Sashe 17
Hauwa Kulu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a ranki, ba wai furta kalmar so ne kadai yake sakawa a yi aure ba, sannan aure ba ya taba samun muhalli a inda babu so. Ko na ce, ko ban ce ba Maijiddah, ba zan aure ki alhalin ba ki da muhalli ko yaya a zuciyata ba. Da wannan nake cewa. Maijiddah ki yi hakuri ki bani lokaci, ki taya ni mu taru ni dake mu raini wannan burbushin SOn, wanda dalilai da hujjoji suka fi shi karfi, daga ni har ke ba mu san me gobe za ta haifar ba, Allah daya halicce mu shi kadai ya san sirrin da ya boye a tsakaninmu. Ina fatan ki taya ni rainon wannan burbushin son, har zuwa sanda zai girma ya zama mashahuri, abin buga misali beyond our expectations”. Sarham ya yi shiru yana nazarinta hawaye sun ki tsayawa a idanunta, amma ta kare fuskarta da tafukanta. Ta sani cikin abubuwan da yake fada duka babu karya, gaskiyar zuciyarsa yake gaya mata, “suyi nurturing dan burbushin son tare har ya girma ya zama mashahuri”. Wanda ita kuma gaskiyar ce ta ke mata daci, ta cewa ita an aure ta ne ba don so ba, sai don wasu dalilai masu karfi. Sarham ya fada ya maimaita a kunnenta, ya fada har a bayan idon ta, wanda shi a wurinsa ba komai ba ne face gaskiyar da ke zuciyarsa kasancewarsa frank person, kuma a wurinsa ya girma da yin karya, wai don ya farantawa mace. Bai sani ba, ita wannan gaskiyar bakanta shi ta ke yi a zuciyarta, har gara ya barwa ransa ita, koda kuwa bai yi mata irin zancen da ta ke son ji din ba kamar na Jamilu mai nuna tsantsar tsagwaron soyayyah muraran. Duk yadda Dr. Sarham ya so su yi kyakkyawar sallama abu ya faskara, shi kuma yana jin nauyi da pride din ya rungumo ta cikin jikinsa ya lallashe ta irin lallashin da yake yiwa Madina in ya bata mata rai, Madinah ai sa’arsa ce, ta kuma mallaki hankalinta, sannan soyayyar ce zallah ta hada su. A wautarsa Hauwa-Kulu ba ta san da irin wannan duniyar ba, ba kuma zai koyar da ita ba balle har a zo gejin da wani abu makamancin nasa da Madinah zai samu mabubbuga tsakaninsa da Hauwa. Hauwa za ta ci gaba da cin matsayinta na tudu biyu, na kanwarsa kuma matarsa. Yayin da Madina ke kan tudun muntsira na masoyiyar romansiyya. Matsayin da ya bata na kanwa kuwa ai ya fi na masoyiyar soyayya, tunda matsayin kanwar jini ya ba ta, kuma dai Hausawa suka ce jini ya fi ruwa kauri, wato soyayyar jini da yake yi wa Hauwa-Kulu kaurin ta yafi na romantic soyayya tasiri, irin wadda ke tsakaninsa da Madinah. Sallamar dai ta ki dadi tsakanin Sarham da Hauwa, ta ki kula shi, ta ki daina kuka. Ta ki yafe furucinsa. Har cewa tayi cikin subutar baki. "Ita da ma ya barta tare da su Inna sun tafi Ghana, ya fi mata alkhairi a kan wanan kaddararren auren nasa, (wadannan kalaman da ya gama gaya mata yanzu sun mata da banzan ciwo), na cewa da yayi ta taya shi su yi nurturing ‘yar burbushin soyayyar da yake yi mata, su girmar da ita tare, har su samu ta zama mashahuriya, wanda in anbi salsala kalamansa na nufin ba ta da muhallin soyayya a zuciyarsa. Wannan ya kara tunzura kuka da rikicin Hauwa. Abinda bata sani ba harda na kewar tafiyarsa. Abin da ba ya son yi wato rungumar Hauwa ya lallasheta shi ya yi a bisa dole, jikinsa yana ’yar kyarma ya hade jikinsa da nata wuri guda suka dunkule cikin ‘tight hug’. Hauwa tana sakin kuka a hankali bata daina ba, wani abu tamkar 'electrical shocking' ya bakunci jiki da zuciyar Hauwa, dana Sarham as well, ta yi kokarin janye jikinta daga cikin nasa, amma yaki saki, ya tallafo fuskarta da hannu daya, kallon hawayen da ke bilbila daga kyawawan idanunta suna sauka akan kundukukinta sumul sumul dashi kawai Sarham ke yi, kafin ya kai dan yatsansa manuni yana kawar dasu one by one daga kan kuncinta, sai kuma yasa fuskarsa a cikin tafukan Hauwa, wato ya tallafi fuskar shi da hannuwanta biyu ya sanya fuskarsa a tsakiyar tafukanta, murya na dan rawa kamar yadda ilahirin jikinsa ke shaking and vibrating da ya hadu dana Hauwa, Sarham ya ce. “Zan tafi Hauwa-Jiddah, sai nazo, ban san yaushe zan samu dawowa ba. Anyway ki kula da kanki, ki kula da ibada kin ji?” Kai kawai ta gyada masa don dai ta samu freedom daga rikon kazar kukun da yayi mata, zai sumbaci tafukanta da ke kan sajensa, idanunsa a lumshe, Hauwa kamar ta san hakan zata faru ta yi maza ta janye hannayenta daga sajen fuskarsa, tsigar jikinta na tashi amma a wannan lokacin ji take bata bukatar irin wannan rarrashin yaje can yayiwa matar so. Duk yadda Sarham yake so sallamar