← Book details Gidan Marayu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 18

Sashe 2

Gidan Marayu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gida ne yahad'a b'angarori dayawa acikin gidan kowa da kalan matsayin shi tundaga chairman akwai Director HOD Akwai Deen Head of the House akwai woman Right akwai b'angarori dayawa y'an wata d'aya zuwa wata tara gunsu daban y'an shekara d'aya zuwa biyu gunsu daban shekara hudu zuwa shida ,goma zuwa sha biyu, sha biyu zuwa sha biyar sha,biyar zuwa ashirin in sunkai shekara ashirin ko sha tara ,ana komar dasu cikin gari suzauna koza zo neman auren su anayin sa,a kuwa ana aurer dasu babu wata matsala..

Sungama cike cike suka zauna suna hutawa duk abun yabasu tausayi in dasabo sun saba da wannan sai kana aiki a gidan ne zaka gane ..

Rafi,atu ",Maryam yanzu muhaka zamu rayu kenan kullum cikin tsangwama da gori wasu su aibatamu wasu ,susomu " karmu sawannan a ranmu wataran zaizame mana labari.amma Rukayya kinsan Safiya jiya zagin mutayi wai mu,kowa in antashi daga makaranta gida yakewucewa mukuma sai dai muwuce gidan marayu"Maryam rayuwarki da Sauk'i a kan namu dan ance iyayenki rasuwa sukayu wutane ya kwounasu "kusan ance watane tazo tasa wutan kuma tunda sukazo babu wani d'an uwansu da yatab'a zuwa ganin su.kukasan ko gudowa sukayi irin masoyan nan ne "duk da haka ke a cikin gida kike" nifa a cikin jeji aka tsince ni wayasan kwanakin danayi inacikin jejin "Rufi,atu "nikuma wata matace takawoni amma tace wai watane zata jefa ni,a cikin rigiya shine ta karb'oni " duk kanmu abun tausayi ne ..

Dan ma,munsamu uwar kirki bamutab'a rashin wani abuba sai dai iyayen mu,daman bamusan dad'in zama dasuba.

A sallah mu y'an gatane,mukan tashi da kaya kala wajen uku ga nuna kulawa da,akeyi mana "abun burgewan tunda akasan mu qawaye ne shiyasa jama,a suke cemana y'an uku.

Rayuwan maraici abune mai wahalan gaske duk yadda kayi wataran sai katino iyayen ka fatan mudai Allah yasa tahanyan aure aka samemu"Maryam " nikuwa in ta hanyan banza aka sameni bazan tab'a yafewa kaina ba.

"Mama Salamatu " meyasa kuke haka ne,banace kudaina zama kuna irin hiran nan ba "kiyi hak'uri zamu kiyaye in sha Allahu kutashi kuje ankawo wani yaro kuduba shi dan kune manya a gidan toh mama da sauri suka d'auki hijabi sai b'angaren ,yara sunji tausayin yaron Sosai sai da sukayi hawaye gashi farine yaron tsutsan yafara tab'a jikin shi wani har yashiga cikin sa za,a kaishi babban Asibiti a duba shi " mama yagana ya jikin yaron da Sauk'i Sosai Allah yabashi lafiya

Amin ya rabbi "kutashi kutafi kar dare yayi sai da safe,lokacin da suka koma kowacce jikinta yayi sanyi ganin yaron da sukayi.

Da safe jikinsu a sanyaye sukaje makaranta suna ganin kaman yaron zai mutu ,dan ko kukan baya,iyawa sosai Allah yatashi kafad'an ka Amin Maryam ...✍

Maman Khairat ce
[25/05, 07:34] Maman Khairat: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
GIDAN MARAYU
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Story And writing by Amina maaji maman Khairat📚✍🏿

True life story

Paid book 200

Last free page 1/8

🅿️7️⃣⏭️8️⃣

*Gidan marayu labarin yazo dawani sark'ak'iya zaki iya biyan dari biyu ta wannan Acc no 4271914014 Fcmb ko katin mtn ta,wannan number 08068748984 ,ki mallaki naki true life story ne akwai tarin darasi dayawa a cikin labarin babu soyayya sai tausayi rashin imani ga rashin bada kulawa a marayu labari ne daya faru da gaske ba k'irk'irerren labari ba, ilmantar wa nisha d'antarwa da kuma fad'akarwa, duk akan farashi mai sauk'i.*

