← Book details Hauwa Kulu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 18

Sashe 15

Hauwa Kulu Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ka aure ni ne saboda kana jin tausayina, kana kuma son ka wanke dattinka da ke cikin raina, sannan don ka dorar da dangantakarka da Innata. Amma kayi mantuwa, ka manta cewa ka riga ka gina zuciyata a kan wani ilmi na kada nakasa tasa in dauki kaina abar tausayi, ko inferior, ko mara amfani a cikin al’umma, ko wadda matsayinta bai kai ga samun kaza ba saboda nakasarta. Ka hore ni ne akan in zama jajirtacciya, cikakkiyar mutum, kuma in nemi ilmin da isheni hada kafada da kowa, ka koya min tsayuwa da kafafuna, in haka ne aurenmu cikin gaggawa ka yi ne don wani abu daban, amma ba don SO ba. In haka ne ai da ka bar ni a gaban Inna ta, na ci gaba da bin koyarwarka as my Pacesetter, na ci gaba da rayuwa da iyayena a gefe na. Koda kuwa ban auri Yaya Jamilu ba zan iya cigaba da rayuwata daidai, saboda ba'a aure babu soyayya a iya sanina. Ashe shiyasa ko amincewata baka tsaya nema ba kafin ayi mana auren, Yaya Sarham ba ka taba tambayata ina so ko bana so ba, tunda ka san da ka furta Inna da Baba amincewa za su yi koda basa so. Hakan bai yi kama da fin karfi ba? Tunda ni dai ban ce inaso a aure ni don a taimakeni ko a ji tausayina ba?". Hauwa ta saka fuska cikin tafukanta tana kuka mai tsuma rai, tana fadin, "Yaya Jamilu ba don tausayi ya yi niyyar aurena ba, ba don ya taimakeni ko ya sani a makaranta ba, zai aure ni ne saboda So, da gittawar Kalmar so da kauna, da kuma niyyarsa ta gyara gurbataccen zumuncin iyayenmu, shi ne ka yi maza ka hana shi, ba don kai din so na ka ke yi ba. Already you have your life and your love, kana da macen da kake so daidai kai; wadda tayi daidai da rayuwar ka, meyasa nima baka barni na auri daidai ni ba? Na gina nawa gidan kamar yadda ka gina naka da so da kauna, a maimakon inda za'a dan raba ni da sunan tausayi da taimako?? Sabida bana gani? Ko saboda iyayena sun ce neman kai suke da ni? Ko kuwa saboda ni ban cancanci a so ni so na soyayya kamar sauran mata?" Ta kara tsananta kukanta harda jiniya kamar tayi masa tumami a kasa. Yau dai Hauwa na shayar da Dr. Sarham matsanancin mamaki, wonders shall never end! Wato abin mamaki baya karewa. Mamakin ma irin wanda bai taba sha a kanta ba. Rikicin sosai yau Hauwa ta tubure tana yi masa, akan don me ya aureta ya rabata da mai sonta na hakika, tana kuka tana sharbe tana da ya barta ta auri Jamilu ya fiye mata alkhairi. Haka ya tabbatar masa da cewa Hauwa ta San 'yancin ta, nan gaba kadan in ta kara shekaru da zurfin ilmi ba za ta taba yarda a danne mata hakki wai don tana makauniya ba. Ya nisa ya sake nisawa, a wahalce ya ce, "Meji... Maijiddah don Allah ki saurare ni, Maijidda nine fa, Ya Sarham dinky, kin san dai babu namijin da zai auri macen da ransa ba ya so ko kadan. Tukunna ma ki gaya min wane irin so ne wannan da ki ke ikirarin ni ba na yi miki? Sai kin gayamin kowanne iri ne kuma a ina kika san shi?" Ya tsattsare ta da ido kamar tana kallonsa, sosai taji idanun sa a jikinta kamar suna mata bulala, kuma wai sai ta ji duk kunya ta kamata, ta rufe ido ta ki budewa, har zai kama hannunta ya kai kirjinsa, don ta ji yadda kirjinsa ke bugawa akan rigimarta da rikicinta da ya daga masa hankali, da yadda kalamanta suka firgita shi, sai kuma ya fasa. Baya so ya zamo