina da iyayensu ke raye har zuwa wannan lokacin, zaka ga iyayen ne da kansu suke fafutukar nema musu gurbin karatu a jami’a bayan kammala sakandire, don basa son ajiyesu a gabansu basa komai, “amma ni Safiyyah abin ba haka ya kasance a gareni ba, na san na shigo jami’a ne kawai (by chance)”. Wato ta samu shiga makarantar ne bisa yardar Ubangiji, da ya riga ya rubuta mata ita a kundin kaddarorinta, cewa zata yi boko mai zurfi ko Malam baya so, da kuma karfin addu’ar data kwana yi akan mahaifin nata, kafin ta doshe shi da takardar samun gurbinta a safiyar ranar da sakamako ya fito. Tace tayi addu’a sosai, ta kuma sa kananan kannenta uku mata Sabah, Rayyah da Rayha sun tayata, wadanda akwai ratar shekaru biyar tsakanin ta Sabah, sauran biyun kuwa wajen shekaru bakwai da takwas ta babbasu, tace sun taya ta addu’a ta basu sadakar cakulet sukayi ta murna, akan Allah ya dorata akan mahaifinta ya lamunce mata zuwa jami’a a birnin Zazzau. Malam ya riga ya horesu da yin addu’a da tsayuwar dare cikin talatainin dare, akan kowanne lamari suke so Allah ya shige musu gaba a kai, don haka shima Malam bai tsira ba, a cewarta ta kai kararsa sunansa ne gaban Ubangiji akan bukatarta da zazzafar addu’a har da sadaqah wa kannenta. Mahaifinta Shaikh Usman Ameen Ladan Dandume, fitaccen malami ne na addinin musulunci a kauyen Dandume, ba malamin allo bane malamin buzu ne, dake karantar da magidanta da samari, kowa ya san zaiyi wuya a rikon addini irin na Malam Usman ya bar babbar diyarsa taje jami’a har wani gari wai Zazzau, ba tareda igiyar aure a kanta ba. Tunda shi da kansa yake bada fatawa ga iyaye maza dalibansa a kauyen Dandume, ta hanasu barin ‘ya’yansu mata sakaka a jami’o’i batare da aure ba. Malam Usman sananne ne a wurin tsaurin tarbiyyah, mutum ne mai kokarin kiyaye dokokin Ubangiji a gidansa, don ya kiyaye hadisin da yace “in kuna tsoron bazaku iya adalci ba, ku auri dai-daya”, shiyasa har zuwa yanzu da ya cimma shekarun girma, furfura ta sauka, bai kara auren wata mace bayan Amminsu Safiyyah ba, an sha kawo masa sadaqar ‘yammata iri iri daga kauyukan Katsina daban daban baya amsa, saboda Allah shaida ne akan Mallam yana mutunta Ammi, yana martabata, yana mutuwar sonta, duk da kasancewarta uwar ‘ya’ya mata zallah a gareshi. Bata taba haihuwar masa Da namiji ba. Tun kafin a haifi su Safiyyah malam na rikon Dansa Ridhwan da suke kira “Yaya Shaykh” wanda ya kasance da ga dan uwansa Abubakar da ya rasu a hatsarin mota, mahaifiyar Ridhwan kuwa tun wajen haihuwarsa ta koma ga Ubangiji, don haka Sheikh maraya ne, Ammi ce ta raine shi da nonon shanu. Bai tashi ya san wasu a matsayin iyaye ba bayan Ammi da Malam. Har ila yau Malam nada wani yaro almajirinsa da ya rika kamar Da mai suna Haroun, yaron da aka kawo masa almajirci daga Geidam ta jihar Yobe. Don haka a lokacin da tayi jarrabawar (jamb) ta kuma ci, sai Yaya Sheikh ya nemo mata gurbi a ABU ta hanyar wani almajirin Malam mai yawan zuwa gidansu gun Malam wanda ma'aikacin ABU ne (non-academic staff), Malam bai sani ba haka Ammi daga sanda taje ta rubuta jarrabawar har gashi ta ci, daga ita har Yaya Sheikh sun san sun yi karambani, amma sun yarda addu’a bata bar kowa ba, basu taba tunanin Malam zai barta zuwa jami’a har a wani gari can, bama cikin Katsina ba, ba kuma nasu garin Dandume ba. Ita kuma Safiyyah Allah ya sani, tun tasowarta babu makarantar da take burgeta take bata sha’awa a fadin Najeriya irin Jami’ar Ahmadu Bello, wannan ya samo asali daga kanwar mahaifiyarta Anti Dije dake aure a Zaria, kuma tayi aiki a ABU kafin ta bar aikin ta zauna a gida, a lokacin da Anti Dije ke can tana yawan zuwa hutu wajenta, Anti Dije na yawan bata labarin garin Zaria da manyan makarantun dake kunshe cikin garin. Ta kan ce “Zaria gidan ilmi ce kacokam! In kin tashi karatu Safiyyah ki taho Zaria, don samun kwali mai nagarta, saboda babu jami’a mai tsohon tarihi a arewa kamar Ahmadu Bello. Ta