Sashe 11
Heart 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da ya gani mai girma, ya kara masa kaimi da ninkin son hada iri da mahaifin Safiyyah. Don haka a ranar bai ko nemi ganin Safiyyah dake cikin gidan ba, bayan sun gama magana da Alaramma Usman sai kawai ya juyo gida cike da wani irin farin ciki, da doki da zumudi mai yawan gaske, ya isa gidan iyayensa a Rafindadi. Ya san daga Baba har Mama zasu yi farin ciki da irin gidan daya nemo aure. **** **** **** WANENE ZAYYAN? T unaninsa ya mika ya tafi ga ainahin asalinsa, tushensa da tarihin iyayensa. Iyayensa duka Katsinawan Dikko ne na asali, gidan mahaifinsa babban gida ne ginin zamani, yana nan daga farkon shigarka shiyyar Rafindadi, wanda a yanzu ya zama ‘landmark’ na kwatancen kowanne gida a unguwar, misali da ka ce “layin gidan Bello Rafindadi” ko yaro karami zai nuna maka. Mahaifinsa Arch. Bello dan asalin shiyyar Rafindadi ne, gabansa da bayansa can aka haifeshi, iyayensu da kakanninsu sune tushen kafa/assasa Rafindadi a Charanchi. Gidan Bello Rafindadi ya fita dabam ne a unguwar kasancewar yafi duk wani gida a unguwar girma da fadi da daukar hankali, kai har ma da kyawun tsarin gini, wanda akayi bisa doron ilmin abin, don hatta ginin gidan, Prof. Bello Rafindadi shi da kansa ya zauna ya zana ya tsara ya kuma gina abinsa daidai da yadda yake so, kuma daidai da yawan ‘size’ din iyalinsa. Tsohon dan bokon da a halin yanzu yayi ritaya. A can baya kafin ya mallaki wannan gidan da suke ciki shida iyalinsa suna zaune a karamin gidansa na gado duk a unguwar ta Rafindadi. Arch. (Prof.) Bello Rafindadi ya rike mukamai iri-iri a jami’o’in arewa, mukami na karshe da Baba Bello ya rike shine na “Chancellor” a jami’ar Umaru Musa ‘Yar Aduwa, Katsina. A lokacin nan da Zayyan ya gano Safiyyah, Baba Bello bai jima da yin ritaya daga aikin gwamnati ba. Bayan ritayarsa, Baba Bello bai zauna a gida ba kamar sauran retirees, don har lokacin da sauran karfinsa da koshin lafiya, in ka ganshi ma bazaka yi tsammanin yanada shekarunsa ba sabida yadda yake kula da lafiyarsa, yana barin koyarwar jami’a sai ya koma kacokam ga harkar karbar kwangilar gini data zana gidaje, ginin ma’aikatu da ginin Estates ga gwamnati. A hankali ya soma samun kwangila sosai daga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Katsina, bisa taimakon abokinsa amininsa tun na kuruciya kuma ubangidansa a harkar Zane da gini, wanda shi ya tsunduma shi a harkar kwangilar gine-gine, kuma shi yake taimaka masa wajen samun wadannan kwangilolin, wato Alhaji Murtala Masari. Bada jimawa sunan Baba Bello ya kara fita a Katsina a matsayin babban contractor na gine-gine da zane-zane ga gwamnatin jiha data tarayya. Arch. Bello da maidakinsa Hajiya Fatima, wadda kowa yake kira da “Mama Fatu”, suna tare tun aurensu na saurayi da budurwa, duk wani fadi tashin rayuwa na Baba ya sameshi ne tareda Mama Fatu. Haihuwarsu ta farko sun fara ne da haihuwar yara mata har biyu, kafin su samu haihuwar Zayyan a matsayin namiji na farko, kuma Da na uku a gidansu. Babbar Yayarsu Zayyan Yaya Zubaidah tana aure ne a garin Batsari, sai Yaya Zubaina ita kuma a Kano take aure. Zaituna