tayi dadi da armashi tsakaninsa da Hauwa, ta yadda bazai tafi tana ajje dashi da kalamansa a ranta ba, hakan bata samu ba, Hauwa ta dauki fushi mai ban mamaki wanda shi a iya saninsa bai da dalili. Meye laifi don ya gaya mata hakikanin gaskiyar da ke zuciyarsa cewa ba soyayya ce ta sa ya aure ta ba? Dalili ne, kuma har gobe zai kara maimaitawa dalili ne mai kwari da karfi ya yi mujazar auren nasu. Ta tayashi su raini wannan dalilin har ya koma ingantaccen SO, Shima zai so hakan. Ko don ya zamo mai adalci tsakanin ta da Madinah. Ya gama gane Hauwa so ta ke ya zauna yana mata karerayin samari ‘yan I love you? Ya karkace kai yana ce mata ‘I can’t do without you, bayan Madinah ce kawai ‘he can't do without’. A ganinsa ya wuce wannan ‘stage’ din tun a can baya, kuma ba zai iya maimaita shi da kowacce mace a yanzu ba, bayan Madinah. Ya tsura ma Hauwa ido daga tsaye, hannayensa biyu zube cikin aljihunsa, ya kasa fita daga dakin, kalma kuma ta kare masa don ta ki tsaida hawayen idanunta, kukan da bai ga dalilin yin sa ba, don ba za ta ce don kewarsa ta ke yin shi ba. Don yana da tabbacin Hauwa bata wani saka shi a ranta ba. Lokaci na ta tafiya, Hauwa na sheshsheka, wadda ke saka Sarham tsuma daga tsaye, kukan nata na huda shi sosai, ya kasa fita daga dakin har sai da Sumayyah ta dawo, ba ta san cewa har lokacin yana dakin ba. Ta yi niyyar komawa da baya ganin yanayin da suke ciki, ya ce murya na sarkewa “Summy, kina iya shigowa, wucewa zan yi in kwanta, kin san gobe asubanci za mu yi. Ina fatan kin sayo ma Maijidda duk abin da za ta bukata din wanda zai yi mata akalla watanni uku?” Sumayyah ta idasa shigowa dakin cikin sanyin jiki na yanayi mara dadin data gansu aciki, ta ce, “Ba abin da ban sayo mata ba, duk da cewa akwai komai a cikin akwatin lefenta, irin su pad, macleans da listerine na karo mata da sauran tarkacen da babu cikin akwatunan". Sarham ya soma taku daya, biyu zai bar dakin har zuwa lokacin hannayensa biyu cikin aljihunsa ya ce, “Maijidda sai mun yi waya, take care”. Da wani irin karfin hali ya bar dakin ba tareda ya jira jin amsarta ba. Hauwa ta ce, “Allah ya tsare, Allah ya sauke ku lafiya”. Wani irin tausayi mai tsanani ya kama Sumayyah ganin cewa, ai Sarham ba irin sallamar da ya dace a ce ya yi da Hauwa ba kenan, za ta iya rantsewa in Madina zai tafi ya bari a wata kasa ba irin sallamar da za ta samu kenan ba. A halittarsa ‘he's very romantic’ ga matar aurensa. Me yasa yake ja baya da Hauwa? Ta hade rai sosai cikin taya Hauwa kishi, ta yi kwafa ta bi shi da harara yana ficewa. Sumayyah ta zauna a gefen Hauwa wadda ke gyara filo don ta kwanta, ta ce, “Aunty Hauwa saboda Allah haka ake sallama da miji ana cin magani ana faman sharar hawaye da sharbe majina? Da me zai tuna ki ya yi dokin sake zuwa gare ki? Hauwa sai fa kin sake lale, in ba haka ba wallahi za su kai ki su baro a ‘yar jiran dakinsu. Ki tashi ki kwato wa kanki ‘YANCIN SO, dana lura anaso a take miki da gangan, don ni ban ga soyayya a wannan auren naku ba, ya fi kama da zallar ‘yan uwantaka. Ni ko yadda na ga ana magana da Madinah ana kashe murya da Ido ba haka na ga ana magana da ke ba. Ke ni fa bana karbar ‘defeat’ na a so wata mace ‘yar uwata fiye da yadda za a so ni, don ban yarda ta fi ni da komai ba, dukkanmu mata ne a halitta, sai dai a ce kowacce da kalar tata fatar. Amma da irin kissar ta, na rantse mai mata irin Madinah, sai kin yi da gaske kafin ki samu gurbin da ya dace da ke a hannunsa, don wallahi Madina ta gama shan gaban Bhaiya daga sama har kasa, har kudu da arewa”. Hauwa ta ce, “Aunty Sumayyah kenan, ta ya ya zan zo in same shi da matarsa in ce lallai sai na hada kafada da ita a zuciyarsa? Nasan irin gwagwarmayar da sukayi tare kafin su kai ga wannan matakin? Kamar zan fi yarda da nasa ‘perception’ din fiyeda naki, da yace in taya shi mu raini nawa son har in samu ya girma a zuciyar sa. Soyayyah ta Allah ce, ba’a mata dole, shi yake sanya ta a zuciyar da ya ga dama, ni ba wani ‘effort’ da zan yi don a so ni, ban da maida al’amurana ga Allah da yin abin da zai amfane ni duniya da lahira. Ban shigo rayuwarsu don in hada kafada da ita a komai ba kamar yadda ban taba tsarawa kaina aure da mai mata ba. na shigo ne ta hanyar kaddarata. To amma ya zanyi tunda Yayanki Allah ya rubuta min? Kuma shi iyayena suka zaba min? Na shigo gidansa ne da sunan shi ne mijin da Allah ya zabar min, kaddara kuma ta rubuta min, ba ruwana da irin mu’amalar da