← Book details Hauwa Kulu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 18

Sashe 3

Hauwa Kulu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zuwa, girkin da bait aba cin mai dadinsa ba, tun ban kai haka ba ina yi masa girki yana shi min albarka, idan baki manta ba. Sai da na shigo madafin yau na tuna ashe fa ba zan iya aikin wuta ba, kada in tsumbula hannnuna a mai ko garwashi, tunda ba ni da ido, komai ma bazan iya ba Inna na taimakon ki, na zama banida amfani?". Zuciyar Inna ta karye, wani irin karyewa, cike da 'maternal love' wanda ya motsa mata, ta ce, "Idan Allah ya nufa, da albarkacin tsarkin Al’qur’ani, da tsarkin mulkin Allah sai ganinki ya dawo kamar na kowa tun a duniya HAUWA-KULU, sai kin ga idon ‘ya’yan ki, sai kun hada ido a lokacin da kike shayar dasu, ina ji a jikina ba za ki dauwama cikin wannan halin na lalurar makanta har abada ba. ubangiji yayi alkawarin kowacce cuta tana da magani, amma waraka lokaci ce. Ina ji a jiki na takaitacciyar jarrabawar ki ce Hauwa mai zuwa ta wuce, da yardar Allah sai kinga fuskar 'ya'yanki a lokacin da kike shayar dasu. Kada ki kara cewa kin zama bakida amfani, duk mai nakasa indai ba zuciyarsa ce ta mutu ba kuma ya tsaya ga neman ilmi ga kowa ina tabbatar miki zai iya komai da mai lafiya ke yi. Allah da kansa ya ce, "Ad'uni Astajib lakum! Wato (Ku roke ni, Zan amsa muku)". Ta daga hannu biyu sama tana fadin "Ya Allah Ubangijin sammai da kassai, ina Mai tawassuli da sunayenka tsarkaka guda 99, a yau ni Safiya uwar Hauwa ina rokonka; Ka budewa HAUWA-KULU idanunta ko kadan ne tun a gidan duniya darajar kaunar da ta ke yi wa iyayenta”. Hauwa Kulu cikin tsananin hawaye da jin dadi ta ce, "Amin-Amin ya Allah Innata". "Yanzu gaya min me ki ke so ki dafa masa sai mu yi tare?” Inji Inna. Ta kara da cewa “duk uban aikin da kikeyi a Tashar kuka da kanoline kin manta, ai ke dinnan ba sakaltacciyar mai lalura bace". Hauwa ta ce cikin jin karsashi ya dawo mata, "Inna funkason fulawa da miyar taushe nake so in yi masa, ko kuwa alkubus da miyar ganye. Na tabbata ya jima bai ci su ba, in kuma ya ci din, to ba irin na gidannan ba". Inna ta yi murmushi tace, "an yi an gama Kuluwar Babanta. To mu yi duka biyun mana? Malam dan gatan Kulu ya ci kala biyun. Bari in tattaro miki kayan hadin sai ki kwaba alkubus din da funkason da hannunki, nikuma in dafa alkubus din, in kuma soya funkason". Hauwa ta yi murmushin jin dadi, Inna ta gama ganeta fiyeda kowa a duniya, bataso nakasar nan tata ko kadan ta maida ita useless (mara amfani), suka soma aikinsu tare suna yi suna hira kamar kawaye. A haka Malam ya tadda su a kitchen din wajejen karfe takwas na safe. "Hauwa da Innarta girki ake yi mana haka?" Hauwa na kwabin funkaso ta yi dariya ta ce, "Ni nake maka girki na musamman Baba, na sannu da zuwa na tabbata zaka ji dadinsa". Ya ce,"Allah yayi miki albarka. To ku gama in ba ki tsarabobinki daga Ubangidana, har da na'ura mai kwakwalwa sabuwa dal a kwalinta ya aiko miki". Hauwa ta ce. "Ai kuwa