← Book details Gangar Jikinsa Na Aura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 26

Sashe 23

Gangar Jikinsa Na Aura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

GANGARJIKINSA NA AURA 1 Part 4 Posted by ANaM Dorayi on 02:25 PM, 30-Apr-15 Under: Gangarjikinsa ta Aura A zaure malam habu ya shimfida tabarmar kaba dawani yagulallen filo da zanin gado irin na da da dadinnan shekara aru aru da suka shude. Nan neshimfidarsa da yake kwana nan ne dakinsa danduk dare duk sanyi da damuna a nan yake sabodaiya abu ta mamaye dakunan gidan. Dakinsa din ya barwa hanna data girma ya dawo zaure don da datana yarinya tare suke kwana a dakin. Ko dayaushe hannah zaka ganta a zaune a gefenbabanta tana lallashinsa tana wayar masa dakaigame da makarantarsu. Tana nuna masamuhimmancin karatu da kuma irin bacin ran da haisam zaiji idan bata koma ba.Ta kwashe labarun abubuwan da suka faru tuntana aji daya har tazo aji shida yadda haisam yakekula da ita da irin tataburzar da aka sha yi akantada dalibai da malamai har ya kwatar mata yancintababu mai dukanta ko zaginta yanzu, kuma yayialkawari zai iya kashe ko waye yake son ya takura mata. Malam habu ya gamsu sosai da bayananhanna ya kuma san haisam ba zai yadda a cuce taba. Hutu ya rage sati guda sai ga uwar biyu ta dira agarin su hanna ta iske hanna da mahaifinta a zaurea zaune zance daya dai suke ta nanatawa kullumshine zancen ya barta ta koma makaranta. Bayansun gaisa da uwarbiyu ta fadi abunda ke tafe da itacewar tazo ne ta tafi da hanna hutu ya kare sai malam habu ya kekashe idanuwansa ya ce shifababu inda hanna zata je. Hanna tayi mamaki da tajiya fadi haka yanzu bayan da ya yarda da tayi masabayani sai kawai hanna ta rushe da kuka, magiyarduniyar nan uwar biyu ta dinga yiwa malam habuamma yaki yarda daga karshe uwar biyu tayi musu sallama ta tafi. Tana isa kazaure ta wuce gidan susafiyanu abokin haisam bata sameshiba ance yanakano sai ta koma gida ta zuba ido ko allah zai jehomata haisam ko safiyanu idan zasu kawo sayayyarhanna ta makaranta tunda sunsan hutu ya karezasu kawo. Har ana gobe a koma makaranta uwar biyu bata ga safiyanu ba balle haisam. A can kuwahanna hankalinta ya gama tashi taji shiru yayahaisam baizo ya taya ta rokar babanta , sai ta daukashima yayi fushi ne yace to a bar masa 'yarsa kartayi karatun mana. Da la'asar likis hanna damahaifinta suna zaune akan lintsimemiyar tabarmar kaba a zauren kasa da rufin ciyawa hanna kukatake yau tun safe. Malam habu lallashin duniyar nantayi shiru ta hakura tama cirewa ranta makarantardon shi ya gama magana bazata koma makarantaba . Taki ci taki sha sai kuka take rafsawa. Kwatsamsuka ji sallama daga idon na da hanna tayi sai tayi ido hudu da yaya haisam , safiyanu da uwar biyusuka yi sallama suka shigo. Da sauri hanna tadauko musu tabarma ta shimfida musu sukazazzauna ta koma ta dauko musu ruwa a randacikin kwanan sha. Ta kawo ta durkusa kasa tagaishe su ta koma gefe ta zauna. Murna ce ta rufe malam habu yama rasa inda zaisa wadannanmanyan baki, yan gayu, ya lalubo kudi a aljihunsaya ce da hannah tayi maza taje bakin kasuwa tasuyo musu fura da nono, su haisam suka ce kaihaba ai su a koshe suke ya barshi kawai. Bayansun gaggaisa malam habu ya gama yi musu sannu da zuwab da tako kare sai safiyanu ya nisayace''baba munzo ne mu ba da hakuri akan dalilinda