← Book details Heart 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 31

Sashe 22

Heart 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da bazai saurareta ba, kansa kawai zai taimaka, kansa kadai zai tallafawa a ranar”. To kenan ga ranar tazo. Ya zamanto cewa rokonta da magiyarta na ya tausaya mata, ya biyar da ita a sannu ma ba ya bari zuwa wani lokaci ba basu yi tasiri ba sam a tare da Habiby, daga yadda gangar jikinsa yaso tafiyar da ita, domin basu taimaka ba ko kankani wajen samar mata rangwame ko yaya yake daga Habibin nata. And that was how their first night happened, a very passionate night, they had a wonderful love making, ever! Wanda daga ranar yayi binding dinsu together suka zama cikakkun Zayyan da Safiyyah da a yau yake bada labari. Tarihin aurensu ya fara ne daga wannan muhimmiyar ranar da ya karbi budurcinta cikin girma da daraja. Domin a ranar ne ya goge duk wanan ‘fear’ dinta akan aure, ya cire hijabin nan na kunyar Safiyyah da take sawa tana lullube tsakaninsu. Safiyyah sai taga komai ba’a yadda take zato da hasashe ba. Kuma ba’a yadda Aunty Dije ta suffantashi gwanin ban tsoro da saka fargaba a zuciyar amarya ba. Bata sani ba Zayyan ya biyar da itane (in a very gentle manner) har ya samu ya gamsar da kansa, duk da irin kidimewa da rikicewar da ya samu kansa a lokacin na kasancewarsa virgin shima. Yet yana gayawa kansa yabi a sannu (no matter how) ta wahalar dashi, kada yayi hurting dinta is her first night. He wouldn’t take it as a revenge! A haka har ya samu ya karbi abinda yake kulafucin karba, wanda duk wani mijin kwarai ke burin karba daga matar kwarai irin Safiyyarsa.... Macen kwarai data kai mutuncinta gidan miji kadai zata gane irin yanayin da suka kasance ciki a wannan muhimmiyar ranar shida Safiyyah. Don haka tafiya Rafindadin da ba’ayi kenan a ranar ba, a gidansu suka shiga Rafindadinsu, sai a sati na gaba. In fact, hakan ya janyo saida ya kara sati daya akan hutunsa, domin satin sai ya koma na jinyar amarya Safiyyah da cigaba da more romon soyayyah tsagwaronta, amarci yake diba son ransa, saida ya fanshe duka hakurinsa, koko muce satin ya zamar masa satin “Shahr Al-asal” (honeymoon) a larabce da kuma turance. A cikin kwana bakwannan gradually dai Zayyan ya maida Safiyyah cikakkiyar matarsa ta sunnah, wadda duk sanda ya zo da bukatarsa da safe ne koda dare koda yammaci, zai samu abinda yake so har da kari, ayi masa welcome wholeheartedly babu kailula. Matsalarsa daya da Safiyyah taki karbar irin sutturar da yake sha’awar ganinta a ciki kullum, kuma bata masa irin kwalliyar daren nan ko irin (dressing) din da yake son gani a jikinta sabida kunyarta da gidadancinta, ko muce saboda irin ‘orientation’ dinta da ‘background’ dinta wato hakan ya samo asali ne da irin ‘decent upbringing’ dinda ta samu. Zai wuni yana jinyar Sophie da tarairayarta, in dare yayi kuma ya karbe ladan jinyarsa in a loving and romantic manner. Zuwa lokacin Safiyyah ta ware, ta karbi rayuwar aure ta reality. Ta daina tsoron shi, tana cooperating dashi dari bisa dari, tana kuma enjoying soyayyar kamar kowacce mace, ta rungumi rayuwar auren yadda ya kamata duk wata macen kwarai ta yi, a shekarun girman diya mace. Burinta kullum kasancewa tareda Habiby da farantawa