← Book details Hauwa Kulu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 18

Sashe 16

Hauwa Kulu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sarham ya shafa ‘man’s pride’ din shi (sajen shi) yana gyada kai, kafin yace “wato akace dama sai hali ya zo daya ake abota, yau kam na yarda da wannan zaurancen”, ya gyada kai ya fice yana cewa, "Lallai Sumayyah kin raina ni da yawa. Watakila ma ke kike koya mata. Ke da ita ki gayamin me ye marabarku? Ai ni kanwa nake da Maijiddah, don haka na girmi kazar amarci da wani zuwa zance". Wannan magana ta kara kular da Hauwa-Kulu, yadda baya zato, Sumayyah na ta dariya ya fice ya rufo musu kofar. Bayan fitarsa Sumayyah ta takura mata sai ta ci abinci duk da fushin da ta samu kanta tana yi dole ta ci abincin tare da Sumayyah, sai da suka kammala Mama ta shigo tana jaye da akwatuna daya bayan daya ta shigo da su har guda shida, ta ce, "Sumy ga nan lefen Hauwa'u ne, da Babanta ya hana a kai. Da ma na ce sai ta zo nan zan ba ta da kaina". Kan Hauwa na kasa sabida nauyin Mama da ta ke ji. Sai Sumayyah ce ke yi wa Mama godiya. Ta soma bubbudewa tana fiddo su, kaya ne masu daraja, tsala-tsala kowanne a diddinke da mayafi mahadinsu, sai akwatin takalma da jakkuna duka flat shoes ne, da karamin akwatin kayan shafa dana wanka, Mama da kanta ta zabo kayayyakin don haka komai ya bada kala da ma’ana. Mama ta zauna tare da su suna magana da Sumayyah kan sha’anin makarantarta da abubuwan da ta ke bukata da za'a hada mata na komawa, dama duk sanda zata koma hutu sai ta sayi abubuwan bukata da babu a Jeddah irin su maggi da sauran kayan girkin kasar Hausa, don tare za su koma ita da Sarham, ta canza booking dinta ya koma daidai da nasa. A nan ne Sumayya ta ji hukuncin da aka yanke daga bakin Mama, cewa Hauwa ba za ta bi su ba. Tana tare da Mama, makaranta za ta fara zuwa itama. Sumayyah ba ta so hakan ba, amma sai ta ga Abba ya fi su hikima da tunani mai kyau. Ina Hauwa ina iya zama da Madinah? Ita kanta ta san ba wai mugunta ke da Madinah ba, ba boka ba malam, amma wutsiyar rakumi ce ta yi nesa da kasa, kuma Hauwa ba za ta taba sakewa a tsakaninsu shida Madinah ba, haka Sarham din ko yadda yake kula Hauwa a yanzu, a gaban Madinah ba za ta samu hakan ba. Sai ta ga Mama da Abba sun fi su gaskiya, gara Hauwa ta zauna a tsakaninsu inda za a kula da ita ta kara ilmin zama da Madina koda watarana Allah zai hadasu zama tare. A rana Sarham ya kan shigo dakin Sumayya wajen sau uku don kawai ya ga Hauwa, ko wannan yana faranta ran Sumayyah, amma tun ranar da ya ce ita da Sumayyah ba maraba bai kara ganin murmushin ta da kalar hakorinta ba. Ko Madina sanda aka kawo ta gidan bai yi zaryar dakin Sumayyah irin wadda yake yi a yanzu ba saboda Hauwa na fushi dashi kadai. Yadda ya kasa samun ko murmushi bayan gaisuwa daga bakin Hauwa, duk irin zaman da zai yi a dakin da irin lallashin da zaiyi mata bazata tank aba abun yana damunsa. Shi ba abun ya kwantar da kai ta hanyar janyota jikinsa ya lallasheta ba, girman kansa bazai bari ba, kada ta ga gadon barcinsa tun yanzu. Ga shi jibi insha Allah za su tashi zuwa Jeddah shi da Sumayyah. Amma har zuwa lokacin ya kasa samun kan Hauwa. Ana i-gobe zai koma Jeddah ya zo ya same su ita da Sumayyah a kitchen wai girki suke yi tare. Amma sumayyah ta kafa mata kujera ta zauna suna hira tana daga zaune tana yanka mata salad. Ta sha wani tsadadden cotton lace mai laushi ruwan jinin kare riga da zani da aka kawo kasan lace din aka yi adon wuyan rigar da shi. Sosai Hauwa ta yi wani irin kyau, sai kyallin amarci take ga daurin kan yayi mata cif-cif a kai, kai ba za ka ce babu idanun ba, don har mascara Sumayyah ta zizara mata. Ta yi mata daurin kallabi mai tsari. Sanda Sarham ya sako kai kitchen din ya ji Hauwa na ce wa sumayyah, “Gaskiya in kun tafi zan yi kewarki Aunty Sumayyah, tunda Aunty Surayyah ba ta zama a gidan nan”. Sumayyah ta ce, “Ta fi son zaman gidan kakarmu tuntuni, ita ta raineta, amma Mama ta gaya mun yau za'a dauko miki ‘yar Baffanmu na Shanono mai suna Mardiyyah, yarinyar na da hankali, na tabbata sai kin fi jin dadin zama da ita fiye da Ya Surayya”. Kamshin turaren Sarham ne ya sanar da Hauwa shigowarsa kitchen din, sai ta nutsu, ta daina maganar da ta ke yi. Wayarsa ya mika ma Hauwa ya ce, “Ga nan Inna na miki sallama sun sauka a kasar Ghana lafiya. Saura ki min kukan naki”. Ya sa mata wayar cikin hannunta, jikin Hauwa har rawa yake jin muryar Inna. Ta kankame wayar tana