yasa ka hana hanna zuwa makaranta. Shinemuka zo da kammu mu roke ka baba duka dukasaura wata nawa ne yanzu hanna zata gamakaratunta ta dawo gida'' nan da nan malam habu ya canja fuskar fara'ar dayake ta gushe yace''wai me yasa kuke sani inamuku kin kyautatawa ne ? Bana so ku tambayeniabinda zan kasa baku na gama magana don allahdon annabi ku bar zancen karatun 'yar baba. Nayanke shawara ba zata koma ba. Haisam kokarin da yake yi allah ya saka maka hakan ma ya isa basai ta kara yin wasu watannin ba. Nace uwar biyuta yi maka godiya ka cika min alkawarin da kadauka wallahi ko bata karasa ba ai ka cika alkawariba laifinka bane. Alkawari da amana ai ba karaminaiki bane cika su amma cikin yardar allah ka cika dai dai ubangiji ya saka maka da gidan aljanna.Amma hanna ba zan bari ta koma ba. Haisam yayidan murmushi game da gyaran murya ya ce'' aminbaba, amma idan baka manta ba a ranar dana karbiamanar hanna nayi alkawarin hanna zata yi karatuto kai ma a lokacin kayi min alkawari,kaga alkawari girma ne de dashi baka cika ba, kayi min alkawarinzaka bar hanna tayi karatun don sai dama nasakayi alkawarin zaka dinga turo hanna makarantabaza ka hana ta ba wataran sannan nayi makaalkawarina. Malam habu yayi shiru zuwa wani danlokaci can ya nisa yace'' anyi haka yaro haka akayi nayi maka alkawari to ammma ai abinda yarinyarnan tace gargadi fa tayi min akan kada in kara tura'yata makarantar nan kaga ai kome tayi mata batada laifi nine ban ji ba kenan'' haisam ya katseshiyace'' kare lafiyar hanna da duk wani abinda zaicuce ta yana daga cikin amanar dana dauka in allah yaso babu mai yiwa hanna wani abu. Ramla kuwata fada ne kawai a cikin bacin rai amma babuabinda zata yiwa hanna, a ina ma zata ganta balletayi mata wani abu ? Ta dai fadi son ranta dontatsorataka kaga baba kuma abinda ta fada ba hakabane hanna karatu take haikan a makaranta, kanwa ce hanna a wajena ni ne mai tsawatar matama misali da ace tana soyayya da samari amakarantar . Baba mu canfa akwai doka babuyadda za'ayi malami yayi soyayya da daliba, babukuma yadda za'ayi wata ya shigo cikin makarantardauke da wata guba taje ta cuci dalibai don haka baba ka kwantar da hankalinka ni da kai duk mucika alkawuran da muka daukarwa allah''.Malam habu yace ''to shikenan allah ya taya mucikawa. Hanna dauko kayanki ku tafi allah yakiyaye hanya''suka duka suka ce amin''sai murnata dira a zukatansu. Cikin farin ciki da jin dadihanna ta shiga ta fara hado kayanta ,iya abu tayicaraf ta fito daga bayan kyauren da take labe ta hau malam habu da fada'' au yarda kayi dawannan dadin bakin da suka yi maka. Duk wannangaskiyar data baiyana yarinya iskanci suke amakarantar don yana aiko maka dana goro shinekaki fadar allah saboda abun duniya ? Kallo dayahaisam yayi mata yaga irin wadannan mutane ne masu abun haushi masu kama da aljanu munanamasu bakin hali yaji ya tsani iya abu har baya so yakara kallon fuskar shegiya. Hannah ta ratayajakarta ta fito ko kallon iya abu bata yi ba balle tayimata sallama. Ta duka ta yiwa babanta godiya tayimasa sallama ta wuce cikin mota. Haisam ya danko kudo mai yawa ya ajiye a gaban malam habu.Safiyanu ma haka ya debo kudi ta ajiye masa sukayi masa sallama dukkaninsu yana godiya sunagodiya suka shiga mota suka tafi. Ba safiyanu bahar haisam yaji ya sake tausaya rayuwar hannasaboda ganin yadda gidansu