← Book details Hauwa Kulu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 18

Sashe 4

Hauwa Kulu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fahimci ba cikin hayyacina nake ba shiyasa ma bai yarda ya barni na shiga gari neman masauki ba yaji tsoron kada in fada hannun bata gari. Sai ya ce, tunda na ce nema na fito, to in bishi ya bani masauki mu ci gaba da sana'armu a nan Kumasi yadda muka saba a Kano, don can din ma Ghana Gwanjo na garawa kuma ya bar Kano ya dawo gida. Ya gaya min yanzu ya dawo Ghana gaba daya saboda mahaifin sa ya kwanta dama, zai kula da mahaifiyarsa da kannensa, dama kasuwanci kadai ke kaishi Kano, amma shi dan nan Kumasi ne. To kun ji yadda aka yi na samu Ubangida cikon taimakon Ubangiji ba tareda na tagayyara bat un daga ranar dana sauka a Ghana, muka ci gaba da sana'armu ta shigo da gwanjo. Alhaji Munkaila na da karfi sosai a sana'ar mu ta Gwanjo don kai tsaye yake zuwa kasar Italy ya saro Gwanjo. Daga baya ma da ya koya mana ni da babban dansa Salisu yake turawa mu saro, shi kuma ya rarraba. Ba jimawa na iya manyan yaren Ghana tun daga yaren Akan, Ewe, Ga, har zuwa Dagbani da Turanci tsilli-tsilli na 'yan koyo a bakin Salisu da abokan cinikayyarmu. Lokaci-lokaci da yaga kamar na dawo hayyaci na na koma cikin nutsuwata Alhaji Munkaila na yawan cewa ya kamata in je gida in ga iyalina haka, ko ya ce in daukoku, Sai in ce masa ba yanzu ba, har ya gaji ya rabu da ni. Mun samu alkhairi mai yawa a wannan sana'a tamu ta shigo da Gwanjo, har wani lokacin da zamana haka ya dame shi ya yi min tayin auren kanwarsa Yahanasu wadda mijinta ya rasu ya barta. Ni kuma na gaya masa cewa, har abada ba zan iya aure a Ghana ba, don na san uwargidana ko mutuwa na yi ba za ta iya auren wani ba ni ba. Ya ce, to lallai in koma gida in zo da ku. A wannan karon na gaya masa hakikanin gaskiyar dake zuciyata cewa ko sunan garin Kano bana son ji! Alhaji Munkaila yace min shi da kansa ya fahimci al'amari na akwai saka hannu a ciki, da shekaru suka yi gaba banida niyyyar komawa gida shi da kansa yasa wani shaihun malaminsa ya dinga yi min addua a boye, ba tare da na sani bama. Idan ma wani makaru ne a jikina ya roke shi ya kwance in koma ga iyalina ko in dauko su inda nake, in Kano ce bana so kwata-kwata. Don a lokacin har gidan kaina da motar hawa na mallaka a kasar Ghana. Rana daya na samu duk dabaibayin da ke zuciyata yana yayewa. Na ji hankalina bakidaya ya dawo Kano. Na zama ba abin da nake so irin in bude ido in gan ni cikin iyalina. Ga mafarke-mafarke da nake tayi a kan Hauwa'u, wai ba ta da lafiya. Wani mummunan abu ya faru da ita. Rana daya ni da kaina na samu Alhaji Munkaila na gayamasa ina da mata da 'ya dana baro, ina so in je in taho da su Ghana, don ba zan iya kara zaman Kano ba, na fi jin dadin sabuwar rayuwa ta a Ghana, wani bare sau dubu ya fiye maka dan uwa na jini. Alhaji Munkaila kusan ya fi ni farin ciki da dawowar hayyaci na, don da kanshi ya saya min tikitin jirgin zuwa Kano daga Ghana. Ya kawo tsarabobin sittiru na gwanjo masu karshen tsada na turawa da na na'ura mai kwakwalwa ya ce a kawo wa Hauwa'u, kuma yana yi wa dansa Salisu dana baro yana karatu a Italy kamun auren ta, don ya san zuwa yanzu ta girma. Na iso Kano lafiya, na hawo drop din taxi daga filin jirgin saman Malam Aminu Kano na zo har kofar gidana. Na sha mamaki ganin sabon gida a muhallin gidana, sai da na tambayi mutane kusan uku ko a nan kofar gidan ko inda Innar Hauwa da 'yarta Hauwa suke zaune ne? Ana ta tabbatar min “eh a nan suke”, wani ya ce min amma ba su jima da dawowa ba, sannan na iya na shigo". **** **** **** Anan Malam Bilyaminu ya nisa, ya ce, "To kun ji wannan shi ne labarina. Da abunda ya faru dani bayan barina gida. Zakari shi ya yi min makarun da ya kore ni don ya cinye gonar gadonmu shi kadai. Na zo kuma na ji abin da ya yi wa gidana, don haka wannan karon nisa da Zakari shi ya fi min alheri, ba zan iya shari’ah da shi akan abun duniya ba amma bazan kara zama gari daya da shi ba, kuma ba zan yi shari'a da shi ba a matsayinsa na dan uwana na jini. Na bar wa Allah ya saka mini, domin hakika ba ya yafe hakkin wanda aka zalinta. Don haka ku yi shiri Hauwa da Innarta za mu tattara mu koma Ghana ne, ina nufin zamu bar BADALA nan da kwana uku, son son samu ma gobe insha Allahu. Amma don in baku dama kuyi sallama da abokan arziki irin likita, zamu tafi kwanaki uku masu zuwa in sha Allahu. Ya juya