___________Taya zaki fad'i haka shegiya kuma E mana bamu,isa muce mu y'an halak ne ba.

Washe gari da safe suka shirya suka wuce makaranta suna shekaran k'arshe a secondary schools ,tunda aka buga break sunfitoh suna zaune wata ce safiya "ku y'an gidan marayu meyasa,kuke shiga cikin masu,iyaye kubari kurik'e maraicin kuma na,taya zakudinga shiga cikin masu asali,har Rukayya zatayi magana maryam tace tabarta " ke Safiya mekike fad'a haka ne? ina ruwan ka,nizakiyiwa rashin kunya ko? Tunda ,aka fara maganan dukkan su shiru sukayi har akatashi daga makaranta har suka isa "lafiya y'an uku?" mama salamatu wata ce kullum take cimana mutunci wai mu y'an gidan shegu "mekukayi mata sunawa ne,wannan abun ba,abun wasa bane ,yakamata kutsaya kuji da kyau " gobe zamuje.

makarantan ,in gawanda ya d'aure musu gindi, babu Wanda ya,isa yacimuku mutunci kuma yarane kaman kowa.

Take tatafi office d'in Director tasanar dashi yace gobe zasuje makarantan ,karsu damu ,k'arfe biyar aka kawo wata yarinya a cikin kwandon shera yara Wanda bazasu wuce shekara goma ba suka kawo ta,"mai gadi nan ne gidan marayu?"E nan ne lafiya a bayan layin jorisalam ne mukaga yarinyan nan a cikin abun zuba shara" kuzo,
muje in rakaku ,anan ne zaku fad'i duk abun da kukasani.

,a lokacin da suka,isa ,a lokacin chief yake rufe office dinshi lafiya ? Kushigo bude marfin yayi yarinya ce aka lankwasata aka rufeta ,d'aukan ta akayi wuyar tagagara tsayuwa Sosai gata gala bai,ta Asibiti aka wuce da ita, kafun a d'auki wasu bayanai nata. Washe gari duk wani Wanda yakeda matsayi yatafi cikin makarantan Su Rafi,atu office din principal suka wuce sukayi mishi bayani aikawa yayi aka kira Safiya"kijuya kije Kitaho mana da iyayen ki ,waya gayamiki basuda iyaye dake, kikeyi musu gori bazamu laminci wannan cin zarafin ba yakamata kigane kedasu waye duk kikirasu koransu akayi akabawa ma,aikatan gidan marayu hakuri akan hakan bazai sake faruwa ba.

SUMSUMMA
Wani anguwa ce dake cikin garin damaturu babu yaren da babu amma fulani sunfi yawa a nan su Sayyada suke rayuwan su,ita da iyayen ta,tun da,aka tashi daga makaranta su,Sulaiman da Sadiq suka d'auki kwanon baran su ,sunyi sa,a sunsamu abinci dayawa aciki har da alale duk da tayi tsami sai kusan karfe uku suka dawo suna dawowa,suka zuba musu har Inna taci "basai, kunkoma bara da dare ba tunda qawar Sayyada sunbamu abunda zamu dafa gashi munada abin dazamuci" Inna kenan kwana nawa zamuyi mutafi muyi kawai sai kiga munsamu ,wannan zaiyi amfani "shikenan Allah yakaimu Amin

Dare nayi suka wuce baran ,lokacin Inna tayi shara Sayyada tadebo ruwa tayiwa Ibrahim wanka ,marfin k'ofar buhuce aka rufe zauren da shi, d'akuna biyu ne a cikin gidan sai band'aki .

.ASALIN JANBO

Janbo shine mahaifin su Sayyada d'an asalin wani kauye ne hanyan gashua kwalji mandawa Janbo yataso d'an gatane agun mahaifinshi dan a cikin yaran shi yafison shi Mohammed bubare shine mahaifin Janbo matansa biyu yanada mata guda biyu maryamu da zainab maryamu yaranta salji da Haruna basuda imani ga San kansu da sukeyi basa wasa da rashin mutunci bulama Saleh da bubare basa,shiri tsakanin anguwan guda biyu antaso da wata k'iyayya Mara tushe dan bulama Saleh yatab'a neman Zainab bai aura ba shine kiyayya yashiga tsakanin su duk da sungirma, amma wannan kiyayyar tananan .

