Sashe 9
Hauwa Kulu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
faman masa kamar an bude famfo. Da murna Sumayyah ta je daki ta dauko abayarta ta rufa masa baya suka dauki hanyar Badala. A hanya Sumayyah ta yi wa Bhaiyanta congratulations, da felicitations ya fi a kirga, amma a aurensa da Madina ai bai manta tsiyatakun da ta yi masa ba, alhalin Madina ba ta yi mata laifin komai ba. Sumayyah kenan. Nan ya saka wa ransa sai ya tashi tsaye a kan mu'amalar matansa biyu da kannensa biyu, don ba ya son bangaranci irin wanda tun ba a je ko'ina ba Sumayyah ta soma nunawa. Surayyah ma ta soma irin nata na taya kawarta Madina kishi don ya lura ta daina kula shi. Abin mamaki ga idonta ga nasa sai tayi kamar bata gannshi ba. Ya kuma fahimci hakan ne zai kasance ta bangaren Sumayyah ma in bai yi da gaske ba. Wato itama ta taya Hauwa kishi da Madina. Mamakinsa daya ne, yaushe har Sumayyah ta yi wa Hauwa farin sanin da ta ke sonta har haka? Duka-duka ya san sau daya ya taba hada su suka gaisa a gidan su Hauwan. Sumayyah ta tuno wani abu sai ta hau hadiye dariya. Da gefen ido Sarham ya kalle ta yana ci gaba da tukinsa cikin wata irin nutsuwa da bai taba ji a tare dashi ba. Yau ji yake ya fi kowa nutsuwa, ya fi kowa kwanciyar hankali da ya auri Hauwa-Kulu, da ba zai ce don soyayyarta ya samu wannan kwanciyar hankalin ba sai don Hauwa ta zame masa wani 'mission' mai muhimmancin da dole ya cika shi a rayuwa in yana son kwanciyar hankalinsa ya dore dari bisa dari. Sumayyah ta ce, "Bhaiya!" Sai ya juyo kadan suka hada Ido taga ya kara mata kyau da kwarjini, har da kyallin angonci akan goshinsa da suka hada ido sai ta hango wani boyayyen ‘contentment’ a kwance kan kyakkyawar fuskarsa, ai kuwa Sumayyah ta fashe da dariya ta ce, "Yanzu Bhaiya, duk inda ka ga kare yana sunsunar takalmi ka yarda dauka zai yi ko?" Shikam ya gaji da shegantakar Sumayyah Harararta ya yi, ya ci gaba da tukinsa, amma da da ne tabbas da ta sha Mari yatsu goma. Sumayyah bata daddara ba ta sake cewa, "Wato Bhaiya, soyayyarka da Hauwa na lura wata irin special soyayya ce boyayya a zukata, wadda Allah kadai ya san ta yadda ya tsara ta. tunda Hauwa dai bata taba ganinka ba. Amma ni dama, ko ka yarda ko kada ka yarda, na dade da sanin a haka za ta kare. Bhaiya Allah ya bada zaman lafiya da zuri’a mai albarka I am so happy Bhaiya na, nafi kowa murna da faruwar al’amarinnan nikam!". Sarham ya yi mamaki da ya samu bakinsa da amsa addu’ar Sumayyah da "Ameen" duk da ya san shi ba wata special soyayya tsakaninsa da Hauwa, sannan ba dole aka yi masa ya aure ta ba. A wurinsa aurensa da Hauwa kaddara ne, kuma DALILI MAI GIRMA ne ya yi sanadinsa. Sai shigo da huhun goro da alewa ake yi ana ajiyewa a falon Inna, bayan ‘yan daurin auren sun watse kenan da waliyyan Sarham da suka zo daga Shanono. Malam Isah shi Baban Hauwa ya bai wa waliccin auren Hauwa-Kulu. Hauwa ta fito wanka a daidai lokacin ta gefen sallarta a dakinta, ta zuba hijabin sallarta