Sashe 20
Gangar Jikinsa Na Aura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a kanta zata je kogi deboruwa. Abdul ya sakarwa talatu wani lallausanmurmushi na so da kauna cikin sassanyar muryahannah(talatu) tace''abdul ba dai tafiya ba'' ya ce''tafiya zanyi talatu nazo ne daman inyi miki sallama'' sai kawai kwaryar dake kan talatu ta fado kasa dangigicewa. Ta rushe da kuka. Abdul ya gigice yaajiye jakar dake hannunsa, hannah ta fara karantotakardar da haisam ya rubuta musu tace'' abdulkayi min alkawari ba zaka yi aure ba a cam har saika dawo ka aureni karka je can ka sami yar larabawa ka aura ni ka manta dani'' haisam yasatafi sai duk aka dau tafi a hall din. Haisam yacekunyi kokari wajen yayi kyau kema maryam tijjaniki dage ki bata amsa dan allah banda dariyar nanda kika saba'' maryam tijjani tace to bazan yi dariyaba'' ta daga ido ta kalli hannah(talatu) wani kallom soyayya da hannah take, tayi wani narai narai daidanuwanta kai sai kace a gaban saurayinta nagaske take. Sai dariya ta kwacewa maryam tijjanisai kowa yasa dariya. Haisam yace ''maryamgaskiya kina bata mana lokaci kullum muka zodariya kawai kike yi saura kwana uku fa mu fita excusion idan kinsan ba zaki iya ba nasawata''maryam tace''uncle allah hannah ce take sanidariya baka ga kallon fa take yimin bafa kamar tasami saurayinta da gaske sai kashe idotake''haisam yayi dariya yace''tsabar tafiki iyaacting kenan. Shi daman wasan kwaikwayo ana son duk abunda aka baka kayi kokari ka nunakamar da gaske ne. wajen kuka kayi kuka, wajen murnakayi murna . Kema kiyi mata kallo kamar kecesaurayin kin hadu da budurwar da kika fi so a duniya. Wannan yana nuna kenan hannah ta iyaacting sosai kamar da gaske. Kowa ya hau dariyaana yiwa maryam tsiya ''kema ki yi mata kallonsoyayyar mana ko baki iya bane? Haisam ya tashi yaje ya karbi takardar hannunmaryam ya ce''koma gefe ki dinga kallon yaddazamu yi sosai don ki koya'' ya ce da hannah''tokara karanto naki''babu kunya hannah ta narkarda idanuwanta ta kashe murya lallausa ta dubihaisam kallo ido cikin ido''abdul kayi min alkawarin ba zaka yi aure ba a can har sai ka dawo ka aurenikar kaje can ka sami yar larabawa ka aura ni kamanta dani anan'' haisam ma ya narairaice ido yakurawa hannah ido kawai wannan kallo da haisamyake yiwa hannah ya sosa mata wani waje axuciyarta, ya ce''talatu ba zan yi aure ba, kuma ba zan manta dake ba. Ko a ina nake, ko da gangarjikina bata tare dake ruhina yana tare da ke.,soyayya baiwa ce, hannah kina raina a kodayaushe . Ina sonki hanna'' taji gabanta ya fadi donjin yaune rana ta farko da hannah tasan ma'anarwakar nan da take yi tayi shiru tana tunani tana kallon yaya haisam ta san tabbas wannan wajen acikin wakar nan da take yi masa ya dauko kamardaga sama taji yaya haisam ya ci gaba da cewa''inasonki ina sonki hannah! Ba zan manta dake bakina raina har abada'' wannan karon bakarantowa ya ke a takarda ba kuma ba talati yace ba, hannah sai ta fara ja da baya taba tafiya ahankali tasa hannu ta rufe idanuwanta tanamurmushi. Kunya ta ka mata gaba daya yan kallonsun zubo mata ido suna kallon sarautar allah, domin kowa ya san wannan kallon kadai da sukeyiwa junan su yafi karfin gwaji balle kalaman da yake fita daga bakin haisam ba a jikin takardaryake ba. Sai yaja wani dogon numfashi ya juya