kiran sunan Inna, sai ta sa kuka. Inna ta ce, “Shi ya sa fa tuntuni na ki yarda likita ya hada ni da ke, na ce sai mun sauka lafiya. Don na san hakan ce za ta faru. Likita Sarhamu ya saya mana tikitin da ya kawo mu Kumasi, Hauwa ba ki ga gidanmu ba masha Allah, yayi ukun namu na Kano, ki yi biyayyar aure Hauwa, ki yi biyayya ga iyayensa da shi kansa, su ma iyayenki ne. ki gode wa Allah da ya hada ki da surukai na arziki ki zauna lafiya da kowa. Kin ji Hauwa-Kulu na?". Hauwa ta gyada kai kamar Inna na kallonta. Inna tace "madallah, ya gaya min a nan gidansu zai barki tareda Mamansa, za ki fara makarantar jami'a, hakan ya fi min kwanciyar hankali fiye da kina tare da kishiya alhalin babu idanu a tare da ke. Allah ya zama gatanku, Ya jibinci al’amarinku. Allah yayi muku albarka”. Malam Bilyaminu ya karbi wayar, shi ma nasiha sosai ya yi mata, kafin su yi sallama har lokacin Hauwa ba ta bar share hawaye ba. Mama ta shigo kitchen din tana cewa, har yanzu ba su gama girkin ba? Me ya samu Hauwa’u ta ke kuka haka?” Sarham ya juya zai fita don shi ma zuciyarsa ta tabu da hawayen Hauwa, har sai da ya gwammace da ya sani bai hada ta dasu Innar ba. Da kyar Mama ta samu ta yi shiru, ta saka hannu aka karasa abincin yau har dakinta ta ja Hauwa, inda suka zauna daga ita sai Hauwa. Mama ta ce, “Na san ba zan maye miki gurbin Inna ba, amma zan kula da ke kamar yadda nake kula da nawa yaran. Na san ana cewa iyayen miji basu da kirki, but I want to be an exception! Ki bani damar zama Uwa a gareki Hauwa, saboda inason Sarham, inason duk abinda zai zama kwanciyar hankali a gareshi, ki ga yadda zan zame miki uwar goyo da zani”. Da ire-iren wadannan kalaman Mama ta lallashe ta suka ci abinci a dinning har da ita. Sarham na idar da sallar la’asar ya soma hada kayan tafiyarsa. Haka Sumayyah tun jiya ta hada nata kowannensu jiki a sanyaye, kuma ba don komaijikinsu yayila’asar ba sai don barin Hauwa da zasu yi ita kadai sai Mama dake wuni a chamber. Bayan isha ne Sarham ya zo yin sallama officially again da Hauwa. A lokacin ita har ta yi shirin bacci. Sumayyah na can falo suna kallon talabijin da iyayensu. Hauwa na karanta addu’ar kwanciya ta ji zaman Sarham a gefen gadon, har jikinsa na gugar kafafunta. Koda ma can turaren shi da sallamarshi sun riga shi isowa gare ta. Da wayo da dabara ya kama hannunta ya dora bisa saitin zuciyarsa. Hauwa na iya jin yadda kirjinsa ke dagawa yana sauka. "To haka fushinki ke azabtar dani kwana da kwanakin nan Nana Hauwa'u. Ba zan dai iya bayyana miki bane don kin yi kankanta kuma kinga nan gidanmu ne, banida sakewa a cikinsa". Wannan kyakkyawan kawaicin na Dr. Sarham har gobe yana tare da shi, ba ya hada girman iyayensa da girman idanunsu da komai na rayuwarsa. “Maijidda zan tafi, ba zan samu dan abin da zan ke tunawa da irin wannan lokacin ba? Dana tafi na bar mata ta HAUWA karkashin kulawar aurena da iyayena ba? Ko da kuwa sallama mai kyau ta fatar baki ce??? Na san kina fushi da ni, amma exactly ina son sanin laifin da na yi miki Maijidda. Honestly speaking bansan laifina ba”. A hankali Hauwa ta janye hannunta daga saman kirjinsa, don ta kasa jure sauyukan da hakan ke haifar mata cikin jikinta da ruhinta, da kyar ta ce, “ni ba ka yi min laifin komai ba, hasali ma sai tarin alkhairi ni da iyayena, irin wanda baki ba zai iya furtawa ba. Sannan babu kalaman da za su isa godewa. Ina rokon Ubangijiya fini godewa. Idan har na yi fushi da kai a kan wani abu Yaya Sarham, to ya zama rashin adalci da butulci irinna an adam, domin ka yi min komai and beyond, da ya cancanci in gode maka ba inyi fushi da kai ba. Kawai in na tuna cewa ni ba SO ne ya sa ka aure ni ba, tausayi ne da son kyautata rayuwata sai in ji komai na duniya ya daina yi min dadi…, burikana na shekara daa shekaru sai inji sun fita kaina”. Sarham ya ce cikin daga murya, “Shi tausayin ba SO ne yake yin sanadinsa ba? Ko kuwa in tausayi ne ashe duk masu lalurar ido na aibitin Murtala na Kano dana yiwa aikin ido sai in bisu in aure su, bana son ki zan kawo ki cikin gidanmu, in hada ki cikin iyalina Maijidda? Bana sonki zan miki takwara da diyar cikina? Tun ma baki zama matata ba?” Kawai sai Hauwa ta ji kukan dadi ya kwace mata, ta sa tafukanta ta rufe fuskarta tana yinsa riiiii-riiiii. A hakan ba ta yi aune ba ta ji numfashin Sarham daf da fuskarta, ya ce, “kin yi kankanta in tsaya ina gaya miki abinda kike son ji daga gareni. Amma duk da haka ina so ki saka
Chapter 16 · 0% Book details