ta tada sallar walha kenan ta jiyo muryar Malam Isah na gayawa Inna daurin aure ya kammala, HAUWA-KULU ta zamo matar SARHAMU, Allah ya kade fitina ya bada zaman lafiya. Kawai sai ta tada kabbarar sallarta cikin gigicewa da tare sautin kuka da tafin hannunta. Cikin sujjadarta ta farko taji muryar Sarham ya yi sallama a tsakar gidansu, sai ta ji gabanta ya tsinko daga kirjinta ya fadi kasa ras! Ras!! Ras!!! Har sau uku. Daga nan sai muryar data shaida ta kanwarsa Sumayyah ce ita ma ta karade gidan da sallama, da alama tare suke. Ta ci gaba da sallahrta amma ta kasa karanta komai daidai har ta idar, lokacin Inna ta rako Sumayya dakin nata, ta ce, “Hauwa, kin idar ne? Sumayya ce suka zo tare da likita". Sumayyah ta shigo ta zauna a kusa da ita, ta mika mata hannu ta rike nata wato (shake hands), sannan Inna ta ce, in sun gama gaisawa Sumayyah ta zo dakinta su yi magana. Sarham na falo a lokacin da Inna ta ce ya shiga dakin Hauwa su gaisa, Hauwa ta idar da sallah. Cikin jin nauyi Sarham ya ce, “Inna ashe tun jiya baki yi mata bayani ba? Wannan zuwan ba nawa ba ne ai na Sumayyah ne, ni ai Yayanta ne ba zance nazo ba, na kawo Sumy ne ta gaishe ku ne". Inna ta yi dariya ta ce, "na san da haka mana, nafi kowa sanin kai Yayanta ne. Amma wanda aure ya dan karawa Yayan matsayi yanzu ya daga darajarsa zuwa ta abokin rayuwa. Na kuma gode da zuwan Sumayya. Amma likita a yi haka? Yaushe rabon ku gaisa da mutuniyar taka idan ka zo? Daure ka je ka lallashe ta don Allah, don ni dai tun jiya da uban ya zaunar da ita ya gaya mata gobe daurin aurenta da kai ta daina kula ni, ta kuma kwana tana kuka. Hauwa ta ina za ta gane cewa ba yinmu ba ne mu duka, wannan auren yin Allah ne, alkawarinsa ne tun fil azal ba na kowannenmu ba? Na fi kowa son kada a yi mata aure ka sani". Idanun Inna suka ciko da kwallah, ta yi shiru don har ta fara jin kewar Hauwa a cikin jikinta, tun ma kafin a yi batun kai ta gidan miji. Sarham ya sunkuyar da kai kasa yana jin wani iri a ransa da ganin hawayen Inna. Ya san irin shakuwar da ke tsakaninta da Hauwa. He can feel for her, na irin kewar Hauwa da za ta yi, amma hakan ne kadai abin da zai yi ya zama maslaha akan rayuwar HAUWA-KULU da ta iyayenta, hakanne kuma kadai abinda zai dorar da dangantakar su, musamman da aka yi sa'a ya lura Sumayyah na son Hauwa, ya tabbatar za ta taya shi kula da ita, kai dai bar Sumayyah da ra'ayin ta na rikau akan abin da ranta yake so da wanda ba ya so. Ya ce, Insha Allah Inna ki sa a ranki ko kin koma Ghana Hauwa na hannunku ne, bana jin Mamana, bana kuma jinsu Sumayyah, za ta taya mu kula da Maijidda. Adduarki za ta bi Maijidda duk inda ta ke. Don Allah don Annabi ki cire damuwar wai Hauwa wulakanta za ta yi a hannun mijinta, wannan shi ne babban dalilina na auren Hauwa, don in tsare mata mutuncinta da martabarta in kuma kula da ita, rayuwar ta bakidaya da ilminta. Ba ni da haufi a kan kowa nawa. Babu Mai cutar da HAUWA cikinsu, Inna za mu rike Hauwa ne da amana da amincewar Ubangiji kamar tana gaban ku". Sumayyah ta shigo tana cewa, "Bhaiya, wannan lallashin fa sai kai, Hauwa ta ki yin shiru duk irin lallashin dana yi mata". Ta zauna a kusa da Inna. Inna ta ce, "Je ka ka ji Sarhamu, lallashe ta, mace tafi son lallashin mijinta sama da na kowa, ta ci albarkacina ba don halinta ba". 