Sashe 13
Hauwa Kulu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kan ledar cin abincin. Ita kuma ta zauna gefen Sarham. Sannan ta zauna tayi serving kowannensu, Surayyah cewa ta yi cikinta na ciwo, don haka za ta je ta sha magani ta kwanta, ba ta jin yunwa. Kwarai kyawun Hauwa ne da kamalarta har ma da kwarjininta ya razanata, duk da kasancewar ta 'yar talakawa din bata zaci ko kusa ilhamarta ya kai haka ba, hakika Surayya ta razana da ganin Hauwa don haka ta ki zaman dakin Mama ta kuma kasa cin abincin taredasu, duk da yunwar take ji ta yi karyar ciwon cikin, gulma na cinta kamar me. Tana so kwarai ta kira Madinah a wannan lokacin ta labarta mata yadda taga Hauwa da yadda Mama ke rawar jiki da ita sannan ta gargadeta kan ta sake lale, tayi babbar dammara in har tana son korar HAUWA sai ta yi da gaske ba kamar yadda ta bata labara kafin ta ganta ra’aayal aini ba, sai ta mike akan Sarham da Mama, kada wankin hula ya kaita dare, domin gabadaya yadda suka zaci abubuwan da Hauwar kanta a kalar 'yan tallen cikin gari ba haka take ba, a nitsenta take, ta tuna gargadin da Madinah ta yi mata na cewa, kada ta kara yi mata zancen Sarham, ko na matar da Sarham ya aura. In ba so take ta samu (heart attack) ba. Da kyar Mama da Sumayyah suka lallaba Hauwa ta ci abincin da suka shirya dominta, amma kadan ta iya ta ci, sannan Mama ta kai ta dakin Sumayyah har bisa gadon da yaji shimfidar sabon zanin gado da sabon quilt, inda a can suka shirya mata sauka. Ta barta tare da Sumayyah, ita kuma ta hada mata ruwa mai zafi a toilet ta ce ta shiga ta yi wanka ta ji dadin yin barci, ta kamata ta kai ta har bandakin ta nuna mata duk abin da za ta yi amfani da shi har saida ta gane kan komai na bandakin, sannan ta fito. Sau biyu Sarham yana lekawa dakin don yayiwa Hauwa sallama zai je ya kwanta, Sumayyah na cewa ba ta fito daga wanka ba. Ita kuma Hauwa sulbi da taushin kumfar da kuma kamshin 'bath gel' na 'Fà' da kamshin turaren wankan da Sumayyah ta zuba mata a cikin ruwan wankan su suka sa ta kasa daina wankan, yi take tana sakewa jikinta na santsi don ba ta taba jin kamshi mai dadi irin su ba. da sabulun da ke dirje fata ta fita sumul kamar wannan ba. Su turarensu ita da Inna daga Dan Duala ne sai Binta Sudan. Sabulunsu kuma dan yanka ne wanda har wanki da shi suke yi, shi ya sa ta dauki lokaci tana saba jikin tana karawa, tana jin kamar bata taba yin wanka a duniya ba sai yau. Ta kwashi wajen mintuna sittin kafin ta gamsu cewa fatar jikinta ta fita sumul, ta lalubi tawul faffada wanda Sumayyah ta aje mata ta ce shi za ta daura a jikinta in ta gama wankan, ta kuma rufa karaminsa a kanta ta tsane kai dashi ta fito. Sumayyah na jin motsin fitowarta ta mike ta kamo hannunta zuwa stool ta taya ta goge ruwan jikinta da karamin tawul din. Gashi daman Maman Salele ta rangada mata sabon kitso kanana da ake kira (weeving) a gashinta baki mai cika, na asalin Hausawa-Kanawa. Sumayyah na taba jelunan kitson da sha'awa tana ce da Hauwa. "Hauwa Jidda kina da kai mai cika, haka kuma mai karfi, wanda baya breaking, amma kamar ba ki taba saka masa 'relaxer' ba". Hauwa ta ce, "Umh, can baya ina yarinta na taba karambanin saka masa danjangabu da sunan zanyi shamfo gaba daya gashin ya sauka kasa, tun daga lokacin ban kara gwadawa ba, don kaina tal kwabo ya koma Aunty Sumayyah". Sumayyah ta dinga dariya, wait tal kwabo, ta ce, "Danjangwabo ai 'traditional relaxer' ne, wa ya aike ki? Insha Allahu da mun sauka a Jiddah zan kai ki saloon din dana ke zuwa a yi miki na amarci wanda zai burge Bhaiyana". Hauwa ta rufe ido tana jin kunya. Sumayyah tace "ah toh! Don in gaya miki gaskiya Bhaiya Dan kwalisa ne na gani kasheni, kuma yana so ‘yar kwalisar matar shi". Sumayyah ta dauke mata damuwa da hirarrakinta masu ban dariya, duk na Sarham da irin gayunsa, nan da nan ta rage mata kewar Inna. Sabuwar rigar barci fara kal, tsayinta iya kauri Sumayyah ta dauko ta bata ta saka, ta bata lotion mai kyau na neutrogena tana shafawa tana mata hira. Sosai Hauwa ta sake da Sumayyah, ta jita (at home) don Summy ta maida kanta sa’ar Hauwa, duk da cewa ta girme ta da shekaru uku kwarara. Mama da Abba na babban falo, Abba Prof. na cin abinci, Sarham na gefensa suna hira shi ya sa ya kasa tsallake su ya je don ya ga yaya Hauwa ta ke coping a gidansu, ya san dai zuwa yanzu ta fito daga wankan. Sumayyah kuma bazata barta ta nemi komai ta rasa ba. Sarham duk da kasancewarsa dan bokon zamani hakan bai cire masa dattaku da halin