Sashe 12
Gangar Jikinsa Na Aura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kwana arba'in da biyu aka basu da zararhutu yana karewa zaki zo ki dauke ta inji ni zakice.Ki san dai kalaman da zaki gaya masa na kwantarda hankali kada ya hanata dawowa kinsantsofaffin nan namu, kice ke uwar dakin tace a wajenki take a makaranta na hadaku, kice inagaisheshi da kyau. Uwar biyu tayi godaya tashialbarka kamar ita aka bawa kudin ko jikarta. Yadauko wasu kudin ya mikawa uwar biyu yace'' kisayawa hannah sarka da dan kunne na jiyal maikyau ki bata'' uwar biyu tace'' kai kudin ai yayi yawa malam haisam duk a cikin wannan ya isa nayimata siyayyar'' ya ce ''ba komai na gode uwar biyuallah ya kiyaye hanya'' tace amin malam mune dagodiya'' ya zagayo jikin wundon da hannah kezaune tayi tagumi ta langwabar da kai a jikinwundon mota jawaye ne yake sulalowa daga idanuwanta daya bayan daya. Haisam ya kalletayayin da yaji kamar zuciyarsa zata fashe dontsananin tausayinta , yayi karfin hali yace'' hannahkukan meye kike don kawai anyi hutu zaki tafigida ? Ai hutu na karewa uwar biyu zata je tadaukoki kinji ko ? Zan zo inyi miki siyayya na mayar dake makaranta, yanxu idan kika je gida kinakuka baba zaice wahala kike sha a makarantar yace ba zaki dawo ba. Amma ki nunawa babamakarantar da dadi ga ladabi da biyayyar da akekoya muku ga karatu da abinci a wadace shi kansazaice ki dawo, kinji ko ? Hannah ta gyada kai ta fara share hawayen idonta. Yace gaba da cewa'' kiyihakuri da abun da iya abu take yi miki hutu nakarewa uwar biyu zata zo ta daukeki ta kawo kimakaranta. Sannan kullum ki rika zuwamakarantar islamiyya kina kuma duba litattafankina makarantar boko don karki manta karatu kinji. Allah ya kiyaye hanya hannah. Ya juya ya tafi,muryarta yaji ta rushe da kuka, ya juyo ya tsaya cakyana kallonta sai ya rasa me ma zai ce mata sai yajuya ya tafi da sauri. Yana mai tsananin damuwa datakaici.kukan zuci kawai yake. Ba tare da ya cewa suauwal komai ba, ya ja mota ya fara tukawa. Canrauda ta nisa tace'' yaya haisam daman hannahfulanin daura ne, ko ba daura zasu ba ? Haisam yayidan murmushi kawai. Auwal yace'' haisam ka cikashige shige ina ka samu wannan buzuwar har da kakarta kuma? Haisam yacce'' wai shige shige ni dakai za'a san me shige shige naga daga zuwa harkasan su naja'at suleman ko banga sanda takebaka adiredhinta ba balle ni dana shekara amakarantar'' auwal yace to ya isa ga wannanzabiyar a baya ta bude kunnuwa tana daukar rahoto'' haka dai har suka isa kano jifa jifa haisamyake magana babu abunda yake tunawa sai halinda hannah zata kasance a gidansu. Zuciyarsa cikeda tausayinta kulle kullen yaya zaiyi yaci gaba dataimakonta yake gashi kuma ya bar makarantar,har suka isa kano . A nasarawa g.r,a suleman cresent gidan su haisam yake, suka shiga cikinkatafaren get din gidan . Bayan auwal da rauda sunshiga sun gaisa da hajiyar haisam sai suka yi mususallama suka nufi suma nasu gidan da yake lamidocresent basu da nisa sosai. Alhaji shitu mukhtar sunan mahaifinsu rauda,mahaifiyarsu kuma hajiya jamila sunanta alh. Shitumuktar haifafen garin kano ne, dan unguwankabara ne tare sukayi firamare da sakandire damahaifin haisam abokaine tun suna yara. Haj.Jamila kuwa mahaifiyar su rauda mutumiyar chadi ce ya aureta. Allah ya albarkacesu da 'ya'ya uku,yaya auwal shine wanda ya kammala karatunlikitansa