← Book details Gangar Jikinsa Na Aura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 26

Sashe 14

Gangar Jikinsa Na Aura Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

tana dayadaga cikin wadanda suka fara dawowa makaranta tun karfe sha biyun rana, kafin yamma makarantata cika makil kowacce ta dawo tana tsoro sabodaprincipal tace duk wacce ta kara kwana dayabaza'a karbeta ba. yaya haisam baya nan kishin da rauda take yi dahannah ya kau yanzu suna zaune lafiya wasa dadariya, sai dai su dukkansu basa jin dadinmakarantar sosao saboda babu yayansu. Haka dukyan ajin uncle haisam basa jin dadin sabon classmaster dinsu saboda baya tarairayarsu kamar haisam. Kowacce bata manta da nasihohin da unclehaisam yayi musu ba akan suyi karatu sucijarabawa idan ba haka ba za'ayi musu repeating .Kowacce ta dage da karatu ba dare ba rana donhaka j.s.s 1a is the best class in f.g.g.c kazaureyawanci a wajen assembly malamai suna fadar haka principal tasa a tafa musu, tana kuma alfaharida su tana yabawa tsohon class master dinsuhaisam saboda tasan shi ya gyara ajin haka. Tanakuma nunawa sauran malamai dasuyi koyi dashidon ire iren su haisam a makarantar.Bayandawowar daliban makaranta da kamar wata guda. Ranar wata litinin da safe ana assembly sai kuwaprincipal tayi musu albishir da cewa.kwararrenmalamin nan uncle haisam ya dawo makarantar amatsayin permanent teacher. Tasa wani malami yaleka waje ya shigo da haisam saboda a waje la labekada su ganshi suki tsayawa ayi assembly suyi taife ife don haka ya tsaya daga waje. Malam haisam na shigowa dalibai gaba dayansu yara da manyasuka hau ihu da tafi murna kuwa ba'a cewa komaimusamman a wajen hanna. Wai! Yau da za'a budezucoyar hannah aga irin farin cikin da yake cikinzuciyarta da abun da yawa. Dakyar dai dalibansuka dan tsagaita da ihu aka karasa assembly kowacce ta tafi ajinta. Yan ajin su rauda kuwa hadabaki suka yi suka yi kungiya suka nufi ofishinprincipal dauke da manya manyan takardu sunrubuta kamar haka '' we want our former classmaster uncle haisam back.'' waisu zanga zanganlumana suke yi principal da sauran malamai suka sha dariya sannan ta basu amsat cewa za'a dawoda haisam dinsu, su koma aji. Sannan suka tafi sunamurna. Haisam ya dawo yaci gaba da rike ragamarshugabancin ajinsa j.s.s. 1A. Hutu yana zuwa karshe jarabawa na karatowahaisam naci gaba da yiw dalibai nasiha dasu dageda karatu musamman ma hannah yana ci gaba danunnuna mata duk abunda bata gane ba. Ba laifihannah tana sake kokartawa fiye da waccan termdin. Ta fara gane ayyukan makarantar sosai tana kuma gane turanci tana yi kuma. Wannan termdinma kamar wancan sunyi jarabawa sun gamasannan malamai sun yi kokarin sun kammala fitarda sakamako. Haisam ya tara yan ajinsa ana gobehutu ya bawa kowacce sakamakon jarabawarta.Wannan ma kamar waccan bata sake zani ba rauda shitu muktar itace tazo ta farko. Nusaiba ta biyu,pamella matin benin ta uku. Hannah ce dai ta samici gaba maimakon tazo ta goma data zo wancankaron yanzu sai tazo na takwas.Hannah tayi murnahaisam har ya fita murna ganin ba kudin banzayake kashewa ba, da bata lokacinsa a banza ba. Kamar wancan hutun, ranar hutu principal ta yiwadalibai assembly, hutunne bashi da yawa sosaikwana ashirin da takwas ne kawai zasu yi a gida.Amma wannan karan direban gidansu rauda yazodaukar rauda sai haisam ya ce ta tafi shima dagagidansu za'a aiko da direbansa yazo ya daukeshi. Bayan tafiyar rauda babu dadewa sai ga dalleliyarmotar haisam kirar jeep da mahaifinsa ya bashibayan ya gama bautar kasa, muntari sunan direbanhaisam, yazo ya duka ya gaishe da haisam, haisamya nuna masa jakar hannah ya ce ya dauka ya sakaa but. Bayan ya saka hannah ta shiga baya, haisam na gaba direba mutari yana tukawa suka fita dagamakarantar. Haisam na nunawa mutari hanya hargidan uwar biyu kamar waccan lokacin suka iskeuwar biyu a shirye tsaf. Ta fito daga gida bayan sungaisa, haisam yace da uwar biyu su dauki jakarkayan su shifa cikin gida a ajiye, kaya kala biyu kawai za'a bawa hannah da silifas faya amma duksauran a ajiye da litattafanta. Da yake safiyanu yabashi labarin duk yadda uwat biyu ta gaya masaabunda ya faru da kayan hannah. mutari direba ne ya taya su da shiga da kayan cikingida. Uwar biyu ta zaba ma hannah kayan da zatasaka ta cire uniform da kambas aka bata silifas dawani kala daya a leda wanda zata tafi dashi. Bayansun fito daga gida sai suka shiga mota suka tafi,basu tsaya a ko'ina ba sai a tasha. Wannan karan ma har bakin mota haisam ya raka su hannah yadauki kudi mai yawa ya bawa uwar biyu yacr suyikudin mota na zuwa can tayin na dawowarta,sannan a ciki taba mahaifin hannah na kashewa taajiye wanda zata je ta daukota idan hutu ya kar e.Yayi wa hannah nasihohi ya bata hakuri game da halin da take ciki a gidansu.Daga karshe yayi musu fatan allah ya sauke sulafiya. Ya juya ya tafi uwar biyu na tayi masa godiyadashi masa albarka hannah na rusa kuka
Chapter 14 · 0% Book details