← Book details Gangar Jikinsa Na Aura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 26

Sashe 2

Gangar Jikinsa Na Aura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

riga a cukurkude, zanin daga kasa ya nadekamar annade tabarma. Takalmin kafarta harda leda tadaure waye zaice daliba ce. Daya ya ce "Danmarar data ci kai kacedandali zata, ta daure kugu tamau. Ina jin ma basu san anadinkakayan makaranta ba (Uniform) balle takalmikambas da safa.Hanne tayi ajiyar zuciya ta hadiye yawun da ya cikamata bakinta tayi shiru, kanta a sunkuye a kasa.Tace a ranta "Lallai ko nafi maye kwakwa dole nahakura damakarantar nan harda kayan makaranta akedinkawa. Wayezai dinka min? Ta sake kallon kayan jikinta tace aranta "Kayan sallar tawa shine suke cewa duk a cukurkude? Niina ganinnayi ado kowa a garinmu da muka zo wucewayana cewaHanne yau kuma ina zaki kika ci ado haka? Su anankazan- kazan suke ganina ashe, dole mu koma gida asheban rabu dawahalar Iya Abu ba. Kuka ya sake kece mata hardashessheka. Malam Habu ya kalleta fuskarsa cike dadamuwa ya ce "Yi shiru 'yar Baba bari zamu san yadda zamuyi mukoma gida. Ni yanzu ke nake ji gashi kudin da yarage mun aaljihuna saura Naira ashirin kacal. Da niyyatainnakai ki makarantar in zan koma gida sai in hau mota daganan zuwatashar Kazaure daga can kuma sai in kama hanyada kafa harBabban- mutum (garinsu) idan dare yayi mun insami waje in kwanta washe gari na tashi naci gaba. Har dai inkarasa kokwana nawa zanyi a hanya. To yanzu ba zai yuwuba tundagaki, sai dai kawai mu shiga mota muje tasharKazauren, ko a bakin tashar sai in siyar da akwatin nan ko katifarkoma dukamu samu muyi kudin motar komawa gida. Hanne tazabura tace "Ka siyar da akwati da katifa fa kace? Kansila aisai yasa a kamaka, cewa yayi fa gwamnati ce ta siya ta bani.MalamHabu yayi kasake yana tunani na wani lokaci maitsawo can yace "To laifin waye? Shi kansila da maigari basu sanda kudi za'a zo makarantar ba, babu wanda ya bamu kosisinsa,kansila kullum yana min alkawarin zai je ya karbokudin da zaayi miki siyayya da kayan makaranta da komai dakomai, har cewa yayi motar gwamnati ce zata zo ta kawoki..Daga karshe ya zo ya fara hanya tun dagagwangwarmarakwatin nan da katifa da bokiti babu abunda yakara kawowa.Bansan wacce shawara suka yi da maigari ba kumadaga karshe suka ce inzo in kawoki haka za'a aiko mikikayayyakindaga baya. To yanzu gashi takardar makarantar cebabu aka yimana korar kare ina ga idan muka shiga ciki aka cemu kawo kudi, muka ce babu ai sai a rakomu da duka. CikinsauriHanne ta ce "Lah Baba na tuna jiya maigari ya aikoda watatakarda da yamma ya ce ta makaranta tace, bakanan. Na karba nasa a akwatina ko itace suke tambaya?Malam Habucike da mamaki da zumudin dauko takardar ya ce"Haba 'yarBaba kina 'yar karamarki kike mantuwa, tun dazufa ake maganar takardar duk baki tuna ba. Yi maza kidaukotakardar in nuna musu ko itace takardar. Hanne tadagaakwatin da sauri ta bude, babu komai a ciki saikayan sawarta kala biyu a cukurkude suke kamar anyi sukuwardoki a kansu.Ta binciko can kasan akwatin ta dauko watadoguwar takardafara ta mikawa Babanta. Malam Habu ya karba dasauri ya doshi wajen masu gadin nan yana cewa "Ga daiwata takarda a cikinakwatinta saiyanzu ta tuna ashe mai gari ya aiko da ita jiya kudai ku duba ku gani ko ita ce. A yatsune daya daga cikinsu yakarba yaduba yana dubawa kuwa yaga takardar shaidar andaukiHanne Habu Imamu a F.G.G.C Kazaure ce wato(Admission