← Book details Heart 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 31

Sashe 3

Heart 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

su biyu ba…… Domin a cewarsa shi da ita ai ‘sharing ideas’ sukayi, suka samar da (tangible final draft) na taswirar Zanen ginin, a matsayinta na (certified architect) itama. Ta kasance mai yawan tallafa masa ta kowacce fuska akan al’amuran profession dinsa na Zane (mataimakiya ta cikin gida). Duk wani jibi (gumi) na wahalar samar da ‘Sunset Estate’ da gudanar da ayyukanshi kafin samuwarshi, a koyaushe ya kan ce ma ‘yan jarida. “Shi da itane suka hadu suka yarfeshi”. Wannan na daga cikin dalilan da suka sa lokacin da aka fara bada hayar gidajen Sunset, yayi mata kyautar ‘Terrace’ guda da sunanta a cikin Estate din bayan wanda suke ciki. Tsarin ginin Sunset Estate da zamanatuwarsa, farin jininsa da ficen da Estate din yayi a birnin tarayyah, yayi matukar jan hankalin ‘yan jarida na cikin gida dana waje, tare da manema labarai akan ilmin fasaha, musamman masu son fito da zallar fasahar ‘yan kasar da tallata baiwarsu ga idon duniya, don duniya ta san da irin fasaharsu, wannan dalilin yasa suna yawan bibiyarshi, a gida ne ko ofis, da tambayoyi na gani kasheni, akan son sanin tarihin rayuwarshi, da sirrin nasarar Estate din. Ana yawaita tambayarsa; “Shin ko a ina ya samo tunani da samfur din zanen Sunset Estate? Wai da gaske ne shi da matarsa suka zana Sunset Estate?” A irin wadannan tambayoyin zaka ji shi yana fadin amsarsa a takaice ga ‘yan jarida cewa. “Yes! I got the samples from ‘Her!’ I mean (My Co-architect)”. Idan kuma aka yi masa tambaya game da sirrin nasarar “Sunset Estate” dana farin jinin da ya samu yake kuma kan samu ko me zai ce? Sabida a halin yanzu duk wani mai babban mukami a gwamnatin kasa, ko ‘yan kasuwa masu kumbar susa, ko ‘yan siyasa mazauna FCT, kokari yake ya mallaki gidan zama ko na haya a cikin Sunset Estate. Baya gajiya da fadar cewa…... “She is behind all these successes, My co-architect!”. Sannan akwai wani suna na musamman da duniya ta shaida ya kan kirata dashi a duk lokacin da yaso soyayya; “My Alter Ego!”. Hakika wannan sunan, ba dadi kadai yake yi mata a zuciya da ruhi ba, yana sawa ta ji kanta ya kumbura, taji ta tamkar tafi sauran mata tana yawo akan gajimare, ta kuma tambayi kanta ko a cikin mata ‘yan uwanta, akwai wadda ta kaita sa’ar samun soyayyar miji? Domin hakika tayi sa’ar dasu basu yi ba, na samun mijin da ke sonta da dukkan zuciyarsa… har ya maida ita barin rayuwarsa, dadin sunan da take ji in ya ambaceta dashi yana wanke duk wani dattinsa daya zo ya yabawa kansa a ruhinta, wato bayan canzawar kaddarorinsu daga positive zuwa negative. Kalmar na tattaro duk wani nau’I na farin ciki ta saka a ranta, zuciyarta kan zama fara kal, kamar danyar madara, idan ta tuno da sanda ya sha kiranta “His alter ego” a lokuta mabanbanta na tarayyarsu da bazasu lissafu ba. Don haka ita da take ce masa “Habibyyy” ta san ai is not enough! Ta san dai bata biyashi kalmar soyayyah ba, bata ko kamanta ba, bata kuma da wata kalmar mai tsada da zata iya bashi bayan wannan. Amma ai yafi kowa sanin cewa shi ruhinta ne gabadaya. Ya zama cewa, a duk sanda ta tuna sunan nan da yakan kirata dashi (a lokutansu na soyayyah) sai ya zama babu sauran burbushin bakin cikinsa a cikin zuciyarta (a lokacin da soyayyah ta canza). A duk lokacin da ya kirata “alter ego” dinsa….. hakan ce take kasancewa da ita!!! Ko zata manta komai, saboda bacin rai, da canzawar zamani, da kuma canzawar zuciya, su wadannan kalaman nasa bata manta su. Ko na rana guda bata taba manta irin tasirin da nau’ikan kalaman soyayyarsa suke haifarwa gangar jikinta ba, a duk sanda ya dubeta cikin ido dinnan ya ambaceta da muryar nan tasa mai dakushe mata kunne da kashe kuzarinta. Sannan ta sanyaya ruhinta all at the same time. Wato idan yaso soyayyah haka kawai ya kan kashe ido ya dage gira yace. “You know you are my alter ego koh?!”. Yana daga cikin daidaikun tsofaffin memories dinsu da basa fading! A gareta. Kuma basa canzawa ko bayan canzawar kaddararsu, har kuwa bayan ficewarta kacokam daga gidansa da rayuwarsa……. ***** **** *****
Chapter 3 · 0% Book details