da Zahra da Hatoon ‘yammatan Mama duka suna gaban ta, Zaitoon da Zahra suna jami’ar Umaru Musa, a mataki da tsangaya daban-daban yayinda autar Mama Hatoon take ajin karshe a sakandiren ‘yammata ta FGGC Gusau. Shine Da na uku kenan a gidansu, wanda ya biyo ‘ya’ya mata biyu a haihuwa, uku kuma suka rufa masa baya shikuma. Mama Fatu sautari in tana hira da manyan kawayenta zaka ji tana fadin Baffa wato (Zayyan) ya iya zama da mata, don cikinsu aka haifeshi, cikinsu ya tashi, ya san halinsu ya san rauninsu, yana yawan tausaya musu”. Wani Zubin kuma Mama kan ce “ko wacece tayi sa’ar zama matar Baffa ta huta. Don zata ji dadin zama da shi, ya iya kula da mata tun yana yaro. A cewar Mama da wuya ya zama mijin mace daya, wato bazai iya zama da mace daya ba, don ya riga ya saba da zama da mata da yawa. Wannan hasashen Mama ne a matsayinta na Uwa, domin hakika Zayyan yanason sisters dinshi, yana tarairayar bukatun ‘yan uwansa mata fiyeda komai. Duk wani aiki mai wahala na kitchen ma baya barinsu suyi, shi yake karba yayi mata, daga yayyen nasa har kannen nasa sunada matsayi mai girma a gunsa. Ya zamanto tun daga kan Hatoon Mama Fatu bata sake ko batan wata ba, gashi Hatoon nada shekaru 18 a halin yanzu. Tun fil azal a bayyane yake ga kowa cewa Baba Bello na matukar son Mama Fatu. ‘Yar lelen shi ce ta ko’ina, yana ji da Mama Fatu ya tsoka daya a miya, bai taba tunanin yi mata kishiya ba kuma bai hada matsayinta dana kowacce mace a gurinshi ba. Mata irin Mama ake kira shalelen maigida, bata laifi a gun Baba Bello, saidai kuskure, wanda yake mata uzurin shi komai girmansa a koda yaushe. Baba baya yiwa Mama iyaka da duk abinda ya mallaka. Komai ya samo nata ne da ‘ya’yanta, danginsa duka a cewarsu sun gama sallamawa Haj. Fatu Prof. Bello ta mallakeshi daga kai har kafa. Kowa dai ya san yadda matan Rumawan Katsina suke dauke hankalin mazajensu da yadda suka iya biyar da mazajensu ta hanyar mulkar gidajen aurensu tsaf. To Mama Fatu ta kasance daya daga cikinsu, irin matannan ne ‘yan hutu wanke goma tsoma biyar a gidanta, dari bisa dari mijinta Baba Bello ya tsaya mata saboda son da yake yi mata yasa ya sakar mata komai nasa. Kowa ya shaida cewa sun fahimci juna itada Baba fiyeda duk yadda ake zato, ba wanda ya isa ya kushe halin Mama a gun Baba Bello yanzu za iyi hannun riga dashi, Mama tana da kirki iya kirki, amma fa a zahiri, Mama Fatu macece mai son kanta kwarai da son ‘ya’ya har ya wuce kima, in kana son zaman lafiya da ita kada ka taba mata ‘ya’yanta ko kace ga laifinsu, ‘ya’yanta sun fi na kowa matsayi a gunta. Bata da kara sai keke-da-keke in dai akan ‘ya’yanta ne. Rayuwa ake ta hakika wadda babu karya a zaman Baba Bello da Mama Fatu. In yana dashi ta sani, haka in babu ta sani. Sun taso tun kuruciyarsu a haka cikin son juna, ya hadu da Mama ne a garin Rumah da yaje wani aikin koyarwa na sa-kai (voluntary teaching) bayan kammala sakandirensa kafin fitowar admission dinsa zuwa jami’a. Baba yana matukar tattalin Mama da tattalin farin cikinta, zamu iya cewa a takaice Baba Bello shine komai dinta a duniya. Saboda Bello ya Aureta tun bata kare makarantar gaba da firamare