san dai akwai taimakon addu’arta, domin ta roki Allah idan karatunta alkhairi ne ya baiwa mahaifinta ikon barinta salin-alin cikin sauki, idan kuma babu alkhairi kada Allah ya bata ikon tambayarsa ma, ta yiwa Ubangijinta alkawarin kare mutucinta dana addininta dana iyayenta, in har Malam ya lamunce mata zuwa karatun, ta hanyar yin shigar da zata kare martabarta data addininta, ta tsarkake idanun maza a kanta, wadda a cikinta suka taso itada kannenta mata dama, wato shiga ta kamala (Hijabs), ta yiwa Ubangiji wannan alkawarin tsakaninta dashi cewa karatu kadai zai kaita Zaria, bata da wata manufa bayansa, muddin ta samu yarjewar Mallam in ta shiga ABU bazata canza halaye da dabi’unta daga yadda suke a Dandume ba. To shi Ubangiji a kullum niyya yake dubawa da tsarkin zuciyar bawa kafin ya amsa masa addu’a. Cikin hukuncin Ubangiji Allah ya amshi rokonta, don yaga tsarkin niyyarta karatun ne kawai a ranta. Malam Usman Dandume ya sahale mata zuwa ABU babu ja’in’ja. Yace ba don komai ya amince ba sai don cewa itace babba cikin ‘ya’yansa, kuma dukkansu ‘ya’yansa mata ne, mata kuma masu rauni ne da kaunar juna by nature dinsu, don haka itace uwar kannenta da zata dauki takalihunsu ranar da basa nan shi da Ammi, ko ranar da karfinsu ya kare tunda basu da Da namiji a cikinsu bayan Yaya Sheikh, don haka dole ya bata damar yin ilmin addini dana zamani, a matsayin jarin da zai iya bata kadai itama ta basu (kannenta). Malam ya rufe zancensa da cewa “kowa yayi da kyau ya sani Safiyyah, in bana ganinki Allah daya halicceki yana ganinki, ya kuma san irin tarbiyyar dana baki da abinda zaki je ki aikata a bayan idona”. Wanan ne yasa Safiyya zama wata irin Kamilah, khashi’ah, khalisah, kamammiya, zaqaqura, zealous (mai himma) kuma smart a jami’ar. Take yin rayuwarta daidai da ita, ba rawar kai ba kidifiri. Ba karya ba kawayen banza, ba sakin fuska ga kowa walau mace walau namiji, Safiyyah taki sabo dakowa, don ma kada a abokantaketa a bata mata tunani, a shiga lokacinta, na abinda ya kawo ta, yasa hatta matan ma bata kulawa ba maza kadai ba, lokaci abu ne mai matukar muhimmanci a gurin Safiyyah, da bazata iya karar dashi akan kawancen makaranta ba, idan kuma hanya ta kure kun hadu Safiyyah zata yi maka sallama ta musulunci shikenan. Kullum fatanta Allah ya fiddata kunyar Mallam, da yardar da yayi ma tarbiyyar da ya bata. Safiyyah kyakkywar ba-katsina, kalar fatarta kamar ruwa biyu, hancinta da bakinta kamar na mutanen kasar Habasha (Ethiopia) ga wadatar sumar kai data gira. Ga lumsassun idanu masu matukar daukar hankalin wanda duk ta kalla dasu ba maza kadai ba. In har bai manta ba, silar haduwarsu kenan, watau zuwanta jami’ar Ahmadu Bello da shekara daya da ‘yan watanni, tana kokarin shiga aji na biyu wato (level two). Daga wancan lokacin zuwa shekaru goma da doriyar watannin da suka shude da yasan Safiyyah, to a jami’ar Ahmadu Bello ya fara saninta, ya kuma ganeta ne daga uniqueness na sautin muryarta (in’ina ce da ita), sautin da ya bambanta dana sauran mata, har kuma zuwa inda yau ke motsi, bai manta sautin in’inarta da yaji na farko shi yasa shi juyowa ya kalleta ba. In’ina ba dadin saurare gareta ba, amma shine sautinta daya fara shiga kunnensa ya zauna, har gobe sautin yana nan a kunnensa, yana shawagi a kwakwalwarsa, yana masa amsa-kuwwa, don shi dadi sosai in’inar tayi a kunnensa, his fondest memories da ita kenan a kullum; (in’inarta). Sautin da har yanzu ya kan sake yi masa amsa-kuwwa, lokaci- zuwa lokaci, idan ya tuno Safiyyah, bai mance shi ba, kuma bazai mance din ba, domin dadin da sautin in’inar yayi masa yaki bacewa daga cikin memory dinsa. Wani irin sarkakken sauti Safiyyah keda shi, mai ‘yar gargada (stammering) wanda dai-daikun mutane kadai Allah yake jarrabta da ita. In’ina wata lalura ce ta furta magana da kyar, ko kana yi tana makalewa, ko kuwa hardewa da ‘yar gargada haka, kana yi kana kwatota daga makoshinka da kyar,