Sashe 12
Hauwa Kulu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
**** **** **** A nan layin shiga gidan Malam Bilyaminu ango Sarham ya kashe motarsa, ya dan zauna a ciki kadan na wasu mintuna dafe da sitiyari yana karanto addu'a a zuciyar sa, addu'ar Allah ya sa aurensa da Hauwa shi ne alkhairin da kullum yake nema a wajen Ubangijin sa da neman zabinSa da yayi ta yi kafin ya furta amincewa da yin sa. Ya kuma bashi ikon yi mata adalci tsakanin ta da matarsa. Ya fito ya shiga gidan da kyakkyawar sallama a bakinsa da murya mai karsashi, Malam ne ya amsa daga dakinsa, ya kuma fito suka hade su duka a falon Inna. A lokacin Inna tana can dakin Hauwa tana tsaye a kanta tana fama da ita a kan shiryawa da sabuwar atamfar da ta dinka mata, dinkin doguwar riga akayi mata daidai jikinta. Hauwa ta kasa tsaida hawayenta haka ita ma Inna amma duk da haka bata fasa karfafa kanta tana lallashinta ba, lallashi irin wanda ba ta taba yi mata ba. Babbar damuwar Hauwa ita ce, jin cewa nan da kwanaki uku Babanta da Innarta za su koma kasar Ghana su barta a Kano hannun mijinta, wannan abu shi ya fi komai daga hankalin Hauwa fiyeda auren da ake ikirarin an yi mata da likita Sarham. Malam ya leko dakin Hauwa yana fadin, "Har yanzu ba a gama shiryawar ba ne? Ko bankwanan bai kare ba tsakanin Hauwa da Innar ta? Naga dai jiya baku rintsa ba kuna hirar bankwana. Har gashi angon ya iso, tun dazu yana jiranku". A lokacin Inna ta yi wa Hauwa lullubi da sabon mayafin da ya shiga da atamfarta ta fesa mata turaren Binta Sudan, ta kamo hannunta suka fito falon. Inna da kanta ta saka hannun Hauwa cikin na Sarham tana faman kokawa da hawayenta. Addu'a ta musamman Malam Bilyaminu ya karanto duk suka shafa, ya baiwa Sarham amanar Hauwa kamar yadda ya baiwa Abba Prof, Inna kuma da aka zo jin ta bakinta cewa ta yi ita ta san in dai Sarham ne ba sai ta jaddada masa amanar Hauwa ba, ita Hauwan ta ke baiwa amanar danta (SARHAM), don ta santa wani lokacin hutsuwa ce, musamman (in ka nemi raina mata wayo), tace ta yi masa biyayya fiye da wacce take yi musu don yanzu aljannarta ta tashi daga yardarsu su iyayenta ta koma kasan dugadugansa. Kan Sarham a kasa, hannun Hauwa cikin nasa, ya rike hannun sosai da riko mai karfi, suka fito daga falon Inna, Malam da Inna suka raka su har bakin motarshi ya budewa Hauwa ta shiga gidan gaba, ya maida kofar ya rufe, shima ya zaga ya shiga mazauninsa ya tada motar a hankali suka bar BADALAR KOFAR NA'ISA. Hauwa na jin 'feeling' na rabuwa da mahaifarta, inda ta rayu shekarun rayuwarta gabadaya, ba’a jikinta kadai take jin kewar BADALA ba, har a cikin zuciya da ruhinta take jin kewar. **** **** **** Suna tafe a hanya jin kukan na Hauwa ya ki karewa Kuma yana taba masa zuciya ba kadan ba. Dr. Sarham sai ya samu gefen titi ya tsaya ya kashe motar, ya kuma yi sama da glassan motar wadanda dama tinted glasses ne. Hauwa jin ya tsaya tsayin lokaci ya kashe mota kuma ko tari bai yi ba, bayan kashe motar da yayi, sai ta rage sautin kukan nata, har daga karshe