Habiby rai, fatanta na yanzu shine samun ‘ya’ya masu irin halayensa da kamanninsa daga gareshi. A duk sanda ya bukaceta yanzu a take amsar gayyatarsa. Don ta gane wuyar sha’anin ashe-ashe bata kisa, shu’umancin Aunty Dije ne. Tafiyarsu zuwa Katsina sai a sati na gaba ta yiwu, ya zamanto cewa sati hudu cif kenan rabon Zayyan da gidansu, wato tun bayan tarewar Safiyyah. Saidai koyaushe basa rabo da waya shi da Baba da Mama da ‘yan uwansa mata. Abinda bai sani ba ashe hakan da yayi wato kwashe sati hudu cur bai zo gida ba yayima Mama Fatu ciwo sosai, ya kuma fusatata, don sanin kowa ne Mama ta kallafa rai akan Zayyan, bata maraba da duk abinda zai canza mata shi ko ya canza tsarin rayuwarshi ta baya wajen kulawa dasu, kasancewarsa da namiji kwal data ke so fiyeda sauran yaranta, ta dai tsaya taga iya gudun ruwansu shi da matar tasa, na sai yaushe zai zo inda take saboda yayi aure. Mama ta kasa yin uzuri akan hakan. Har rannan take cema Yaya Zubaidah cikin damuwa, ranar Zubaidah tazo mata yini kamar yadda ta saba zuwa gida ta wuni duk sati. “Zubaidah ko kin fahimci Baffana mace ta janye min shi tun ba’a je ko’ina ba?”. Zubaidah tayi dariya kadan, tace “kai habawa Mama! Har yaushe aka yi daren da garin zai waye? Ki barshi na dan lokaci ne, giyar amarci ke kwasarshi in kwannafi ya kwanta kanwa ta kar tsami zaki ganshi ne da kafafunsa. Amarya kota buzuzu ce sai an yi dokinta Mama”. Mama ta ce “umh” kawai. Don bata so zancen yayi nisa ya kara janyo mata bacin zuciya. Wannan itace haduwar farko tsakanin Sophie da surukuwarta Mama Fatu, haduwa ta zahiri. Saboda a hoto kawai Mama ta taba ganin Safiyyah sai ko yau data ganta a gabanta kuma a dakinta. Nan Safiyyah taga inda Zayyan ya debo ruwan kyawunsa na Rumawa. Bai baro Mama a komai ba. Hatoon na makarantar kwana haka su Zahra suna jami'a. Cikin sa’a daga Mama har Baba suka samu a gidan, dattijan suna shan hutun karshen mako yadda suka saba. Baba Bello da ‘yar lelensa Hajiya Fatimah (Mama shalelen Baba) inji ‘ya’yanta. Kasancewar Asabar ce Baba yana gida bai fita ba. Zayyan ne a gaba, Safiyyah na biye dashi a baya, yayi sallama suka shiga kasaitaccen falon Mama. Mama dake hakimce cikin kujerar falonta ta sha ado da (swiss lace) dan gaske, ruwan zuma, kwalliyar ta musamman ce yau ta karshen mako kasancewar Baba na gida yau yace ba inda zashi, kai in ka ganta a lokacin tamkar Hakimar Rafindadi, tana jiran Baba ya gama wayar da yake yi tayi masa korafin Zayyan, har yau bai zo ba tun tarewar amaryarsa. Yanzu ita dashi sai dai waya, yana faman bata uzuri na zai zo, zai zo, sai kuma katsahan taji sallamarsa. Mama ta amsa sallamarsa ciki-ciki don ta dau muryarsa tun daga waje, yana shigowa tace cikin nuna mamaki. “Muryar wa nake ji mai kama data Baffana? Halan ka yi batan kai ne yau Baffa?" Watakila saboda haushin Zayyan yayi sati hudu bai zo ba shiyasa Mama ta kasa yiwa Safiyyah kallon kirki. Duk wani dan canji yanzu ta cewa kanta sai tana kula, don kada diyar Alaramma ta janye mata shi da laqaninsu da tofinsu na ‘ya’yan Alarammomi. Shi daya jal din da Allah ya bata a matsayin namiji cikin ‘ya’yanta mata kenan bata wasa da al’amarinsa, bazata barwa wata mace kuma ‘yar talakawa da ta zo daga sama tayi yadda taga dama da rayuwarshi