yakalli sauran dalibai yace'' kuje ma karasa gwajin dadaddare'' ya fita ya nufi gidansa. Dalibai su ka firfitosuna gulmammaki'' wannan anya hannah da unclehaisam ba soyayya suke yi ba, ke kinga kallon da suke yiwa junansu uncle haisam kamar yarungumeta fa. Haka suka shiga dakunansukowacce ta nufi bangaranta. Rauda ta sami hannah a kwance akan gadonta tadora filo a kanta babu abinda take tunanowa saiidanuwan yaya haisam sai kuma tsananin mamakinyadda ya rike baitukan wakar nan da take yi masatun tana aji daya. Tace a ranta ashe ma'anar wakarkenan banda yarinta nake kai kaicewa nake rera masa ko da gangar jikina bata tare dakai ruhinayana tare da kai. Har nusaiba take cewa hannahmeye ruhi nace ina jin larabcine ashe ni ban sanhausa ba ce tsaba a lokacin . Ruhina , ruhina'' tsakitaji anyi a kanta ta bude ido sai taga raudaamurtuke. Tayi furgigit ta tashi zaune tace'' rauda har kun dawo? Rauda ta kaste ta tace''haka zaki cemana har mun dawo da acan zamu kwana? Komuma son maso wani muke yi da zamu bishigidansa? Yaya haisam dai yana da wacce yake sokuma an gama magana gara kowacce ta komakauyenta ta sami wani bakauyen ta aura amma haisam sai ramla. Hannah tace'' rauda me ya faru ,wani abun akayi ? Nusaiba tace'' ke rauda meyehaka wasan kwaikwayo ne fa kowa yasan gwajine ba gaske bane. Wai ke rauda me yasa bakya sona zauna lafiya ne ? Rauda tayi tsaki ta fice tana cewa'' duk gulmace gulmacen da ake ina sane. Dan iskan kauye yafi na burni iya iskanci da rashinmutunci ai. Hannah ta fashe da kuka, tayi kuka kamar ranta zaifita. Nusaiba na lallashinta da kyar hanna tayi shirusuka je suka yi alwalar magaruba. Bayan sallarisha'i sunci abinci karfe takwas dai dai sai suka jesuka kora dalibai kowacce ta fita ajinsu don yinprep din dare, uncle haisam ya fito daga gidansa takwas da rabi yazo ya kirawo yan hausa club donsuzo su karasa gwajin wasan kwaikwayon da sukeyi. Ta bayan wundo ya hango rauda tsaye akanbencin hannah tana ta gurza mata rashin mutuncihar cewa take da ba'asam asalin balbela ba sai tacemadina ne garinsu. Yaga hanna zaune tayi shiru tana hawaye, ran nusaiba ya baci ta taso tashigarwa hannah kamar zasu daku da rauda. Saihaisam ya leko ta wundo yayi musu tsawa ya ce sufito waje yana son ganinsu. suna zuwa gabansa kallo daya suka yi masa sukasan babu wasa yau a murtike yake kasancewarsunsan bacin ransa babu kyau sai kowacce ta fararawar jiki. Ya daka tsawa yace kowacce tayi kneeldown bayan sun yi ne ya tambayi nusaiba me yafaru. Nusaiba ta zaiyana masa dukkan abunda ya faru tsakanin rauda da hannah tun daga yammahar na yanzu ya juya ya kallo rauda yace'' raudahakane ? Ta gyada kai gami da tabe baki tace''haka ne kuma gaskiya na fada'' haisam ya fusataya kaiwa rauda mari tayi sauri ta kwanta a kasa baisameta ba. Tace' yaya haisam yau ni zaka mara akan hannah? Haisa yayi shiru hannayensa a cikinaljihu kansa a sunkuye a kasa. Can ya dago yace danusaiba ta tashi ta shiga aji. Ya dubi rauda wacce kedurkushe a kan gwiwarta a gabansa rauda tarushe da kuka. Haisam yace'' rauda tun ba yau ba,tun kuna aji daya na lura kin kafawa hanna karan zuka a makarantar nan. Yanzu kece kadai kikarage a cikin masu takurawa hanna zan iya daukankowanne irin mataki a kanki muddin baki fitaharkar hannah ba ki kiyae, idan kuma kin ki ni zanfiki farin