Soyayya mai k'arfi yashiga tsakanin Janbo da Aisha ,amma bulama Saleh yace ya haramta wanna soyayyar bai ga ,in daza,ayi ba Janbo yanada addini yataso a ruga amma yanada ilimi gashi da dukiyan shanu da tumaki kaza yanada zuciyan nema ga Tausayi,shiyasa mahaifin shi yake son shi,a lokacin yataso yazo yasami mahaifinshi" kurage gaba kubarmu, muyi auren nan tunda bai shafemu ba kuyi aiki da hankalin Ku.

"Janbo badaga niba ne,daga gun Bulama salah ne nikam na manta ma,karka damu kuci gaba da soyayyar Ku kawai Allah yabada sa,a zanje kankare akwai yayan shi bulama Sa,idu in gayamishi kaci gaba da had'a kayan auren tunda kagina d'akin dazaku zauna.

Da safe yawuce kankare yaje gun Sa,idu yagaya mishi komai"karka damu kuzo da sadaki nizan d'aura mata aure gobe da Janbo zan aika shi Saleh yazo goben godiya yayi, yayi murna,a lokacin da yasanar da Janbo abunda yake faruwa yayi murna yabada sadaki da komai abun da al,adan fulani keyi .

Yayun Janbo haushin sa,sukeji saboda yafisu komai sunyi aure har da yara ga mahaifin su,yafi son Janbo akan su,.

Lokacin da Bulama saleh yadawo shiga d'akin mahaifiyar Aisha yagaya musu,bashi babu ita in kuma aka d'aura auren nan kar,adafa komai ya sallamata a cikin zuriyan shi, mahaifiyar ta Adama taji haushin furicin maigidan nata, amma babu yadda ta,iya "Aisha kiyi hak'uri kizauna karki saka komai a ranki gacen kayanki da muka siya za,aje ajera miki, shanayen ki guda biyu kibari zamu kulamiki da shi amma gobe za,a siyar da guda d'aya ayi miki siyayya kinji ." nagode kizauna kinga kekadai na haifa banso auranki,yazama haka ba.

Da,dare a,kakai amarya Aisha d'akin ta,murna sukayi Bubare yayi musu komai a she haushi yakebawa sauran yayun shi sunyi sati sukafara zuwa da dare suna damun shi yagane ana hakan yasamu ,mahaifin shi yasanar da shi"Janbo abun da nakeso da kai ka gudu gobe ko jibi kasiyar da shanun ka guda uku da tumaki biyar, ka had'a kud'in katafi wani gari sai ,in abun ya lafa kadawo kaji "zantafi jibi gobe zanyi duk yadda kace ,Washe gari duk a,kasiyar da abunda suka lissafa,Aisha har gida taje dan yin bankwana da mahaifiyar ta da dare suka tattara suka gudu Inna Zainab tasha kuka gashi Janbo ta haifa ,shi kadai.

Dare nayi sukaje sunmayar Janbo yananan Bubare ne yayi dabara kaman mutane ,suka hau jibga a she ciyawa ne ,ba komai ba jin bugun yayi yawa Bubare yazo " kai meye haka wato kune ko har da kai yayan Aisha Washe gari sukayi shawara ,a kan su kawar da Bubare shikuwa yakirasu yace "Janbo yabar dukiyan shi kurike mishi Amana ,a daren suka murd'e mishi gaban shi ,suka kashe shi Washe gari sai gawan shi ,aka gani sunkashe mahaifin su da kan su.

``` wasan yanzu aka fara kudai kubiyo ni kusha karatu sai mun had'u a paid group ```

Maman Khairat ce
[25/05, 07:34] Maman Khairat: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
GIDAN MARAYU
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

🅿️9️⃣⏭️1️⃣0️⃣

Mutuwan Bubare yabawa ,kowa mamaki mutuwa babu rashin lafiya ,salji da Haruna kodamun su mutuwan bai yiba ,haka aka gama zaman makoki,lokacin da Janbo yasamu labarin rasuwan mahaifin shi ranshi yab'aci sosai dan sai da,akayi sadakan bakwai kafun yasani ,zuwa sukayi da Aisha sukayi kwana goma sukajuya da tumaki guda shida,nacikin garken sa

Inna Zainab tanashan wahala agun su Haruna, sutayi mata habaice,habaice ko kulasu batayi.
Chapter 2 · 0% Book details