letter) Sun sha mamaki kwarai da ganin nanmakarantar kuwataci ba batan kai suka yi ba. Cikin sakin fuska sukayi musuizinin su kwaso kayansu suzo su wuce. Cikinmurna Hanne da Mahaifinta suka kwashi kayansu suka wuce izuwacikinmakaranta. Basu tsaya a ko'ina ba sai a bakin wanibabbangini wanda ya kunshi doguwar baranda da ofishinMalamai.Babu kowa a wajen hatta leburori masu share-share da goge-goge duk basa nan, wajen tsit kamar babubil'adama. Sukasami gindin wata bishiya suka sauke kayansu.Hanne ta hau kan akwatinta ta zauna Malam Habu ya ce "To fawannanshine ko in kula, yanzu kuma ina zamu dosa kokuma wazamu tambaya? Ni wallahi abun nan na makarantarbokon nan ya ishe ni daga nan sai can ana tsattsare ka datambayakamar a lahira mun gama da masu gadi yanzukuma Allah nekadai Ya san wa zamu hadu dashi, kai Allah Yakyauta, wannan shine ake cewa ba shiga ba fita wai anbawamahaukaci gadin kofa. Shigowar wata dalleliyarmota ce Jeeplaunin koriya (dark green) wacce ta tunkaro indasuke, ita ta katsewa Malam Habu surutun da yake yi. Ta zo dafda su tatsaya babu abinda yake tashi a cikinta sai sautinkida dasanyin A.C maza ne samari guda biyu suka fitodaga gani wa ne da kaninsa, kanin yana sanye da kayan bautarkasa ajikinsa wato (N.Y.S.C) Yayan kuwa wata tsadaddiyarshadda cefara sol a jikinsa sai kamshin wani tsadadden turarene yake tashi. Abunka da kauyawa sai kallo suke dukkauba da *yar,kanin ya bude but din baya ya dauko wata Jakarkaya, yamayar ya rufe ya ce da wansa "Yaya Habib, na godesai dai nace maka Allah Ya kiyaye hanya. Yaya Habib yayimurmushiya ce "To madalla. Allah Ya bada sa'a sai yaushekuma zaka zomana weekend? Ina fatan dai wannan karan zakayi kamar wata baka zo ba ko?Su duka biyun suka tuntsire da dariya, kanin yace "Ai Yayaranar juma'ar nan zaka ganni a gida ko ba'azodaukana ba mazanzo Kano, haba ai sai jini na ya hau zama a kauyein ba dole ba wa zai iya? Yayan yana dariya ya mikawakanin hannusuka gaisa ya ce "To Allah Ya taimaka, ina ganinranar juma'arda zaka zo may be baza mu hadu ba saboda dasassafe zan tashi zuwa america kai kuma nasan sai da yammazaka tahosai an tashi *yan makaranta ko? Kanin ya ce "Ehkuwa bazamu hadu ba Allah Ya kiyaye hanya Ya dawomana da kai lafiya, Yaya akwatinan auren da nawa da naka yazamo iridaya. Yaya Habib ya ce "Insha Allahu, Yaya Habibya shigamota har zai ja kofar motar ya rufe sai ya juyo yakalli Hanne da Babanta ya ce "Salamu alaikum" Malam Habu yaamsagami da daga hannu, Yaya Habib yaja motarsa yajuya ya nufikofar fita kanin na tsaye yana daga masa hannu.ayan da motar Yaya Habib ta kure, idanuwansuduka na kantasannan hankalin kowa ya dawo jikinsa. TunaninHanne yakoma ga kallon kyakkyawan ginin makarantarginin bulo da bulo,yaune rana ta farko da take tunanin take saran zatakwanta a dakin ginin bulo ba gidan kasa ba rufinazara. Ta cea ranta "Cafdijan yau kuwa zan iya bacci? Anyabazan ringa jin sanyi ba a wannan dogayen gininnikan. Bata sansanda tayimurmushi ba har hakoranta suka fito, sai tawayence ta kifakanta akan cinyarta kada Babanta ya ganemurmushin dadi take. Kyakkyawan saurayin nan ya tunkaro indasuke yanarataye da jakarsa a kafadarsa, ya yiwa Malam Habusallamagami da dan dukawa kadan, kana ya wuce su yajegindin wata bishiyar dake kusa da tasu ya daga wani benci yazauna yaajiye jakar kayansa a kusa dashi yaci gaba dakallon Hanne daMahaifinta. Can Malam Habu yaje ya same shi a indayake zaune ya ce "Dan Allah *yan samari