'Yar dariya Dr. Sarham ya yi, kamar Inna ta san tun ranar da ya ganta suna tadin soyayya ita da Jamilu yake jin haushinta, ya kuma fita sabgarta bakidaya, babu gaira babu dalili ya tsani ganin da yayi mata da Jamilu. Ko ta gaisheshi sai ya ga dama yake amsawa. Amma yau ji yake duk haushin nata da yake ji akan Jamilu ya kau. Sosai yake jin tausayinta don ya san rabuwa da Inna ga Hauwa ba wasa ba. Sallamar Sarham a dakinta ya sa ta wani irin saurin dagowa, kamar a firgice. Ta watsa masa manyan idanunta harrrr! Kamar tana ganinsa da suke jike jagab da hawaye. Dr. Sarham ya tsaya 'standstill' daga bakin kofa hannayensa duka biyu zube cikin aljihunshi, as ango as he is, ko makiyinsa ya san ya yi kyau har ya gaji kamar ranar farkon aurensa, ya koma kamar yaro matashi dan 27 kai ba za ka taba cewa ya ajiye hamshakiyar mace kamar Dr. Madinah Sorondinki a gida, har da albarkar 'ya ba. Hauwa tana iya jin idanun Sarham na bin jinin jikinta, don haka ta kasa jure kallon hararar da ta sa gululun idanunta yi masa, ta sunkuyar da su kasa. Ta kuma lumshe su duk a lokaci guda. Sarham ya tako cikin dakin ya zauna a kujera kwalli daya da ke dakin, karonsa na farko da shigowa dakin Hauwa, tun dawowarsu sabon gidan. Saidai ya dan leko daga kofar daki I zai wuce gida. Cikin rishin kuka Hauwa ta ga ya dace ta gaida Dr. Sarham, ko da kasancewar mugun haushinsa ta ke ji yanzu, nayi mata katsalandan cikin rayuwa, amma Dr. Sarham na da muhallin gaisuwa daga gare ta (no matter what), wato cikin kowanne yanayi. Hauwa ta sa habar hijabinta ta share fuskarta, ta kuma bar fuskar a cikin tafukanta da hijabin nata ta ce (kamar wadda aka yiwa dole sai ta gaishe shin), “Masa'ul Noor”. Sarham bai yi gaggawar amsawa ba, don ya raina ‘yar gaisuwar tata mai kama data rowa, ganin irin kukan da ta ke yi kuma, bayan furta gaisuwar ya san takura kanta tayi ta furta ta tamkar kuma ta kwace abarta ta mayar cikinta, ya yi kwafa cikin jin wani maqaqi a ransa na rashin son da ya lura Hauwa na yi masa, ya ce, "Shin wannan kukan na mene ne Maijidda? Tsakani da Allah auren da ni ne ba ki so ko? Na tabbata da wancan yaron dan polo ne yau Inna ta aura miki, da yanzu kin takarkare kina shafa hoda don tarar zuwansa matsayinsa na angonki. Amma da yake nine dube ki don Allah, a haka wai amarya ce mai shirin tafiya dakin miji, da wani zurmemen hijabi kamar mai zuwa fadar limamin jihar Kano". Hauwa ta tale baki ba ta ce komai ba, ya ce, "To ya ishe ni kukan nan haka Malama, ki tashi ki yi sallah raka'a biyu ki roka mana duk wasu alkhairai na duniya da lahira da zaman lafiya, har da jikoki masu yawa da albarka ga