touchy a kanta. A ganinsa Hauwa ta yi kankanta ya zauna yana bayyanar da ‘inner feelings’ dinsa gareta bari dai ta kara hankali zuwa can gaba, watakila shi ma zuwa lokacin ya samu ya fahimci kansa da kansa, don shi kansa a halin yanzu bai san wane irin so ne zuciyarsa ke yi wa Hauwa ba, bai san alqiblarsa ba, ya san dai ba irin na Madina bane, ba kuma irin na Sumayyah kanwar da suka fito ciki daya ba kamar yadda yake kuskuren ikirari. Ganin ta rasa inda zata sa kanta don kunya don ya dage shima sai ta gaya masa wane irin so ne take nufi da baya yi matan. Shi bai san wane iri bane. Mikewa ya yi yana ce da ita, "tunda bazaki gayamin ba bari in tafi sabgogi na. Zan shiga AKTH Haj. Soyayya, na rantse sai kin gaya min da bakinki wane irin so ne wannan don ni ban san shi ba ko ba yau ba, akwai abin da ki ke so in zan dawo in taho miki da shi?" Hauwa ta kara kuluwa, tunda kuwa abin da ta ke son ji din daga bakinsa Sarham bai fade shi ba har zuwa lokacin. Sannan ya maida zancen rainin sense. Bai kuma musanta kalamanta na cewa ba don Inna ya aure ta ba, har ila yau, bai musa cewa don yana jin tausayinta ya aure ta ba, haka bai ce ba don kada Jamilu ya aure ta ne ya sa shi yin gaggawar aurenta ba, haka bai yi mata karyar da take son ji ba, wato ya karkace kai yace da ita yana mata so ne irin wanda Jamilu ke mata ko fiye, wato na zallar ‘I LOVE YOU’. Hakan ya sa Hauwa ta kara tsananta sautin kukanta. Don ta tsani a raina mata hankali. "Cry more!" In ji Sarham. Yana takawa zuwa kofa. Tunda ni din dai da ba ki so ni Allah ya bai wa ba Jamilun da ki ke so ba, wanda ya iya kalaman I love you da ni ban iya ba". Ya dawo ya russuna daidai fuskarta har tana iya jin sanyin numfashinsa a saman fuskarta kamar zai sumbaci hannayen da ta rufe fuskar da su, sai kuma ya fasa. “Kiss”. Abu ne mai nauyi da sai da Madinah kadai yake iya shi. A ganinsa Hauwa is too young a yanzu ya tsaya yana sumbatarta. Tunda kuma ta yi masa gorin Jamilu ya fi shi sonta, ya kara sanya shi shiga taitayinsa da ita, yasa a ransa ba zai barwa Hauwa kofar sanin zuciyarsa a kan kowaccen su ba ita da Madinah, wadda tun ba'a je ko ina ba ya gane Hauwa irin matannan ne masu son soyayya, da son miji ya zauna yana gaya musu yadda yake son su a ran sa, koda karya zai musu to yafi musu dadi akan ya ki furtawa, shi kuwa duk wata kalma ta ‘I love you’ da ire-irenta da dangoginta ai ya gama fadawa Madinah su a can baya, ‘in his twentieth’ ba yanzu da ya fara zama Uba ba. Har yanzu yana nan a kan bakansa na cewa, ba auren soyayya ko son sauke sha'awa yayi da Hauwa-Kulu ba, a'ah, auren dalili ne, kuma auren jihadi da kawo maslaha cikin rayuwarta data iyayenta. "Sai na dawo Maijidda, me zan kawo miki?" Hauwa tayi masa shiru, tana jan hanci, ya ce. "Ko kina son ‘ice cream?" A nan ne ta ce a dan fusace, "Ban san shi ba, kuma ban iya sha ba". Ya ce, "Zan sayo ki koya?". Da sauri tace. "Wallahi bana bukata". Murmushi ya yi, a ransa yace "oho dai, ba zan ce I love you din ba". Ya juya zai fita, sai ga Sumayyah na shigowa dakin. Ya ce, "Summy, na ce zan sayo muku ‘ice cream’, sarkin rigima ta ce ba kwa sha". Sumayyah ta yi dariya ta ajiye tray din da ke hannunta a gaban Hauwa, ta ce, "Bhaiya, ka fa yi babbar mantuwa, shin ka kawo kazar amarci ne kafin ice cream din? Ko ka fara zuwa zance ka kafa gwamnatin ka yadda ya kamata???
Chapter 15 · 0% Book details