ga Sarham ya ce, "Likita Sarhamu, Da nagari, dan albarka na ji duk halaccinka a kan iyalina, ba ni da bakin gode maka ina rokon Ubangiji Ya fi ni godewa. Allah ya yi maka albarka duniya da lahira, ya tallafi haularka a bayan idonka kuma Ya jikan iyayenka, Ya kara yalwata musu kamar yadda ka zama yalwa kuma farin ciki ga iyalina. Ina so kafin mu koma Ghana ka raka ni gun mahaifinka in yi masa godiya, don ni ban taba jin mutum mai kyakkyawar zuciya karimi kamarka ba, wanda ba komai ba ne kyawun tarbiyyar da ka samu daga garesu ne na taimakon mara gata da wanda yake cikin yanayi na bukatar tallafi da lalura irin wannan…… Kafin kowa ya yi magana, aka ji Hauwa ta saka gunjin kuka har da sheshsheka, hankalinsu ya koma gareta, Inna ta san Hauwa bata kuka na banza haka kawai mara dalili sai mai dalili, shiyasa ta san tabbas kukan nan baka da zuci take yin sa, tana fadin, “ni ba zan koma Ghana ba, ba zan iya barin Kano ba, b azan ma iya barin ko gidannan ba, ni Baba bazan iya barin BADALAr da aka haifeni a ciki sabida zaluncin Baba Zakari ba”. Ta kare zancenta da cewa "ba inda zamu je, muna da gida na tarihi, ina son zaman cikin Badala, Baba da Inna ku barni in yi karatun da zan zama lawyer wallahi sai nayi muku maganinsa". "Yau nake ganin sakarcin wofi. Lauyo!" In ji Inna, "wato kin fi so mu ci gaba da zaman Kanon dai yana binmu da kulli yana illata mu, ko saboda soyayyar da kike da dansa Jamilu ko? Ya ci gaba da yi miki naci yana zuwa azure yana kalallame ki da shirme, ke kuma kina biye masa, tun farko ma ai ni so na yi mu bar Kanon gaba daya tun ranar da ya rusa mana gida. Saboda Zakari abun gudu ne, kika dage kika hana ni sabida son Badalar ki, da kafiya da naci kamar kuturwa, ni na san a Kano cibiyarki ta ke, mu duka ruhinmu ana yake, amma Manzo (S.A.W) ma da kansa lokacin da Makkah mahaifarsa ta yi masa kunci saboda kiyayyar abokan gaba da kafirai yayi hijira ya koma Madinah inda ya samu sababbin masoya, suka karbeshi karbar da ahalinsa basu yi masa ba, sannan ne ya zauna lafiya. Ki duba tarihin Hijirar manzon Alah SAW zuwa Madinah. Banda wauta irin taki wai har bayan jin abin da Zakari ya aikata wa mahaifinki kina marmarin ci gaba da zaman Kanon inda yake zaune taki kadan zuwa dan agundi, yo ni ai ko don in raba ki da dan Zakari haihata-haihata na tafi Ghana, kurwata kur da iyalin Zakari da shi kansa. Zakari abin neman tsari ne. Malam Bilyaminu kam ya sha mamakin Jamilu a kan Hauwa, wai yana son auren Hauwa, koda yake tuntuni ya san halin Jamilu na kirki duk cikin ‘ya’yan Zakari shine kadai in ya hadu da shi a hanya yake gaida shi, sai ya rage mamakinsa ya ce, "ki mata a hankali, lallashinta za kiyi, sabo ne, amma Ghana dole mu tafi ba makawa muddin muka kai kwana uku a raye, komai na rayuwata ya koma can, sannan ba zan kara rayuwa a inda Zakari yake ba, na barshi da Allah, na bar shi da fitowar rana da faduwarta. Amma tafiyarmu zuwa Kumassi (Ghana) ita ce mafi alkhairi a garemu, ko yaya ka gani Likita Sarhamu?" Dr. Sarham wanda tunda ya dukar da kai yana sauraron su bai ce komai ba, amma bai taba jin tashin hankali irin wanda yake ji a zuciyarsa yanzu ba, musamman da Hauwa take wani irin kuka kamar na fitar rai tana fadin bazata bar BADALA zuwa GHANA ba, tace gara abarta ita kadai ta zauna zata iya rayuwa a gidan su ko babu dan jagora. Malam Bilyaminu wanda shi ma kukan Hauwa ya rikita shi, kalamanta kuma sun hautsina shi, amma bukatarta na ya cigaba da zaman Kano ba mai yuwuwa bace, ya ce, "Haba Hauwa-Kulun-Majadun, ‘ya daya tamkar da dubu! Shin ke ba kya fatan yin aure ne kamar kowacce mace, sai fatan dauwama a cikin Badala ko a gaban Innarta? Ai ke yar gidan wasu ce Hauwa'u, don haka barinki Kano zuwa Ghana ba komai bane, don idan ban da lalurar nan da na same ki a ciki, tuni na bada auren ki ga Salisu dan wajen Alhaji Munkaila, to a yanzu na san ba lallai ya yarda da zabin mahaifinsa ba, in ya kasance sun ji kin daina gani, ba kowa zai yarda ya auri marar ido ba sai mai soyayyar gaskiya, don haka na bar wa Allah ya zaba miki abin da ya fi zama alkhairi ga rayuwar ki, amma hakika nafi so kiyi aure". Inna ta yi sauri tace, "Mafi alkhairi ya fi a ce yaro mai nakasar ido yana tare da uwa da ubansa a gefensa? Suna zama garkuwarsa da karfinsa a lokacin duk da yake bukatar su a tare? Ka taimaki kanka Mallam, ka kuma bai wa kanka zaman lafiya ta hanyar cire wa ranka batun son
Chapter 4 · 0% Book details