← Book details Gidan Marayu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 18

Sashe 16

Gidan Marayu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallama sukayi sukabaro wajen " babu inda suka nufa sai gida"Rashida tana parlour ita kad'ai sai jin shigowar mutum tayi ,"sannu da zuwa yauwa "nikuwa suwaye suka d'auke mun yarona tun yana jariri " wani yaron kenan kardai kacemun yaron daba,ayi suna ba shine "eh " wani dariya tayi "nine nad'aukeshi nakaishi k'ofar wata mata, tana soya k'osai na,ajiye shi nagudu dan naji tausayin shine ban sa,ankashe shiba tunda akan yaron kakeyimun gadara,zafgamata mari yayi " kizo kinuna mun ,sama da shekara 29 kika cutar dani ban yafemiki ba"Faruq kaji wai, kof'ar wata mata takaishi mai suya"a wani anguwa a *Abasha* takaishi wajen bayan tasha "kishiga mota " muje kawai tashiga mota, aguje yafigi motar suka hau hanya .

Maman Khairat ce
[25/05, 07:35] Maman Khairat: 🅿️8️⃣1️⃣⏭️8️⃣2️⃣

Sun,isa wajen figota yayi a cikin motar "kinunamun in da kika yasar mun da yaro, in bahaka ba duk zuriyan ku zan kama in d'aure kinji nagaya miki" Abokina inaso mubi komai a sannu "kaga mutane hankalin su yafara dawowa kanmu ..

Gwoggo tafitoh zatabawa yaro kud'i yasiyo mata suger taga mutane har zata koma ,wani abu yace tadawo" lafiya kuwa? da duk kansu sunyi shiru ganin tsohuwa ce karkuma subar gayamata,yazama sunada amsar dazasu samu "kaka wannan ceta tazo ta yasar munda d'a shekaru a shirin da tara" mekace ka,k'ara fad'a "Alhamdulillah yauzanyi kukan farin ciki " kuzo muwuce cikin gida dan d'aga darajan mu,bayan sunshiga suka zauna da,aka shinfid'a musu taburma kukiramun Wannan number kunji sa number Malam nura akayi tafara ringing suka mik'a mata "d'an Albarka kazo inason ganin ka " ganinan zuwa minti sha biyar sai gashinan ganin mota a k'ofar gidan Su yabashi mamaki shiga yayi yaga mutane"sannun Ku da zuwa "tabbas wannan yarona ne, inji Alhaji musa dan kuwa ga kamanni ya nuna ..

Gwoggo ne tayi magana " kugayamun yadda abun yafaru"kiyi musu bayani"daman nine nad'auko d'an abokiyar zamana,tun cikinta na k'arami naso in zubar da shi babu kalan abunda banyi ba har karkashi nasaka,a bakin k'ofar band'aki toh ranan data haihu da kwana biyu ,a ranan da yacika kwana biyu a ranan nad'auke shi ,nashiga d'akin ta kusan mangariba natarar ta had'a shayi shine najefa magani ,a ciki kasancewar ita ba yar gari bace shiyasa y'an uwanta basuzo ba ,da dare naje na d'auke yaron ..

Natab'a wucewa naga ana siyar da waina mutane, suncika har nima nasiya ,dana tambaya akace batada yaro shine ,nakawo shi ,nan na,ajiye shi danaso inyi mishi wani abu nabarshi ..

Afusace Alhaji musa yatashi "tabbas anyi haka,wani kayane ajikin yaron ?" Kayan yarane blue har zanin goyon nashi ,tashi Gwoggo tayi tad'auko da abunda ta tsinci Malam Nura a ciki..

Rungume mahaifinshi Malam Nura yayi "yanzu kekika rabani da mahaifana kikasa na sheganta kaina koniba d'an sunna bane kincutar dani kin zanlince ni Allah zai sakamun..

Gwoggo ne tayi magana a she ana,iya samun mutane irin ku,azzalumai, banbar Nura cikin walak'anci ba yayi karatun addini nina shayar da shi nakuma sskashi a makaranta ya yi,karatu yasamu aiki Yakuma yi aure " kincutar da kanki Allah kuma bazai tab'a barin kiba nasakawa Yaron suna Nura nayi mishi yanka ..

"Mungode sosai yadda kika rik'e Yaron nan batare da kinnuna bake kika haifeshi ba muna godiya a gareki ..Malam Nura ,nad'auka nibanida asali nad'auka ni tsincecce ne nad'auka iyayena kwounewa sukayi a she ni d'an asali ne a kullum addu,a ta Allah yahad'ani da dangina da iyayena ,gashi kuwa " kardai kacemun kaine Mijin Rukayya eh nine Abba Faruq baka ganeni bane?

