← Book details Hauwa Kulu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 18

Sashe 10

Hauwa Kulu Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Inna da Malam". Ai Hauwa ba ta san sanda ta sake barkewa da sabon kuka ba. Ya dai tabbata ta zama matar likitan nata yau, ba mafarki ta ke yi ba, ba kuma dan uwanta Jamilu data ke so aka aura mata ba. Dr. Sarham ne. Hauwa ta yi kukanta mai isarta ta goge ido, Sarham da ya lura ta gaji da kukan sai ya mika mata farin hankicinsa cikin tafin hannunta yana fadin. “Ki yi kuka ba zan hana ki ba, don dole ne a wurin mai uwa irin Inna yayi kuka, in aka ce ga ranar rabuwarsu ta zo. Amma ki sa a ranki ba hannun makiyanta ta kai ki ba, ko inda ake son ta da tozarta da wulakanta kamar yadda ke ki ka fi so (hannun su Zakari). Na san duk wannan kukan don ba shi ne mijin ba, ni da ba ki so din ni Allah ya baiwa HAUWA, sai inga mai kwace mini, don haka ga hankici na baki, ki yi kukan da zai jika shi jagab, ki gama ki fara shirya goya 'ya'ya na, ki haifa mun su da yawa kamar dozen su zama kannen Waheedah takwarar ki, kin ji ko Maijidda?” Daga haka ya koma lallashinta, da kalamai masu taushi da alkawarin bai aureta don ya wulakantata ba, bai aureta don y araba ta da farin ciki ba, bai aureta don ya raba ta da iyayenta ba, lallashi dai irin na namiji mai wayo, ilmi, wayewa da dabarar a saurareshi, har ya samu Hauwa ta yi shiru da kukan. Ta ki karbar hancikin da yake bata, amma kuma ta gyada kai kan nafilar da ya umarce ta da yi, sannan ya yi mata sallama kan zai koma gida a shirya mata dakin da za ta zauna kafin a gama yi mata visar tafiya tare da shi da Sumayyah zuwa Jeddah. Da ya kai bakin kofa sai ya juyo yace "ki cigaba da kwalliya, da shafa hodar dana taba gani kinayi a asibiti, tayi min kyau ranar, ina son gayu fa ni Maijidda dan gayu ne, matata ma ‘yar gayu ce sai kin shirya da zama 'yar gaye". Yayi murmushi cikin kallonta, ta saki baki da kunne tana jin sa, sannan ya fita da murmushin a fuskarsa. A ranta tace ba hodar da zan shafa, inna gumbuda tayi yawa ba lallai a gayamin ba. Karshenta ma sai dai yayi min dariya shi da Inna. Allah yasa matar tasa balarabiyace karewa kenan. Ji take da dai Jamilu ne da kuwa tayi duk abinda yake so ba hoda kadai ba. Tayi maza tayi istigfari akan wannan tunanin don ta san yanzu akwai igiyar aure a kanta. ***** ****** ******
Chapter 10 · 0% Book details