ba. Idon Mama ya koma kan amarya Safiyyah. Duk inda Zayyan ya cire kafa nan take mayas da tata a falon, cikin yanayi na nuna bakunta da surukuta. To da yake Mama bata zaci zuwanta a lokacin ba, yasata binta da kallo tana shigowa, da takunta na nutsuwa kanta a kasa. Ta lura wani kallon kurilla Maman Zayyan take mata. Mama ta tsaida idonta a kanta tana kallon ‘Hijabhie’ din Zayyan dinta, wato Safiyyah Usman Dandume. Tun daga kallo na farko ta hango macen kwarai, amma son zuciya daya lullubeta da kyashin kasancewata diyar talakawa yasa taji kawai daga gani na farko Safiyyah bata yi mata ba. kamar yadda tun farkon fara zancen aurenta ma zancen bai mata ba. Abun mamaki Mama ta kasa boye haka a kan fuskarta, don sai yamutsa fuska take yi kamar taga abun kyama. Kwarjinin Safiyyah irinna cikar tarbiyyah da riko da addini yaso ya dan rikita Mama, wadda a baya take mata kallon raini tun kafin ta ganta, just because an ce diyar Alaramma ce, sai ba haka ta tsammaci ganinta ba, wato dai ya zama cewa Safiyyah din ganinta yafi jinta! Ta so ganinta typical bakauyiyar Dandume, yadda zata ji dadin raina mata wayau. Amma ina! Wane mutum! Safiyyah dai girman kauye ce amma bata da Ruwan kauyawa, sannan ta wuce ido ya kalla ya raina domin Safiyyah ta sha rubutun kwarjini a gidansu ta koshi. Ashe ba duka mazauna kauye keda appearace na kauyawa ba inji Mama. Sai tafi mata kama da kalar matan manya ba yara ‘yan makaranta irin danta Zayyan ba; she is looking extremely classy, a cikin hijabin. Yawanci mata masu tsayi da kyawun surar fuska dana kirar jiki irinna Safiyyah basu cika yawa a arewa ba, duk da za’a iya cewa Safiyyah bata da zubin kalar 'yammatan da Mama ta saba gani tareda ‘ya’yanta, wato Safiyyah ba ‘yar gayu da son kwalisa bace, kwatankwacin ‘ya’yanta su Zaitoon da ire-iren kawayensu da ta sani, ma'abota kawar zamani irinna ‘ya’yan hutu, wadanda iyayensu wasu ne a Katsina, sun kuma daure musu gindin yin shiga mai tsada ta kece raini, ire-iren ‘yammatan da ta so ace Zayyan ya aura kenan, amma kuma ita Safiyyah nutsuwarta da kamewa, da innocent looks dinta da zubin halittarta na Alkyabbar mata yasa duk ta fisu kwarjini da kamala. Ko makiyinta in ya ganta a lokacin, da irin shigar mutunci da tayi tazo gaban surukanta zai ce “Safiyyah is decent and classy”. Duk da fatarta ba mai haske bace can, yatsun hannunta duk sun sha adon jan lalle na amarci har na kafarta, wanda bai gama fita ba har lokacin. Domin kumshi ne mai nagarta aka yi mata na aure. Kyakkyawar round face (zagayayyar fuskarta) kawai kake iya gani a jikinta da zara-zaran yatsun hannunta, bata shafawa fuskarta komai ba bayan ‘lip gloss’ data dan shafa kadan a fatar bakinta mai sulbi kamar yankan reza, zaka gane ita Safiyyah mai yalwar sumar kai ce (mai yawan gashin kai) ta hanyar tudun dankwalinta ta baya, nata tudun kallabin natural ne ba irin wanda ake kira a cuci samari bane. Koko yace rashin haduwar jini na farat daya shi ya kara afkuwa physically a haduwar Sophie da Mama, tsakanin Mama da surukarta Safiyyah. Don sam Mama har ranta bata yi farin ciki da zuwan Safiyyah gabanta ba, ta so ace shikadai ma ya zo, su sake su wuni hira abinsu. Safiyyah tsugunne a gaban Mama Fatu, tana gaisheta da dan
Chapter 22 · 0% Book details