an koya mana amfani da ita kadan a makaranta, lokacin da muna aji biyar, an gaya mana zamu iya amfani da ita muma ta duk hanyar da mutane ke amfani da ta a matsayin 'assistive technology' ga masu lalurar idanu". Can kuma ta dubeshi ta ce, "Baba baka gaya mana ina ka je ba, da abin da ya faru cikin batan naka, rana daya muka rasaka, haka rana daya katsahan muka ganka cikin koshin lafiya ka dawo. Ba tareda tsumi da dabarar mu ba. Ni dai na san addu’ata ce Allah bai wofintar da ita ba, don bana yin sallah na tashi daga inda nayi ta ban roki Allah ya bayyana min kai ba, ni nasan addua ta bata fadi ba, lokacin amsarta ne Allah ya jinkirta min". Malam Bilyaminu ya ce, “Tabbas Hauwa’u, addu’a ba ta taba faduwa kasa banza, don nima na san tasirinta da alfanunta ne yau ya dawo da ni cikin iyalina lafiya da nisan kwana….". “Assalamu alaikum. Inna me kike dafawa ne haka duk lokon nan ya dauki kamshi?” Sai jin sallamar Dr. Sarham da korafinsa suka yi a gidan da safiyar Allah, wand aba lokacin zuwansa bane yafi zuwa da daddare, misalin karfe tara na safe yau yayiwa gidan tsinke. Kallo daya za ka yi wa Dr. Sarham ka san ya fito daga gida ne ba tare da shiri ba, don Malam Isah ne ya kira shi da sassafe ya tabbatar masa Baban Hauwa ya dawo, har sun gaisa dashi yau a masallaci wajen sallar asubahi. Dr. sarham ya zo gidan ba shiri ba don ya yard aba sai don tabbatar da labarin Malam Isah. Duk da dai ya san da kyar in zai fadi abinda bai gani ba. Ilai kuwa da Baban Hauwa ya soma tozali tsaye a kofar kicin, suna hira shi da iyalinsa. Sarham ya lumshe ido yana murmushi lokacin da ya karaso yayi musabiha da Malam Bilyaminu, yana kallon fuskokin wadannan family da suka cika da annashuwa yau. "What a family!" Sarham ya gaya wa zuciyar sa cikin jin dadin walwalar da suke ciki. Inna ta amsa masa fuska fal annuri. Malam ya yi masa barka da zuwa tare da cewa su karasa falo, suna shiga yana cewa, "ko ba a yi min gabatarwa ba, jikina da zuciyata sun gama bani likita Sarhamu ne wannan". Sarham yayi kasa da kai cikin girmamawa, ya ji wani irin farin cikin ganinsu haka complete family kamar nasa iyalin, bakinsa da murmushinsa ‘from ear to ear’, wato daga jiyan zuwa yau kadai har Malam Bilyaminu ya san da zamansa, wanda ke nufin yana da matsayi mai girma a wajen Inna, (don ba zai ce a wajen Hauwa ba), ya san bazata iya bawa Babanta labarin sa ba don ba damuwa tayi da shi ba sai ko Inna. Amma tabbas ya san ta bashi labarin saurayinta dan polo. Inna ta saka mishi funkason da alkubus din a nashi farantin ta zuba miya a karamin kwanon Samira ta aje masa gabansa, bai yi fulako ba don kuwa bai karya kumallo ba ya fito, kai ko wanka bai iya tsayawa yayi ba saboda wannan albishir din da Malam Isa yayi masa, Inna da Hauwa suka kammala aikin su suka dawo falon suka karya kumallon tare. Sai da suka kammala tsaf, kowa ya wanke hannu ya sha ruwa, suka sa Malam Bilyaminu agaba kamar sa hadiye shi, har Sarham din ya kagu yaji inda ya shiga, malam Bilyaminu ya fara basu