Sashe 6
Hauwa Kulu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sukayi in ya tuna sai yaji ransa baya so, ace dansa ya auri ‘yar mai abinci a tasha, sai hya kada baki ya ce, "Lelen Abba na dade ina jiran ranar da za ka zo min da wannan bayanin akan Hauwa dinnan ai, na kuma san dama da wuya in ba karshen alewa kasa ba. Ni ban yarda wai ba son Hauwan nan ka ke yi ba, ka cire maganar wani JIHADI da ka ke fakewa da shi, don jihadi kala-kala ne in shine akwai wanda yafi wannan lada ma, amma ka sani ni ba yaro ba ne kamar ka. Da zan tsaya yaudarar kaina da kaina. Ka saka sa a ranka kawai tuntuni, ko recently, ka fara son yarinyar nan ka fara developing interest a kan ta yanzu, ko ba yanzu ba. Well, ba ni da hujjar hana ka, amma ka shirya daukar dala babu gammo daga matarka, wai makauniya da auren nesa. Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Na yarda wadannan mutanen suna cikin kaddararka, don haka ba ni da ja cikin abin da Allah ya hukunta. Kawai dai bana so ka gurbata zaman lafiyan gidanka da auren rainon tasha. Ka san rayuwar sayarda abinci a Tashar mota kuwa? Da kallon da akewa mai yin ta? Hummm. Amma tunda ka ga za ka iya ka kuma yarda da tarbiyyarta ni shawara ce kawai tsakaninmu. Zan tura insha Allahu a karba maka auren kafin iyayen nata su koma Ghanan. Ko babu komai ni ma ban san yaya karshen rayuwar nawa 'ya'ya matan zai kasance watarana ba, ba wanda aka gama yiwa halitta sai ranar da ya koma ga mahaliccinsa". Wani irin relief ya sauka a zuciyar Dr. Sarham. Tunda har ya samu hadin kan Abba ya san na Mama Maishari’ah ma ba zai zamo mai wahala ba. Mai wahalar da ma Innar Hauwa ce, ita kuma ya gane ba ra'ayinta daya da maigidanta akan Hauwa ba don haka nata ra’ayin ba zai yi tasiri ba, yana da tabbacin malam Bilyaminu din zai iya janyo masa ra'ayinta. Kenan matsalar in ma zai sameta to zata fi karfi daga matarsa uwar 'yar sa Dr. Madinah ne. Madinah zata fahimci komai amma banda lamarin kishiya ya sani. Inda shine babban weakness dinta. Kamar Sarham ya sani kuwa, don kuwa Malam Bilyaminu yau wuni ya yi yana ganar da Inna, yana fadakar da ita don Hauwa ta rasa ido ba yana nufin bata da feeling ba, don Hauwa bata da ido baya nufin bazata so daukar yaran data haifa ba, ya kuma ce Allah ya halatta mata yin aure wanda sunnar kowanne musulmi ne don kare kansa daga dattin zina. Bata da hujja har a wurin Allah na cewa bazatayi aure ba, tunda yarinyar nan duk da lalurar ba ta rasa ma su son aurenta jajirtattun mazaje irin haka ba. Yace idan ma ta hana Sarham to shi zai baiwa Salisu. Bata yadda zaayi ya aje Hauwa a gabansa ba aure in ta kai shekaru 20 wai don kawai bata gani. In ita bata gani su sun ganta sun ce tayi musu. Duk yadda Inna ta so ta ganar da shi abin da ta ke hangowa wato wulakanci da tozarci take gujewa Hauwa Malam Bilyaminu ya ko ki sauraronta, cewa yake. “Ba ki isa ki katange ta daga duk wata rubutacciyar kaddararta ba. Mai lafiya ma yana shan wahala a gidan aure yana fuskantar kalubale kala-kala ba sai mai nakasa kadai ba. Aure ibadah ne dama ai, ba gidan jin dadi da kashe ahu bane. Ni dai fatana da addu’ata Allah ya ba Hauwa dacewa a cikinsa, dama kowacce irin rayuwar aure ta samu kanta. Na yi amanna ibadah ce. Zan roki Allah yayi mata jagora a duk inda ta shiga ba tareda Dan Adam yayi mata jagora ba. Na yarda da wannan yaron SARHAMU dari bisa dari, daya ne tamkar da dubu, shi din mutum ne har da rabi, ban da dan Adam butulu ne a halittarsa, ai ko wani daban Sarhamu ya kawo miki koda kuturu ne, ya ce ki ba shi auren Hauwa-Kulu ba shi da kansa ba, tofa bai kamata ki daga ido a kan al'amarin kina jayayya dashi ba, balle shi da kansa yace zai aureta ba wani ne ya tursasa shi ba. Duk abin da ki ke hango mata Allah Ubangiji da ya halicce ta ya riga ki hangowa, kuma yana tare da ita fiye da ke". Inna ta rasa yadda za ta yi Malam ya fahimce ta, ita kam in ba tare da ita Hauwa za ta je gidan miji ba, hankalinta ba zai taba kwanciya ba. Hauwan da ko Saka always pad sai da ta tsaya tsayin daka ta koya mata. Ita har gobe Hauwa kamar 'yar goge take a wurinta, musamman da ta lura hankalin HAUWA yafi karkata ga Jamilu ta kara tabbatarwa kanta Hauwa bata gama sanin ciwon kanta ba har gobe. Ta kasa boye wannan tunanin nata har sai da ta furta shi ga maigidan nata. Na cewa saidai su tafi tare gidan mijin ita da Hauwa. Wannan karon dariya Inna ta bai wa Malam Bilyaminu ya ce, "yanzu idan na kyaleki sai ki bar