kai maka'aikacine ananko kaima bako ne? Yayi murmushi ya ce "Yaya akayi Baba?Malam Habu ya ce "Yarinya na kawo makaranta tundazu banga kowa ba balle in tambayeshi hannun wa yakamata indankata? Saurayin nan ya gyara zama gami da cirehular dakekansa ya ce "Daliba, daliba ce wannan? Malam Habuya ce "Eh nan aka ce na kawota kuma gama takardar canbari ta mikogama korarmu akayi dazu da babu takardar, yakwalla kira yace "Hanne kawo takardar nan ta dazu.Cikin sauri Hanne tasa hannu a cikin bokiti dakegabanta tadauko takarda tazo ta mikawa Babanta da hannubiyu ta dukahar kasa. Babu abinda wannan saurayi yake saikallon Hanne sama da kasa kayan jikinta yake kallo da takalmindakekafarta wanda ta daure da leda saboda ya tsinkekudin naninma aiki ne, wata uwar danmara kai kace dambentsiya za'a kwasa, wuyan, hannu da kafa tsakiyoyi. Saurayinnan ya kulada lallai Hanne ita kanta tana jin kunyar shigar nantata ganinkallon da yake yi mata, sai yayi sauri ya fara dubatakardar da Malam Habu ya mika masa. Ya karance tsaf, sannanya dagoya ce "Hanne Habu Imamu ko? Tace "Eh, ya ce "ToBaba saikun dan jira don nima nan Malamin nake jira gashitakamaimai ma ni bansani ba ko yana makarantar kobayanan don nima shigowata kenan. Malam HabuyayiHamma gami da yin dan siririn tsaki ya ce "Yaroyanzu bayadda za'ayi ka karbi yarinyar nan, dole sai waccan din ya zo? Saurayin ya ce "Ni Malami ne amma kuma bapermanentteacher ba bautar kasa (service) nazo yi, a ka'idarwannanmakarantar kuma senior master ne ya kamata ya karbetamusamman ma kasancewarta sabuwar daliba ce.Gashi yau lahadi, dama litinin ce ko sauranranakun aiki lokacin principal tana nan, da sauranpamanent teachers duk sai su karbeta koda seniormaster baya nan, amma yanzu ku jira kadan idannan da minti talatin bai dawo ba, zan tashi nima nashiga staff quaters din na gani ko yana ma cikin makarantar dan nima shi nake so na gani zan karbimukullan gidana. Malam Habu ya ce "To Allah Yakawoshi lafiya bari nayi sallar la'asar, nasan biyartayi ko sallar la'asar bamu yi ba. Yaro ina buta? Yanuna masa wani fanfo can kusa dashi kuma dazagayeyyen waje nan ne Masallaci. Malam Habu ya ce "To madalla. Ya kalli Hanne wacce ke tsaye agefe har yanzu ya ce "*Yar Baba koma kanakwatinki ki zauna zanje nayi sallah kinji. Cikinsanyin murya ta ce "To, ta juya ta doshi wajenakwatin. Malam Habu ya bita da kallo zuciyarta cikeda tausayinta ganin yininsu guda babu abun da suka ci tun dan kokon safe da suka dan kukkurbaa tsattsaye bala'in Iya Abu ya hanasu su zauna susha sosai. Malam Habu ya girgiza kai alamartausayawa kansu da kansu ya ce "Allah Sarki *yarBaba hakuri dai za ki yi, ki kuma ci gaba dayi.Sannan ya juya ya nufi wajen fanfo. Kyakkyawan saurayin nan na zaune yana kallonsu zuciyarsacike da alamomin tambaya da tsananin tausayi. Canya nisa yayi ajiyar zuciya ya zaro gilashin dakealjihunsa ya saka a idonsa gami da cusa hular dakehannunsa a cikin aljihunsa na wando yasahannunsa ya dafe habarsa yaci gaba da kallon Hanne dake zaune kan akwatinta tayi lamo tanatunani ba tare da tasan wani na nan gefenta ta cikingilas yana kallonta ba. Ya ce a ransa "Wadannandaga wanne kauye suke?Sun kuwa karanta takardar dake hannunsusunsan me ya kamata su tanada suzo dashi? Kaibasu san dokar da aka rubuta ba a jikin joininginstruction din nan ba. Lallai kuwa da sun san meaka rubuta da baza taci uwar danmarar nan ba tashigo makarantar nan haka ba. Bayan kamar
Chapter 2 · 0% Book details