ciki don zaki ga abunda zan zartar a kanki.Ko amratu 'yar shekara bakwai zan iya.hukuntata muddin ta nemi takurawa hannawannan alkawari nayi wa allah kuma sai na cika shidon hanna amana ce a wajena'' kamar a mafarkirauda take jin kalaman yaya haisam, tana fada aranta lallai abun nasa babbane da gaske yake'' daga karshe ya ce ta shiga aji tana sharbar kuka tamike a fusace ta shiga aji. Ya shigo shima ajin yakalli hannah wacce ido yayi mata jawur don kukayace hanna ki kira sauran yan hausa club ku tahohall ku sameni mu karasa rahazal din. Cikin ladabihannah ta amsa masa. Ya fita ya nufi hall. Hannah cewa'' rauda muje hall yaya haisam na kira'' tadago ta harari hannah tace'' bazan je ba kuma nafita daga club din ko za'a sani dole ne? Hanna zatace wani abu nusaiba taja hannunta tace ''kyaletamu tafi mu kira sauran. Hutu ya kusa karewa har ana shirye shiryen farafirst term examination. Kowacce karatu takehaikan, sunyi jarabawa an basu sakamako kafinranar hutu. Hannah ce tazo ta daya a ajinsuwannan karon, rauda ta biyu nusaiba ta uku ranarhutu bayan anyi assembly hutu da wur wuri kafin kowa ya fara tafiya haisam yazo ya sami hanna,rauda nusaiba da wasu kawayensu a zazzaune akan barandar hall suna ta hira. Bayan sun gaisheda shi sai ya ce'' hannah taso ga safiyanu yazodaukarki, idan muka saukeki a gidan uwar biyuzamu wuce dashi dan musa can jahar katsina acan yake neman aure zamu kai kayan gaisuwarsurukai'' su duka suka kyalkyale da dariya. Hannahtace ''oh yaya safiyanu daman aure zai yi ko ya fadamana sunanta ranar nida nusaiba muka ga hotontaa motarsa muka ce budurwarsa ce ya ce wai shi babudurwarsa bace'' nusaiba tace'' haka ne kuwa a bayan hoton an rubuta dan musa har nake cewadan musa kuma sunan mace dan musa ya ce ehhaka sunanta. haisam yayi dariya , sannan ya juya ya kallo raudatasha kunu ta kawar da kai gefe daman tundaakayi wannan abun bata cika yiwa hannahmagana musamman idan taga haisam da hannah.Ga uwa uba hannah ta kwace mata position tazo tadaya , sai take jin haushin kamar ta kashe hannah. Haisam ya ce'' rauda ni ba kano zanje ba sai mundawo daga danmusa don gida ma nace kada aturomun da mota auwal zaizo daukarki ko direba?Tace '' sai dai direba yaya auwal yanamaiduguri''yace''oh haka ne fa, to ki gaishe dasuhajiya sai wahen jibi zanzo kanon. Idan muka tafi yau ba damar muyi tafiyar dare dole mu kwanasannan washe gari mu dawo kazaure wata kila inkwana a cikin gari jibi muje kanon da safiyanu .Rauda tace zasu ji . Allah ya kiyaye hanya. Hannahta kira wasu juniors suka dauki jakunkunanta sukazuba mata a mota. Tayi wa kawayenta sallama tana zolayarsu su tana cewa yau itace farkon tafiya dukmakarantarn ta barsu su yan kwantai ne. Rauda tatabe baki tace'' yanxu wata kila har kowa ya isagida ke baki isa gida ba, saboda hanyar garinkukwalta ce sambel ba kasa ba'' hannah da nusaibane kawai suka gane rauda bakar magana ta fada, wato hannah bakauyiya cekenan take nufi saihannah tayi murmushi kawai ta tafi ta shiga motatana dagawa nusaiba hannu har suka fita get . a gidan uwar biyu su haisam suka sauke hanna ,haisam ya shiga cikin gidan bayan ya bawa uwarbiyu kudaden motarsu da wanda zasu kaiwamahaifin hannah suka yi godiya yayi musu sallamaya juya ta tafi har yaje kofar fita ya juyo yace '' koyanzu zaku tafi mu ajiyeku