Allah mai ,iko lalle duniya makaranta ne Babba yanzu duk fad'i tashin da mukeyi a she kana kusa danima Allah ya,isa abun isarwa Allah kayi mana mai kyau "yanzu wannan duk kanmu ya ishemu babban darasi mai tarin yawa, Allah yarufa mana A siri Amin

Gwoggo ", a kullum burina,kafun in mutu inga iyayenka Nura sai gashi yanzu nagansu wannan shine mahaifinka na,asali babu Wanda zai dunga kiranka da d'an Gwoggo dan haka kagodewa mai sama,dan shine duk yatsara wannan abun kuma sai yakasance ..

Hakane hawaye duk yajik'a musu gaban riga dan kuka"haba Nura kaine mai yin wa,azi a mutane sai gashi Kaine Yau da fitinan kuka namanta rabona da in ganka kana kuka tun kana yaro.

Gwoggo bawai inayin kukannan saboda wani dalili bane saboda mutuwar uwata da banganta ba shine in dan gatane kinyi munshi koda iyayena ne ,iyakacin abunda zasuyi mun kenan.

" yanzu muyafewa juna koyau na mutu Alhamdulillah tunda Nura bazai sha wahala ba gashi ga iyayen sh.

Tsabagen dad'i ko iya magana Alhaji musa bayayi saboda murna, in yakalli Rashida sai yaji kaman ya,kasheta sunjima kafun sukawuce bai wuce gida ba gidan su Rashida yawuce har gaban iyayenta yakaranta musu abunda tayi yakuma bata takaddan ta kafun suka koma gida .

Tunda yashigo gida Maryam tanata mishi sannu da zuwa amma sama,sama yake amsawa "meyafaru ne duk abunda yafaru yagaya mata,tare da cewa mijin Rukayya shine d'anshi murna tayi daga k'arshe " meyasa ka saketa "bazan tab'a zama da mungu ba muddin in nasan shi mungune ..

" koma yaya ne hak'uri zakayi"Maryam daman natab'a sakinta guda d'aya yanzu nak'ari sa kinga babu zancen in dawo da ita har gida zankai mata kayan ta ,dan nace karta dawo mun gida ..

Rafi,atu tasake ranta har d'an jiki tayi dan kullum cikin janhakali sukeyi mata da nasiha har tayi sanyi sai shirin tafiya karatu duk Kansu sukeyi ..

KWALJI MANDAWA

Su Haruna zasuje gashuwa su sayar da shanun da suka boye motar su ,tayi hatsari take d'ayan shi yarasu Haruna yasamu karaya ,a cinya ga hannu duka biyu sun karye kowa ya ganshi sai ya tausaya mishi ana zaman makoki ana jinyar k'afan Haruna ,lokacin da su Inna sukaji labari sunzo gaisuwa a nan ne Haruna yace ,a kirawosu "kuyi hak'uri hak'ika mun cutar da Ku har,a siri mukayi muku,mune mukaje har gida muka kashe Janbo mune muka kashe Baffa ,kuyafe mana mune muka sa ,aka saka muku wuta dan munduba gidan Ku a kafe yake dan haka ni yanzu nawa yak'are dan Allah kuyafe muna,.", mund'auki shanun da muka boye dan musiyar da tinkiyoyi shine motar tayi hatsari direban bai mutuba mune dai kud'in motar muka biya gaba d'aya

" babu komai munyafe muku"shikuma Janbo kujira Wanda ya halicce shi yamuku abunda zai muku, tashi yaran sukayi yana kiransu sunk'i wai wayansu sai Garbati "wannan kad'an makagani badai cin dukiyan marayu ba" ko had'a ido bayayi da Garbati
[25/05, 07:35] Maman Khairat: 🅿️8️⃣3️⃣⏭️8️⃣4️⃣

Zonan Garbati badai wani abu kayi musuba?aa Inna banyi musu komai ba Allah ne yakamasu ta hanyar dayaga dama amma babu hanuna ..
Shikenan bakayimun k'arya Sadiq "inna kenan meyasa kikadamu da Wanda sukasamu bara " karka damu yanzu kam yawuce"Inna zaiwuce dai saboda yawon baran damukayi bazan tab'a mantawa da bara ba, munsha wahala wataran sai munyi wa mutane aiki kafun musamu abunda zamuci mukan sha wahala wataran muna gani abincin ya lalace fa"hmm Sadiq nasan ka da kafiya "kiduba sai yanzu nagama makaranta dan talauci ..