a america yanzu cikakken likita ne. Sai antiramla wanda ta gama sakandirenta a wannanshekaran tana jiran sakamakon jarabawarta tawuce jami'a bayan an cancara bikinta da angonta haisam, saita fara karatu a gidanta, sai yar autarsurauda wacce yanxu take ajin farko a sakandire.Tsantsar yan boko ne yaya uku sun ishesurayuwar duniya suna basu cikakkiyar kulawa datsantsarso da kauna. Allaha yayi musu arziki maiyawa don haka a daula suke ta ko ina hutu, ba su fi shekara biyu da dawowa nijeriya ba kasancewaralh. Shitu muktar yana aiki a embassy, shinejakadan nigeria a america {ambassador} don hakaduk a can suka yi karatunsu har mahaifiyarsu haj.Jamila acan tayi digirinta.al'amarin hannah da uwar biyu kuwa, bayan tafiyar haisam uwar biyu tayi sauri ta sauka daga motartaje ta yiwa hannah siyayyar kamar yadda malamhaisam ya umarceta da tayi. Ta dawo cikin mota dasauri ta iske motar dai bata cikaba , bayan mota tacika suka kama hanyar tafiya. A hanya uwar biyu taci gaba da lallashin hannah tana bata baki dakyar tayi shiru da kukan da take yi. Ta dade daman tanaso taji labarin hannah da dangantakarta da malamhaisam, saboda tsananin kulawar data ga yana yimata, cikin wayo da dubara irin na manya uwarbiyu ta dinga bugun cikin hannah tana son tajilabarina. Abunka da yarinya kuma mai neman agaji da take yi ta ko ina hannah ta fayya cewa uwarbiyu komai daga biri har wutsiya. Uwar biyu tatausaya hannah ta sake jinjinawa malam haisambisa jihadin da yayi saboda allah na taimakonhannah. A garin babban mutum suka sauka aka saukemusu jakarsu . Tun daga sauka hannah ta farafaduwar gaba tazo garin da bawa ya fita jin dadi.Uwar biyu ta lura da hakan sai tayi ta bata baki tanakwantar mata da hankalinta. Kawayen hannahmaza da mata yan garin suka baibayeta suna kallonta wasu kuma suna shishshige mata harrububin yi mata magana su ke. Masu daukar matajaka suka dauka suka dunguma zuwa gidan suhannah. Samarin garin sai kallon hannah suke ganisuke kamar ba hannar da bace da suka sani. Tayijawur da ita tsaf tsaf. Babban mamakin kambas din da ta dana a kafarta suke kallo wasu na cewatakalmin yan ball tasa, wasu na cewa na faretinsojoji ne. Mamaki ya ishesu yadda akayi hannah tazama haka kamar baturiya a wata guda nan danan, kyau na zuba duka cikar garin da batsewarsababu mai kyawun hanne da gogewarta. Nanfa samari kowa ya hau cewa gaskiya tawace wannan.Wancan na cewa na rigaka. Kawayenta da yawasun kudiri niyyar suma sai sun tuburewa iyayensuan kaisu makarantar kwana irin ta hannah donsuma su goge suyi jawur haka. Kafin hanne takarasa gida labari ya kai cikin gidansu ance ga hanne nan zuwa ta zama fara kal kamar baturiya itada wata tsohuwa. Farin ciki ya rufe mahaifinta yaiwuf ya fito kofar gida ya tsaya yana murna yanajiran isowar hannensa(yar boko). Budar bakin iyaabu kuwa sai cewa tayi watakila ciki aka yi mata amakarantar tayi haske don hanne ba fara ba ce kal. Surutai dai na hassada da bakin ciki barkatai tadinga yi.Hanne na doso kofar gida ta hango mahaifintasai su duka murna ta lullubesu. Hannah ta karisa dasauri taje ta rungumeshi kamar yadda taga sunusaiba suna yima mahaifansu sai hawaye suke itada mahaifinta. Iya abu a tsakar gida ita da yayantababu wanda ya amsawa uwar biyu sallamarta da tayi, sai malam habu yace shigo kawai ai ba zasuamsa muki ba'' ya shiga daki ya dauko tabarma dasauri