← Book details Hauwa Kulu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 18

Sashe 1

Hauwa Kulu Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

 ‘YAR CIKIN BADALA
(HAUWA-KULU)
3

PAID BOOK
SUMAYYAH ABDULKADIR

(whtsp only)

SADAUKARWA
SADAUKARWA NE GA DUK MAKARANTA LITTATAFAINA ‘YAN CIKIN BADALAR KANON DABO.

HAUWA-KULU -3
BAKO DAGA KUMASI (GHANA)
Y
ammacin ranar wata Alhamis, da misalin karfe hudu na yamma, iskar damuna na kadawa mai dadin gaske a tsakar gidan su Hauwa, hadari ya gangamo, gab ake da fara ruwan sama. Innar Hauwa na zaune akan kujera ‘yar tsugunne a madafinta tana kullin alalar leda wadda za suci da daddare.
Idan ta kulla ta saka a tukunya. Tana yi tana sauraron radiyo abunta cikin shirin jakar magori A daidai wannan lokacin ita kuma Hauwa tana daga cikin dakinta a kwance kamar wadda ruwa yayiwa duka sabida yadda ta kudundune a cikin bargo bisa dindimemiyar sabuwar katifarta (vitafoam), amma kuma zuciyarta babu dadi, a kwanakinnan ta rasa me ya sa ta ke jin babu dadi sosai a cikin ranta, amma data yi tsam da ranta ta yanzun kusan ta gano dalilin hakan; LIKITA SARHAM! Shine dalili ba komai ba.
Yau kusan kwanaki bakwai kenan da take fama da wannan damuwar a kasan ranta, don ganewa da ta yi Dr. Sarham ya daina kulata, ga shi dai yana zuwa gidan ba wai ya daina zuwa ba, amma yanzu sai dai kawai ta jiyo muryarsa daga waje shi da Inna in suna babatunsu, ko nemanta ya daina yi a cikin gidan in ya zo. Balle ya zo kofar dakinta ya takaleta da Magana yadda ya saba.
Hauwa ta yi duk iyaka tunaninta don gano laifin da tayi masa da har yasa Likita Sarham ya daina shiga sabgarta ta rasa. Kamar ma gaba yake da ita yanzu.
Hauwa ta muskuta ta gyara kwanciyar ta. Wata zuciyar ta ce da ita. "To ke Hauwa? Me ye abun damuwa don Sarham ya daina kula ki? Tunda dama ba don ke yake zuwa gidan nan ba, yau ina ganin ikon Allah don Innarsa ne yake zuwa fa shine har albarkacin ta yaga dama ya kula ki. Name zaki dorawa kanki damuwa a kansa don ya ga damar daina kula ki kuma??? Tayi wani tsaki irin na jin haushin kai. Ta ce wa ranta, daga yau ita ma za ta koyi fita sabgarsa, kome yake ji dashi ya tara ya samu, me yake takama da shi da ya wuce likitancin da bai iya ba? Ina dalili da za ta damu kanta akan fushinsa da ita, fushin ma na babu gaira babu dalili? Da dai ace ta san ta yi masa wani laifi ne sai ta damu, amma tunda ta san bata yi ba ina dalili?
Don ko ta jiyo muryarsa a falon Inna, ta jawo mayafi ta fito daga daki, ta tsaya daga bakin kofarta ta gaishe shi, ta lura tana kuma jin sai ya ga dama yake amsawa, yana wani basarwa kuma a shalake kamar an yi masa dole sai ya amsa. Daga amsawar kuma baya kara ce mata komai saidai ta gaji da tsayuwarta anan ta koma dakinta.
Ta yi kwafa data tuna jiya haka haka yayi mata, ta girgiza Kai tana fadin. "yayi da ‘yar halak. Ni na damu kaina da shi, mutumin nan fa babu wata alaka ta jini tsakaninmu, banda ta zumuncin Allah da taimakon da ya saka kansa yi mana. In haka ne me zai sa canzawarsa gareni ta dame ni? Tunda ita Inna ai bai canza mata din ba kaamr ma yafi zuwa akai-akia yanzu har fiye da da, koda ba zai jima ba.
Amma abin mamaki, duk yadda ta so ta daina damuwa din da sharetan da Dr. Sarham yake yi, ta kasa daina damuwar, abin ya dameta, saboda ko ta ki ko ta so, ta san cewa Sarham wani mutum ne mai matsayi a rayuwar su, wanda ya taka muhimmiyar rawar data fi ta dan uwan jini a rayuwar ta data Innarta, wanda ya fi gaban ta dauki gaba da shi, wai don kawai ya daina kula ta bisa ra'ayin kansa.
Muhimmancinsa a gare ta ya zarta haka. Aka ce ka yiwa dana dam uzuri sau saba’in kafin ka kama shi da yi maka laifi.
Ta saka a ranta me zai hana in yazo ta tambaye shi ko tayi masa laifi ne?
Tunanin da Hauwa ke ta yi kenan wuni guda yau ta kasa moruwa, ta jibge a katifa, ta kasa fitowa ta taya Inna aikin alale, tunda kullin alala ne zata iya don ta saba tayata, ta kasa jin dadin ranta ko kadan.
Ga yawan mafarkin Babanta Malam Bilyaminu data ke yi a kwanakinnan wai ta ganshi ya dawo amma bashida lafiya. Wannan ma ya kara dugunzuma damuwar Hauwa kuma ta kasa gayawa Inna don kada ta daga mata hankali in tace tana yawan ganin Malam ya dawo cikin halin rashin lafiya na shanyewar barin jiki.
Cikin wannan halin damuwar da Hauwa ke ciki, harda hawaye na diga ta gefen idon ta, daga bakin kofar shigowa tsakar gidansu aka rafka wata irin sallama cikin muryar girma da koshin lafiya.
Chapter 1 · 0% Book details