" karka damu saura kad'an tunda Allah yanuna musu iyakar su ,sosai makuwa gobe zamu koma saboda makarantan Sayyada tunda yanzu tayi nisa da Ibrahim..
Duk wani gaishe gaishe sunyi washe gari suka dawo damaturu duk a gajiye suke ,maman Sadiya tazo ta,aziyya da Hajiya zulai dan tasana diyan Sayayda duk tadaina wasu irin halayya irin har malam nura,dan shikam wuni yakusanyi, .

Malam Nura niyanzu bansan meke damunka ba "duk munga iyayen mu, kaifa d'an asali ne gashi mahaifin ka yasamu yabo dan Allah kamanta Rukayya kenan dan nasamu iyayena ba shine zaisa in samu nutsuwa kawai rayuwar ne takeban tsoro ..

Shikenan kiduba yadda Allah yatsara Allah dai yasa mudace,Amin

Gashi gobe zakatafi makaranta Allah yamuku jagora sasai " bantab'a zaton zanyi karatu ba

BAYAN WASU SHEKARU

Malam Nura yana barno yana karatu ,SU Rafi,atu suna university suna karatu kowa da department d',inshi duk course daban daban suke karanta wa, wani ma,aikacin gidan marayu yanuna yana matuk'ar son Rafi,atu dan Soyayyar matayi nisa Abba faruq yace sai tagama tunda sunyi kusan gamawa, Suwaiba dataji labari tace a d'aura kar,ajira tagama shikenan aka daura da likitan gidan marayu Malam umar tunda sukayi aure babu wata matsala sunason junan su sosai soyayya mai tsafta sukeyi ..

ALHAJI MUSA

"Nake ganin zamu koma gidan cen dan tafi babba kuma gayara banaso yaran suna kwana sukadai tun da,aka gayamata sukafara tattare kayan su,dan dan har gyara ,akayi .

Rashin lafiya ne yakama Gwoggo mai tsanani,shine Malam Nura yadawo ,a lokacin da yadawo a gidan Gwoggo ya sauk,a ana shirin kaita Asibiti Gwoggo ", gani meke damun ki," Nura zan barka kaci gaba da hakuri rike mishi hannu tayi

Ga Baban ka kayi mishi biyayya ka kula da matarka karka barta tayi kuka kaci gaba da tarbiyan da nabaka kadinga yafiya kazama mai hakuri ,burinka nacewa zaka taimakawa marayu kacikashi hannun shi tarike shak'uwa tanemi ruwa sai kalman shahad'a..
[25/05, 07:35] Maman Khairat: 🅿️8️⃣5️⃣8️⃣6️⃣

Kwanciya malam Nura yayi a kan Gwoggo"meyasa kikatafi kika barni nakai lokacin da zansaka miki da abunda kikamun kuka yake mal cin rai "kutaimakeni Rukayya takasa bawa mijinta hak'uri kuka,,takeyi kafun kace miye antaru kowa fad'an Alkairin ta yakeyi jama,a dayawa sunyi rashin Gwoggo shiryata a kayi ,aka kaita makwancinta sai dai muce Allah yamata rahama ya gafarta mata danginta dayawa sunzo dan Alhaji kyari yad'auki dawainiyan komai koshi yafara sabawa da Gwoggo sanadiyan Yarshi..

Haka,akayi tazama har kwana bakwai kowa yakoma, duk Wanda ya kalli Nura yasan yayi rashi Sosai dan ko y'an uwanta basukai shi damuwa ba Maryam da Rafi,atu duk sunzo tare dasu a kayi zaman makoki..

" Inna kinga sakayyan rayuwa ko,haka lamarin yake yakika gani yadda Allah yayi ikon shi haka rayuwan yake kinga yadda Rayuwan yajuyawa su Haruna "hakane babu komai haka Allah yake ,ikon shi mugunta kenan gashi takomamusu .

Mutane masu Aikin NGO sunsamo Sulaiman " munzone muga wani irin rayuwa kuke ciki anyi mana kwatancen gidan Ku,E mungode amma kutaimakeni akwai wani gida da sunfimu buk'ata dan Allah kuzo muje kufara d'aukan sunan su ,tunda kunce kayan abinci zakubayar"karka damu "zamu d'auki sunan mukuma d'auki sunan Ku, sannan zamu baka wani aikin a cikin mu ka,iya rubutu? E na,iya har karatu" shikenan
Chapter 16 · 0% Book details