ta yi shiru gaba daya tana ajiyar zuciya. Sarham yayi kyacci, ya ce, "Maijiddah kin san me? Wannan kukan da ki ke ta yi mun yau, da wanda aka ce kin kwana yi, yafi min kama da irin kukan nan na an miki auren dole. Ni na tabbata da Dan Polonki aka aura miki ya daukoki zai kaiki gidan Baba Zakari, ba za ki yi ta yin wannan banzan kukan ba. A'ah, inada yaqinin farinciki zakiyi tayi na kin auri wanda kikeso yake son ki, wanda har masoyanki sai sun taya ki wannan farin cikin. Sai gashi ni din da ba ki so kuma kike kullace dani sabida wani dalili naki na rashin Tawhidi ni Allah Ubangiji ya ga damar baiwa. Don haka ki ci gaba da kuka son ranki Maijidda, ina taya ki bakin cikin auren tsoho, mai mata, har da 'ya, ba yaro dan Polo sabon jini ba". Hauwa ta dauke numfashi, ta daina hadiyar zuciyan da take yi don tana iya karantar irin (bitterness) din da ke cikin muryarsa akan Jamilu da halin da ya shiga a sanadin kukan nata a sautin cool muryarsa. Me ya sa yake son yi mata wannan fassarar da wannan habaicin ne kullum a kan Yaya Jamilu? A ganinta koma dai yaya ne, zancen ta da Jamilu ne koma waye) ya wuce, tunda an riga an daura musu aure itada shi, ai zance ya zama past, tana so ko ba ta so, sunanta matar Sarham yanzu, bai kamata ya yi ta yi mata gori, yarfe da mita a kan Jamilu ba. "Ka yi hakuri". Kawai ta iya cewa cikin dusassar muryar data gaji da kuka. Ganin kamar ban hakurin nata bai gamsar ba, domin har zuwa lokacin bai ja motar sun cigaba da tafiya ba, ta cigaba da sauke ajiyar zuciya sannan ta dora da. "kayi hakuri don Allah. Na daina kukan Yaya Sarham, kuma ba don shi nake yin kuka ba, a'a, don kewar Malam da Inna ne. Kada ka manta fa kasar zasu bari gabadaya babu ni". Ta fada cikin rauni, da jin kamar cewa ta zama ita kadai kwal ta rage a fadin duniya tunda babu Inna jagorarta, wadda itace garkuwarta, karfinta, sannan kwarin gwiwarta a kan komai tun bayan da ta rasa idanunta. Sannan babu Baba a tare da ita yanzu, wanda shima ta kwashe shekaru ba tareda shi ba, bata mori komai na dawowarsa ba an yi mata aure, wannan tunanin ya sa wani sabon kukan ya dawo mata ta soma kokawa da shi ta hanyar toshe bakinta kada ta kara laifi wa Sarham. Sarham ya rasa inda zai sa ransa, sabida kuka irin wannan musamman na mace na kassara shi ba dan kadan ba, koda kuwa ace baida alaqar komai da ita, da hannunsa biyu ya bugi sitiyari sannan ya kifa kansa akan sityarin, yana sauraron yadda Hauwa ke rera kukanta wanda ya zarta na rabuwa da iyaye yanzu kuma, ya koma na tunanin yadda rayuwa zata kasance mata a gidan surukai da kishiya in general, alhalin bata da idon ganin su, kuka take tukuru, mai fita tun daga kasan ruhinta. A baya ya saka a ransa Hauwa ba abun tausayi ba ce, Hauwa za ta iya yi wa kanta jagora a duk inda ta samu kanta saboda karfin halinta da ki-fadinta, ya san ita ko lalube irin na makafi da son a taimaka a kamata a yi mata jagora ba ta cika yi ba, saboda zuciyarta dakakkiya ce, tsayayya kwarai, ya san Hauwa na da taurin zuciya mai sawa ta ji cewa za ta