kawaici akan mata irin na manya ba. Bokonsa bai cire masa wasu daga halayen kawaici irin na mazan da a gaban iyayensu ba, duk kuwa da kasancewar iyayen nasa yan zamani ne kuma 'yan boko suma. Banbancin tashin yaro a kasar musulunci irin Saudiyya da kasashen turawa kenan Abba ke tambayarsa ko yaushe 'annual leave' din nasa zai kare? Kuma yaya ya tsara zaman iyalin nasa? Kafin Sarham ya shirya amsar bashi kuma yace. In zaka bi shawarata, to Hauwa ka barta tare damu a nan, ta fara karatun degree a nan BUK tunda tana da WSSCE certificate, Jamb kawai zata zana a samar mata gurbi a duk tsangayar da take so”. Abba Prof. ya kara da cewa, “bana so ta je Jeddah mata biyu su hada maka zafi, a matsayinka na likita mai bukatar nutsuwa wajen gudanar da ayyukan sa, Hauwa na bukatar (special care) in kun tafi kullum kana asibiti, matarka na jego, wa zai kula da ita? Tunda Sumayyah a makaranta ta ke zaune ba'a gidanku ba, don haka in har shawarata kake nema, to Hauwa'u ta zauna tare da mu a gidannan, Mamanku ta kula da ita, ni kuma in sa ta cikin jami'a zuwa gaba kadan mu ga me Allah zai tsara muku. For the mean time". Sarham kansa na duke a kasa ya kasa dagowa balle Abba ya ga irin yanayinsa, da irin karbar da yayiwa shawarar sa. A da kam ya so ne ya tafi da Hauwa. Amma shawarar Abba Prof. ma abar dubawa ce, bai auri Hauwa don yayi rayuwa ta soyayya da ita ba, ko don biyan bukatar ransa, ko don ya yi auratayya da ita nan kusa, har gobe kallon kanwa yake yi wa Maijidda kanwar ma ta jini abar kulawa a gareshi, cikin dalilan da suka sa ya aureta harda dalilin zamowarsa sanadin nakasar idonta, da har gobe ya kasa yafewa kansa da kuma sauran dalilai masu tarin yawa, da bazau lissafu ba, ciki har da kaunar sa ta hakika ga Inna, da kuma alkawarin da yayiwa kansa na gina rayuwarta positively da tallafar ilminta koda idonta bai gyaru har abada ba. Da kyakkyawan burinsa na ganin cewa ta zama wani abun amfani ga alumma, kuma abin alfahari ga iyayenta da duniyar masu nakasa. He wants to become HER PACESETTER in life! In haka ne kenan shawarar Abbansa tana kan hanya, kuma ita ta fi dacewa da Hauwa. Bai auri Hauwa don sha'awa ko soyayyarbukatar gangar jiki ba irin wadda za’a kasa controlling ba, ya auri Hauwa ne don ya tallafi rayuwarta ya zame mata, ya ginata ta kowanne bangare ya kuma nema mata lafiya. Da wannan tunanin Dr. Sarham ya amince da shawarar Abbansa na zai tafi Jiddah ya bar Hauwa tare dasu, ya dago a hankali ya ce, "Abba na amince da shawararka. Hauwa ta zauna karkashin kulawar ku, na tabbata sai tafi samu kulawa har fiye da a hannunmu". Abba ya ce, “To masha Allah lelan Abba, haka nake so ka dinga fahimtata a komai, yanzu sai a samar mata karamar yarinya daga Shanono cikin yaran family dinmu, wadda za ta zama mai aikinta ita kadai ta kuma dinga raka ta cikin makaranta kullum, ko’ina ya zama suna tare, ko ni in zan fita in fita da su in kai su department dinsu. In yaso sai su dinga dawowa da kansu in ta gama lectures su dawo gida tare da mai aikin nata. Zan yi wa Babanku na Shanono magana ya bamu aron 'yar sa Mardiya tunda ba su kai ga yi mata aure ba. Yarinyar nan Mardiyya na lura tana da hankali sosai ga nutsuwa. Har suka gama hira shi da Abba Sarham bai tsallake su ya je dakin Sumayyah gun Hauwa ba. Har sai da Abba ya tashi ya shiga turakar barcinsa, bayan ya gaya masa sati mai zuwa zai koma Jeddah, hutun nasa next week zai kare, kuma zai sayo mata (JAMB form) ya cike mata komai kafin ya koma in sha Allahu, don a lokacin Mama ta ke gaya musu an fara sayar da jamb form na wannan shekarar. Bayan wucewar Abba bedroom dinsa ya rage daga shi sai Mama suka ci gaba da hira. Mama ta ce, "Yanzu da gaske iyayen nata jibi za su koma Ghana? Su kuwa me yayi zafi hana da bazasuyi hakuri su zauna a mahaifar su ba?" Ya ce, "Eh Mama, ni ma abun yana tayar min da hankali sosai don wallahi na saba da Innar Hauwa yadda ba kya zato. Saidai ko ke kika ji cikakken labarin Malam Bilyaminu da dan uwansa Zakari, zaki bi bayan hukuncinsa na yin nisa dashi shine mafi alkhairi gareshi da iyalinsa, ga dukkan alamu arzikin sa yana can". Ya ba ta labarin irin yadda Inna ke sonshi da kula da cikinsa da abincinta mai dadi da tsafta, da yadda ta ke yawan yi musu addu'a su iyayensa ba dare ba rana. Da halin da Zakari ya janyo musu na shan wahala da sayar da abinci a tasha, sakamakon rushe gidansu da yayi, ya ce, “Mama, in na tuna hakan sai in ga hukuncin da Malam Bilyaminu ya yanke na barin Kano ya fi masa alkhairi