ni nikadai a Ghana, nida nake sabon angonki ki nima, tafi taya Hauwa zaman daki a gidan miji? Kai jama’a? yaushe kika barar da kunyar malam bahaushe har haka akan abinda kika haifa Safiyya? Bayan ni ma shekaru aru-aru ba na tare da ke inata dokin kasancewa dake?" Inna ta ji kunya sosai harda sunkuyar da kai, ta ce, "Malam! To ai abin ne… ni kwatakwata ya ki zama daidai a kwakwalwata ko kankani. Hauwa ta je gidan Sarhamu alhalin ba ido, alhalin yana da mata har da 'ya. Da dai a ce ma babu kishiyar ko Hauwa lafiyarta kalau ko daga shi sai ita, sai na fi kowa farin ciki da wannan al'amarin. Don jinin Sarhamu abin so ne da kauna agareni". Malam Bilyaminu ya ce, "Ki manta da komai kike hange ki bar Hauwa a hannun Ubangijinta, ki daina tunanin ke ce mai kare ta ko ke kadai ce garkuwarta. Allah shi ne mai kiyaye bayinSa, kuma Shi kadai ne garkuwar bayinSa a ko'ina suke, kada wannan ya shafi imanin ki da kaddara". **** ***** *** A daidai wannan lokacin, shikuma Sarham, yana durkushe gaban Mama shi kuma, wato mai shari’a Haj. Maimunatu yana fada mata bukatar da yake da ita a safiyar yau, don Daddy ya ce ya je ya nemo yarda da amincewar mahaifiyarsa da albarkar ta, kafin ya yarda ya je gun Baban Hauwa sai mahaifiyarsa ta amince ta kuma sanya albarka. Mama shiru ta yi tana sauraron Sarham har ya kai aya a kan bukatarsa na auren HAUWA KULU nan da kwana uku kafin iyayenta su koma Ghana da ita. Mama ta dade tana kallonsa kansa a sunkuye, kafin ta gyara zama tace, Sarham ni abin da ka zo da shi yanzu bai zamo bako a gare ni ba, ko da ma na san watarana makamanciyar wannan na nan tafe tsakanin ka da ‘yar mutanen Badala. Na kyale ka ne in ga iya gudun ruwanka a kan mutanenka na Badala. Sarham ka daina fakewa da cewa za ka auri Hauwa don kada a koma Ghana da ita, wannan hujja ce wadda hankali ma ba zai taba kamawa ba. Ka fito kai tsaye ka ce min za ka auri yarinyar da ka dade kana so, ba tare da kai kanka ka san son nata ka ke yi ba….". Dagowa ya yi cikin mamaki yana kallon bakin Mamansa wato Mai Shari'a da ke wannan furucin da shi bai taba sani ba, wadda a dabi'arta yasan ita bata daukar abubuwan da bata da hujja, sannan kuma ita mama bata kallon abubuwa sakaka yadda kowa yake kallon su, komai da muhimmancin da take bashi, yana son tabbatar da sahihancin maganarta a tsakiyar kwakwalwarsa; Anya yana da digon soyayyar HAUWA komai kankantar ta cikin ransa kamar yadda iyayensa duka biyu suke ikirari? Kamar yadda Mama ke jaddadawa bayan na Abba Prof.? A saninsa duk wata soyayya dake zuciyar dan adam ya gama mallakata ga matarsa first love dinsa MADINAH. Ba wata mace da zai so a bayanta. Ba ayi ba, kuma baza’ayi ba. Mama ta yi murmushi ta ce, "Sarham, Allah ya bada sa'a, Allah ya sanya albarka a ciki, amma hakika ina jiye maka wahalar dake cikin auren nan, musamman dai ido, da ake kira mutuwar tsaye, saidai na san ladan da ke ciki ya fi wahalar dake ciki yawa. Sannan ka tsayar da adalci a tsakanin matanka ba zancen mai lafiya da marar lafiya, duk sunansu matanka. Madina ba za ta karbi al'amarin nan da sauki ba na sani, don haka sai ka aro hakuri ka kara akan wanda kake dashi. Na dade da sanyawa a raina duk ranar da ka zo min da batun auren Hauwa ‘yar mutanen Badala zan mara maka baya a bisa dalilaina na kashin kaina masu yawa”. Mama bazata daina shayar dashi mamaki ba sai sauraron ta yake da sukunin zuciya, a yadda take magana kamar dama tana jiran zuwan wannan ranar ne. Tace. "Na farko son da ka ke yi wa Madina ya yi min yawa Sarham, ban sani ba ko saboda baku da wani tsiran shekaru masu yawa ne tsakanin ku, kuma matakin ilmin ku daya kaida ita, yasa nake kallon auren naku wani abnormal, zan so kwarai ka auri macen da ka girma nesa ba kusa ba, sannan wadda kafi ilmi da wayewa sosai, kuma wadda ka ke yi wa matsakaicin so. Sannan ne zaka san dadin aure Sarham da jin cewa ka isa a gidan ka. Amma yanzu kam! Ban san sunanka ba banda mijin Madinah. Wannan din ra'ayina ne kawai na fada ba lallai sauran mutane su yarda da abin da na fada ba. wasuma cewa zasu yi na yi son kai. Amma iyaye irina zasu yarda dani. Sannan in har ba auren yarinyar nan ka yi ba 'yar mutanen Badala ni na san ba za ka taba samun kwanciyar hankalin da kake bukata ba a ko’ina kake. Ko don yadda ka damu da su, zamanta tare da kai matsayin iyalinka shi zai ba ka kwanciyar hankalin da kake nema shekara da shekaru, da albarkata nake cewa Allah Ubangiji ya sanya alkhairi a auren