iya komai da mai lafiyar ido zai iya, amma wannan kukan da ta ke yi a yau, da iyayenta suka damka ta hannun sa bisa igiyar aure ya karyata duk wata jarumtakar ta, da duk abinda ta yarda da shi akan karan kanta. Ta koma ganin bazata iya komai ba yanzu tunda babu Inna. A yau ta yarda duk wani mai nakasa yanada rauni, da dole wani lokacin sai ya bukaci kusanci da tallafin wani nasa. Ya yarda Hauwa abun tausayi ce yanzu, tana bukatar tausayinsa, kaunarsa da adalcinsa, da kauna daga iyayen sa da dukkan ahalinsa da sadaukarwar su suma, hakan ne kadai zai karfafeta daga karayar data yi a halin yanzu. Ya lura ta gama karaya da nakasarta yanzun, ta gama sarewa da rashin Inna a tare da ita. Ta gama sarewa da cewa ada tana da confidence. (tabbas aure yakin mata). Dr. Sarham ya ja motarsa a hankali, suka ci gaba da tafiya sannu sannu, yana mai kokawa da zuciyarsa da ke cewa, dole ya koyawa kansa soyayyar HAUWA. Tunda aure ya riga ya gitta kuma babu jin qai a cikinsa idan babu soyayya ko yaya take, zai kuma tsaya wa rayuwarta daga yau kamar, koma fiye da da yadda Inna ta ke kula da ita, zai kula da ita ya tsare mata mutunci da martabarta wadanda sune makasudin dalilan da suka sa ya aure ta. Abun da zai mayar da hankali akai yanzu shine koyawa zuciyarsa soyayyar wata macen bayan Madinah a inda hakan ya zama dole. A kofar flat din gidan su Sumayyah suka tarar tsaye tana jiran isowarsu. Daga isowarsu bakin Sumayyah ya gaza rufuwa, ta karasa ta bude barin Hauwa, sannan ta kama hannunta ta fito daga motar fuskarta rufe ruf cikin mayafinta. Har dakin Mama Sumayyah ta isa da Hauwa, Mama Mai Shari'a ta daga ido a hankali tana kallon Hauwa-Kulun, Kuluwa, AKA Maijidda (ta bakinsa), HAUWA'U kuma Hauwa-Jidda tana shigowa dakinta, da tafiyarta cikin nutsuwa da tsentseni, duk da ta rufe fuska da mayafi za ka gane akwai nutsuwa mai yawa a tattare da ita. Har gefen gadon Mama Sumayyah ta kai ta, Mama ta yi murmushi ta ce, "Barka da zuwa cikinmu Hauwa'u, cikin iyalin Abbas Shanono, nan gidanku ne, don haka bude fuskarki ki daina kukan haka. Ajiye mayafin ki sha iska kin ji? Mu duka nan yan uwanki ne da iyayenki daga yau. Ga abincin barka da zuwa kannenki sun shirya miki, sauko bisa ledar cin abinci mu ci abinci tare har Sarham din kin ji? We are family, insha Allahu ba za ki yi nadamar shigowa cikinmu ba". Hauwa sosai ta ji dadin maganganun Maman Sarham, taji duk rabin damuwarta ta yaye nan take, a lokacin Sarham din ma ya shigo dakin ya zauna a kujerar da ke fuskantar gadon Maman, Sumayyah ta sauke mata lullubin sai Mama ta samu damar ganin kyakkyawar fuskar Hauwa sosai. Da manyan fararen idanunta masu kama da an diga musu zaiba ma'abota kayatar da idanun duk mai kallonta. Mama ta yi tazbihi cikin ranta, ta kuma tabbatar bayan son taimako, shakuwa da son yin jihadi ga rayuwar HAUWA KULU, danta Sarham zai iya auren Hauwa (on the ground) na so da kauna, domin ta isa mace ga kowanne namijin da ba kyale-kyale yake so a macen aurensa ba. Sumayyah ta zaunar da Hauwa kusa da Mama a