yake. Gidan kasa ne anyi masa katanga da kara rufin azara abin dai abintausayi talauci dai tsagwaransa. Babu abinda zakadaga a gidan ka sayar dashi dari biyar komai ragaraga kaico!hannah na komawa makaranta tasalittafinta a gaba tahau karatu. Sune yanzu masushirin zana s.s.c.e don haka babu wasa sai karatu. kwance tashi su hannah sun fara jarabawarsu takarshe [s.s.c.e} saboda daman tuni sun gamatsarge karatu. Sai suka ga cin tuwo yafi jarabawarwuya sai kawai suka hau fede ta. Geography dinmalam haisam itace wacce suka yi ta karshe damisalin karfe hudu na yamma suka gama daman jakunkunansu su suna baki hall din da sukejarabawar suna fitowa sai kowacce ta dauki jakartasai tafiya daman kowacce ta kagu taje gida taga'yan gidansu basu taba irin wannna dadewa amakarantar ba har watanni bakwai a makaranta.Hatta hanna da bata so ayi hutu itama yanzu so taje gidq taga mahaifinta sai mafarkinsa take kullum takwanta barci. Hanna da kawayenta sun sha kukanrabuwa musamman ita da nusaiba sun saba sosaigashi zasu rabu. Gashi kuma babu waya a garinsuhanna balle su dinga gaisawa a waya. Rauda ma tarungume hanna tana kuka taji duk babu dadi yanzu da zasu rabu kuka wiwi juniors suke yi narabuwa da seniors dinsu zasu tafi su barsumusamman hanna basu ji dadin rabuwa da ita basaboda tayi musu mutunci samun shugabar dalibaiirin hanna sai an bincika. Ta koya musu abubuwana cikin kungiyoyinsu {club}na makarantar. A haka kowacce ta tafi gida kuka wiwi. Safiyanu ne yazo yadauki hanna ya kaita gidan uwar biyu. Yau haisamtun kafin su shiga jarabawa yazo yayi musu sallamaya koma gidansa ya rufe kansa kansa ko wajen daake bankwana bai zo ba saboda tsananin bakincikin rabuwa da yan ajinsa da yake matukar so. Gidan uwar biyu ma sai washe gari yaje ya samuhanna a can. Bayan sun gaisa ya ce da hannah''yau zaki tafi gida ko sai kin sake hutawa kamar satidaya anan sannan ki tafi ? Hannah tayi caraf tace''yaya haisam yau zan tafi na dade banga babanaba'' haisam yayi dariya ya ce'' wato ke yanzu kin bar kazaure kenan zaman kazaure sai mu ? Tayidariya tace'' sai ku ai mun daku wannan hutun harna daina sha'awar garin allah yaya haisam'' haisamya mike ya ce'' to ki shirya zanje nan makwabtasafiyanu yana ciki wajen abokansa ana wankemasa motar ana gamawa sai ku fito zan aiko yaro yayi kiranku sai mu kaiku tasha ku tafi. Da har cangarin zamu kaiku inyiwa baba godiya ince masagaki na dawo masa dake lafiya na cika alkawarishima ya cika to sai safiyanu ya ce kano zai tafi dakakarsa in anjima'' hanna tayi dariya tace'' kai yaahaisam ai babu komai yana gani na yasan lafiya na dawo lallai kuwa ka cika alkawari'' ya juyo yakalleta yace ''ko? Tayi murmushi tace'' E'' sannan yafita yana murmushi. Bayan fitarsa da dadewa sosaiyaro ya shigo ya ce wai uwar biyu da hanna su fitoinji su safiyanu suna kofar gidan dallatu'' daman ashirye suke tsaf sai hannah ta dorawa yaron jifgegiyar jakar kayanta. Jakunkuna uku ne. Yakaiya dawo ya dauki ta biyu sannan yazo ya dauki takarshe sannan suka fito uwar biyu ma da buhuntaa kanta, suka shiga mota sai tashar kazaure.Hannah ta hado kayanta kakaf na gidan uwar biyu.Katifa da bokiti kuwa taba uwar biyu kyauta. Kaya masu kyau atamfofi da shaddoji da yawa. Hanna tabawa uwar biyu kyauta da 'yarta halima. Dake kayatsadaddu leshi ma uku, shadda da
Chapter 23 · 0% Book details