ba, amma da taimakonshi da tsayuwarshi akanta sai da ta kai har matakin NCE, tana karatun NCE tana haihuwar yaranta a jejjere. Baba Zayyan baiyi wasa da tarbiyyar yaranshi ba ko kadan, duk da anso a samu matsala ta fannin Mama Fatu, ta kasance me matukar rauni akan tarbiyyarsu saboda soyayyarsu, don ko Baba ne yake musu fada wani lokacin zaka ga ranta yana baci, hancinta yana bubbudewa tana wani irin canza fuska da cin magani. Baba ya karanci halin matarshi tsab, don haka sauda dama baya musu fada a gabanta saidai ya kebe dasu, duk da baya son bata mata rai yana yawan tsawatar mata akan sangartar da take yiwa yaran, musamman auta Hatoon da ta haifeta a shekarun girma, tana da rauni akan tarbiyyarta, shiyasa yarinyar ta tashi a sangarce, don zaki ga wani abun ma tsoron idon Baba ne yasa takeyi ba tsoron Mama ba. Ko akan zuwa islamiyyah Baba ya sha tasa su Zahra a gaba ya kora su da dorina, ko yaje makarantar yasa a zanesu tsaf, amma fa a bayan idon Mama, don in sunce wa Mama sun gaji bazasu je Islamiyya ba, nan da nan zakaji Mama na fadin “to a barwa gobe”, in kuwa makara sukayi nan zaka ji tace bazasu je ba, ba gardin da zai bugar mata diyoyinta, su zauna a gida suyi bita su huta sai gobe. Zafin neman ilmi ba shi ke sawa ayi kudi ko ilmin ba. Ita ai NCE kawai tayi, me ta rasa a rayuwarta? Mai cin abin hannun Mama kuwa sai ‘ya’yanta. Mama akwai rowa. Baba duk inda zai taka a fadin kasar nan da Mama Fatu yake zuwa, don haka ko a cikin tsararrakinta zaki ga ita tana da wayewar kai sosai, sakamakon zama da rikakken dan boko irin Arch. Bello Rafindadi, sun yi yawon bude ido ita dashi sosai a gari-gari a cikin kasar Nijeriya, duk wani wajen hutawa da buda ido a arewaci da kudancin kasar nan Baba da Mama sun taka shi. Haka siddan zasu dauki hanya su tafi suyi sati a Yankari itada Baba in suna son hutawa daga haniyar gari data kacaniyar yaransu. Rufin asiri daidai misali a lokacin Baba Bello nada shi, kuma mutum ne da bai san dadin abun hannunsa ba, me son ‘yan uwanshi da na Mama Fatu, a wurin shi da danginshi da nata duk daya ne. Gidanshi ya kasance ‘open house’ ga kowa nata da nashi. Kai tsaye bazaka ce Mama bata da kirki ba sai ka zauna da ita, halinta ya bambanta dana mijinta Baba Bello sosai. Shi Arch. Bello kowa ya shaideshi da hakuri, kuma mutum ne mai sanyin hali da yawan kyauta, ma’abocin tawali’u, mai faram-faram da rashin nuna bambanci cikin mu’amalar shi da kowa da ya rabeshi. Amma wani nakasun Mama Fatu shine, mace ce mai nuna bambanci tsakanin mai shi da mara shi cikin mu’amalarta, mai nuna iko da mulki ga wadanda ke karkashinta da dangin mijinta. Gata da izza, fadin rai da saurin daukar zafi (saurin fushi akan ‘ya’ya) bata kara ko kadan a kansu, tamkar ba bafullatana ba. Har dai in aka zo batun lamarin Baffanta, nan zaka ga rashin fulako gun Mama. Mama bata kawaici a kansa sam, duk yadda kake da Mama kada ka sake kace ga laifin Baffa, gara ita ka bata mata daka batawa Baffa, in har kana son zama lafiya da ita. Kusan haka take behaving akan auta Hatoon ma. Kada ka sake ka taba auta in kana son Mama ta cigaba da bude maka hakoranta. Wannan yasa Hatoon ta tashi