labarin abin da ya fidda shi ranar daga gida, da rayuwarsa ta tsayin shekaru bakwai da yayi a ‘Kumasi’ ta kasar GHANA. "Asali muna da gona ta gado ni da dan uwana Zakari, wadda takardunta suke hannunsa, kullum na yi niyyar karbar hakkina sai in ji kamar an mantar da ni. Rannan dai da karfin addu’a Allah ya ba ni sa'a na taka same shi har wajen sana'arsa ta wankin hula, da zancen ya kamata mu sayar da gonar nan tamu haka, mu ja jari mai tsoka, mu kama manyan shaguna ya fiye masa sana'ar wankin hula. Ni ma in samu in zama babban dealer na gwanjo, in dinga zuwa sarowa da kaina, maimakon da da sai dai in sara hannun ubangidana. Wato ya zama cewa na samu jarin da zan dinga fita kasashen ketare kawo gwanjo da kaina. Zakari ya gama saurare na tas, sai cewa ya yi, shi babu wata gona a hannunsa, bai kuma san da zancenta ba”. Na ce, to idan ya hana ni, wannan karon zan kauda ‘yan uwantaka, zan sa hukuma ta kwatar min hakkina, zuwa shari’a a kan gado ba yau muka fara ni da shi ba. sai dai wannan karon kotu zani ba gun mai unguwa ba. Amma ko sati biyu ba muyi da yin wannan takaddamar ba rannan ba kya gidaina shirin fita kasuwa sai ga Zakari ya zo har zaurena ya same ni, tunda na yi tozali da shi gabana ya fadi, mummunar faduwa, mukayi tozali da juna sai kaina ya soma sarawa, duniya ta soma juyamin, sai ya miko min hannu ya ce, in ba shi takardun gidana da na saya a hannunsa, wallahi kamar sihiri, babu musu babu jayayya ko bakinsa bai gama rufewa ba na shiga gida na fiddo su na kawo masa. Sai da ya karba ya saka a aljihunsa, sannan ya ce min cikin daga sauti na bada umarni. "Tashi ka shiga duniya, kada ka tsaya cikin kasar nan, ka tafi ko can tsakiyar kasashen Africa ta yamma ka rayu a can, ko bangon duniya kai duk inda mai ya kare maka". Malam Bilyaminu yace, "Iya abin da zan iya tunawa kenan, sai ganina na yi a mota mai zuwa kasar Ghana, kuma da yake ba ka raba dan kasuwa da kudi a jikinsa, sai ban rasa kudin biyan kudin mota ba. Musamman da yake a jiyan ranar, na bude dealer din gwanjo na sayar. Saukata a Kumasi ke da wuya kuma wallahi cikin hankalina nake komai, muna tunanin inda za mu raba mu dan huta zuwa wayewar gari mu san inda zamu nufa na ji daga bayana an kira sunana cikin matukar mamaki. Ina juyawa na ga Alhaji Munkaila, wato Ubangidana wanda a wurinsa nake sarar gwanjo a Kano, cike da mamaki yace me ya kawo ni kasar su? Anya lafiya kalau nake? Wa na sani a Ghana me na zo yi kuma? Na samu bakina kai tsaye da cewa, "Neman na kai na fito!". Alhaji Munkaila ya ce, “amma a sanina, daidai gwargwado Bilyaminu ai sana'arka na garawa a Kano, na ga in ka kwance dealer ba ka kwana uku ta kare ka zo neman sabuwa ba. Na ce masa ra’ayina ne barin Kano in dawo Ghana don in yi sana'ata a nan, ya fimin kwanciyar hankali. Alhaji Munkaila ya ce, Ina da wajen sauka ne? Na ce "ni fa Alhaji na dai zo Ghana ne. Amma ban san kowa a cikinta ba, ban kuma san meyasa na zabeta ba”. Alhaji Munkaila yace min tun a lokacin, ya
Chapter 3 · 0% Book details