ya shimafida mata ta zauna a sanyaye cike damamaki irin wannan tsana da ake yiwa wannan yarkaramar yarinya wanda ma yake sonta an tsaneshi.Hannah taje gaban iya abu ta durkusa ta gaisheta ko ta amsa ta juya ta gaishe da yayyenta 'ya'yan iyaabu kenan suma suka kwata abunda mahaifiyarsutayi. uwar biyu ta rike baki tace ''oh ikon allah bayinallah me yayi zafi hannah nawa take ? Don allahkuyi mata yar fara'a mana ko taji dan sanyi yanzuko dokinta bakwa yi kusan wata biyu bata nan, aidarajar sabon idon ni bakuwa kwa raga mata harin tafi'' suka yo ca akan uwar biyu uwar biyu nayi yayan nayi, ta mike tsaye ta juya ta kalli hannahwacce ta kame a jikin katanga tana makyarkyatahawaye ne ke zuba daga idanuwanta tasan yauduka da zagi allah ne kadai yasan iyakarsa da zatasha. Hawaye ya kecewa uwar biyu tace'' hannah yihakuri wuya bata kisa ko anki ko anso gidan ubanki ne duk inda kika je sai kinzo gidan dole,''iya abu tace'' gidan uban nata ya gagareta zamaidan naso ba. Malam habu shima yayi jugum yakasa magana tashin hankali ya isheshi sabodayana tausayin hannah yasan wahala zasu ci gabada linka mata ganin allah ya rufa mata asiri tayi kyau, uwar biyu ta fita malam habu ya bita hannahma ta bisu da sauri, uwar biyu tasa gefen gyale tashare hawaye tace'' allah yana nan, malam ni yaraikece. Malam haisam malamin daya karbeta ahannunka din nan. Malam habu ya katseta yace ''ehna gane kiyi mana godiya da kyau da kyau na gode madalla. Tasa hannu a dan tofi ta dauko kudimai dan afki ta bawa malam habu'' inji malamhaisam ya ce a bashi nasa ne na kashin kansa banamakarantar hannah bane. Da zarar hutu ya kare itada kanta zata zo ta dauketa, malam habu yayi shiruyana sauraron uwar biyu sai girgiza kai yake kawai yana mamakin wannan tara ta arziki da haisamyake yi musu yana fadin ashe akwai masu halinsahabba a duniyar nan masu kyautar da dukiyarsuga mabukata irin malam haisam. Malam habu yadago ya kalli uwar biyu yace'' kema daya aikokikika rike amana allah ya saka miki da gidan aljannah dashi da yake mana hidima allah ya bashida mai yi masa haka munji dadi mun gode. Ni inanan wata rana na gaza barci ina tunanin ko yayayar baba, kome take ci a makarabntar na bartababu abinci? Ashe tana cam ta fini koshi, kalliyadda tayi bul bul ah alhamdulillah. Maigari ya aiko da garin kwaki kwano biyu da suga rabin kwanosai kudin motar zuwa kazaure ya ce in kai matamakaranta wallahi matar nan tawa data ga garinnan da kudin mota sai ta sulalo ina bacci ta sacekudin motar ta tilla ledar garin ya dinga tsiyayewa akasa, da naje na shaidawa mai gari ba kiga cin mutuncin da suka yimin ba wai daman talauci yaisheni na sami kayan gwamnati ina wadaka dashi,su babu ruwansu ya dai ya ta ce in barta yunwar takasheta. Nayi kuka da hawaye nazo na zauna nahakura sai addu'a na dinga aikamata daga na allahya hadata da mai bata. Allah ya amsa addu.ata gashi bamu girbe amfanin gona ba shine yasa kotaro nakan tashi babu a aljihuna. Uwar biyu tace,kaico haka kake rayuwa ta malam ? To ni daishawarar dazan baka dan allah dan annabi(S.A.W)duk runtsi duk wuya ka toshe kunnankakome za'ace game da karatun hannah karka cire ta daga makaranta. Babu sisinka. Ba kai zaka dauketaba. Bakai zaka mayar da ita va nice zan dingakawota ina zuwa ina daukarta sai dai ka bata izinikarka hanata saboda karatu ne kawai zai farfadoda hannah ta sami