Sashe 21
Gangar Jikinsa Na Aura Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
a tashe'' hannah tayi sauri tace yaya haisam da yamma zamu tafi ina soinje gidajen kawayena a nan cikin gari. Yayimurmushi ya ce'' wato akuyar daure ta samu sake,su hannah an iya yawo ko? Su duka suka yi dariyasannan ya fita. Damisalin karfe biyar uwar biyu dahannah suka isa babban mutum , suka je suka iske gida a hargitse anyi tashin hankali. Malam habumahaifin hannah kuka wiwi. Cikin rikice da rudanihannah ta tambaya meya faru babanta yake kuka.Iya abu ta tuntsire da dariya tayi buda da shewatace'' tambayi ubanki. Karshen tuka tiki tik yauallah ya nuna mana gaskiya'' hankalin hannah da uwar biyu ya sake tashi sosai, suna so suji me iyaabu take nufi da wannan habaici nata. Malam habuya sharbe hawaye da babbar riga ya ce''muje zaurein fada muku abunda ya faru'' da yake damantsakar gida suka iske su. Suka je zaure sukazazzauna malamhabu ya nisa gami da langabar dakai yace'' idan ka haifa dole a jawo maka, damanance dan kuka shi ke jawa uwarsa zagi. Uwar biyu dahannah su dai sun kagu suji abunda ke faruwayace'' yanzun nan babu dadewa watakila kunhadu da wata bakar katuwar mota a hanyar shigowa garin nan wata fitsararriyar yarinya cetazo ta cimun mutunci a kofar gidan nan har ta taramun mutane. Hannah tace''wacece baba? Cikinrudani da fargaba ta tanbaya. Ya ce'' farko da tazosai ta tsaya ta karemun kallo a wulakance sannantace naji kunya wallahi yasa naji kunya. Dama yarinyar yar talakawa ce yake bata mun lokaciakanta to baba bari in fada maka ka jawa yarkahanna kunne ta kiyayi mijina idan ba haka ba nizan zamo ajalinta domin zan iya kashe duk yarinyarda zata rabani da haisam abun sona. Kuma ka cireyarka daga makarantar nan domin idan bata bar makarantar va haisam ba zai bar makarantar ba yarabu da ita. Muddin hanna ta sake komawamakarantar to kuwa har makarantar zan bita inzartar da abun da na yi niyya. Ba tana takama itakyakykyawa bace to zan kwara mata wani abuafuskarta {acid}fuskar ta sale ta kwakwkwabe har makarantar zan tarar da ita in yaso sai inga fuskarda zai sota. Don soyayya hannah take yi da mijinava karatu ba. Har sakamakon jarabawar kanwatayake dauka ya bata tazo ta daya a ajinsu. To na gajiwannan shine lokaci na karshe dana bawa hannahidan taki ji ta koma makarantar to wallahi ta kuka da kanta'' malam habu ya sharbe hawaye yaci gabada cewa'' da wata kanwarta yar makaranta tanasanye da kayan makaranta irin naki yar baba itamatana taya ta suka yimin tas, iya abu na ihu tanadariya tana cewa daman ta sani ba tun yau bahanne karuwanci aka kaita tayi ba makaranta ba yanzu gari duk ya dauka maganar ake yi don agaban mutane aka yi haka. Tace hannah taci sa'ada bam sameta ba da sai ta faffalla miki mari sannansuka shiga mota suka tafi. Hannah bata iya cewakomai ba sai ta sunkuyar da kai kasa tana kukamalam habu ma kukan yake uwar biyu ta matse hawaye tace'' kuyi shiru, ku daina kuka wannanduk abune na shirme da karya ita wannan yarinyardata zo ina tunanin matar da malam haisam zai aurace take ganin son hanna yake alhali kowa yasanhaisam a matsayin yaya koma ince uba yake awajen hanna tun tana karama fa inah, ai zancen so ma bai taso ba. Hannah karatu take a makarantababu wata soyayya daga wannan hutun ma bazasu sake dawowa har sai sun gama makarantar makwata kwata saura wata bakwai su gama. malam habu ya zabura yace'' wacce komawa aihanne tazo kenan baza ta koma ba ina wanizancen saura wata bakwai hanne ta gama aikosaura kwana bakwai ne hanne ta gama karatuntabayan a gaban mutane aka ce ba karatu take yi amakarantar soyayya take yi sannan in bar yata ta koma ai sai a dinga cewa tana can tana iskanci harwata bakwai ba ta komo gida hutu ba, ni daiabunda zance muku uwar biyu ke da wannan yarohaisam allah yayi muku albarka amma hanna bazata sake koma wa ba karatun ya isa haka dukkawayenta harma da kannanta duk sunyi aure gara itama in hadata da wani a dangi tayi aurentabaki alaikum kafin a kone mata fuska. Damanabunda muke ji a redio gaskiya ne ace an fesawawani ko wata wani ruwa a fuska ya kwakwkwabogaske ne to ba zai faru akan hanne ba. Karatun datayi na baya ya isa nagode madalla'' cikin rudewa uwar biyu tace'' haba malam habu yaya zaka yimana haka ? Baka kyauta masa ba yarinyar nanduk zance take haisam ba zai barta taje gurinhanna ba balle tayi mata wani abu. Bama a barinkowa yaga dalibai in ba ranar bisitin ba dokarmakarantar ce'' malam habu ya mike ya shiga gida yana cewa'' nifa na gama maganata uwar biyu kiyihakuri ki bar maganan komawar hannemakaranta. Ai ko karan hauka ya cije ni ba zan baryata taje inda za'a halakata ba ina hanne ina kishida wadannan gogaggun yan burnin masu kudi.Tunda tana ganin mijinta son hanne yake ai sai a hakura da taimakon na baya ma allah ya saka'' yashige ya bar hannah tana matse hawayen dakeidanuwanta da wani farin hankici dake hannuntatace uwar biyu'' kyale shi ya tsorata ne kafin hutuya kare zai yadda idan na wayar masa dakai ahankali na lallabashi sai dai idan hutu ya rage sati guda kizo don muji mai zai ce in yaki yadda sai daiyaya haisam yazo ko kuma ya turo principal idankuma yaki yarda na shiga uku karshen karatunaya zo. Hannah ta rushe da kuka, uwar biyu tace ''yadda za'ayi shine haisam zan turo yazo garin nanmahaifinki ya kalli kwayar idonsa ya ce ya hanaki ki koma makaranta, haisam zaizo da kansa. A hakahannah da uwar biyu suka yi sallama. Hanna tayitayi da uwar biyu ta shigo cikin gida ta huta sannanta tafi uwar biyu tace baza ta shigo ba ina zata iyashigowa wajen iya abu masifaffiyar matar da zataiya kashe mutum ma don rashin imani. Hannah ta raka ta har tasha ta shiga mota sannan hanna tadawo gida.