← Book details Gangar Jikinsa Na Aura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 26

Sashe 17

Gangar Jikinsa Na Aura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

masa wasika tace ''inji senior juwairiyya da senior salaha suncedole in taho musu da amsa kar inzo babu amsa yabata rai ya karbi wasikar ya bude ya karanta.Wasika ce irin ta kullum daga juwairiyya ya cecirayuwarta tana sonsa.Haisam ya cikuikuye ya wurgar ya ce'' sun bakimagungunanki'' tace''ah ina ji sune anan'' ya karbaya bubbude yana tsiyaya mata a murfi yana mikamata sai ta karba tasha. Sai da ya tabbatar ta shadukka sannan ya daure ledar ya mika mata ya ce tawuce daki ta kwanta gibe idan taga baza ta iya fitowa aji ba tayi kwanciyarta zai sanarwa da dutymaster. Daga karshe ya ce'' sai da safe allah ya bakilafiya hannah. Tace amin '' har ta juya zata tafi sai tatuna ta juyo tace masa'' me zan cewa seniorjuwairiyya ? Ya ce'' kice nace tazo ta karbi amsar dakanta. Hannah ta amsa da to sannan ta tafi. Daman su juwairiyya na zaune a wata baranda suna hangosu. Hannah tazo wucewa suka kirata tace musu takai masa ya ce amsar taje da kanta ta karba. Salahatace'' jeki to'' juwairiyya ta nisa tace'' kinga haisamko wallahi wulakanci yake shirin yimin tunda ya ceinje da kaina ni nasan ba wata maganar amincewa zaiyi min ba. Saboda ai nagani cukuikuye wasikartawa yayi ya yar a kasa, ya buge da bata magani aidole ma son hannah yake'' salaha tace'' ammakuwa sunan yarinyar na gawa don sai taci ubanta amakarantar nan , mu 'yan s.s.3 muce muna sonsayaki ya so junior mu ai bazai yuba. Jeki kiji abinda zai fada muki don muci uwarta da hujja'' juwairiyyata mike ta nufi ofishin haisam tana wani karkaderiga tana gyara fuska. Tayi sallama gami da turakofar zata shiga ya dakatar da ita da hannu yace''tsaya daga nan baranda kiji abunda zan fada miki.Don me kika sake yimin aiken wasika bayan nace kada wanda ya sake zomin da wasikarki. Kumawanne rashin tausayi ne da zaki taso yarinya mararlafiya ki aikota, duk daliban makarantar nan, saihannah ? Me yasa sai ita zaki aiko juwairiyya ?Juwairiyya ta tsuke fuska tace'' amma uncle haisamduk aiken dana keyi baka taba kirawoni kace meya sa nake aiko kawayena ba sai dai kacewayan aiken duk wacce ta sake zuwa zaka sabarmata. Meya sa baka fadawa yar aiken ba a wannankaron sai ni ka kira ? Haisam ya fusata ya dakamata tsawa yace'' ina tambayarki kina tambayata ?To kar kiji yauce rana ta karshe da zaki yimin haka. Ki rike darajarki da mutuncinki a matsayinki na yamace budurwa. Idan sai kinyi soyayya a makarantaba karatu ya kawo kiba to ga sauran malaman dasuke rubibin sonki amma ni bani da ra'ayinsoyayya, this is the last warninng bana son na sakeganin sako daga wajen ki sai anjima kije. Wani jiri jiri juwairiyya take ji ta juya ta tafi tana kwafa.Salaha tazo ta tare ta a hanya tana cewa'' meyenake hangoki a baranda ofishinsa ma ya hanakishiga ? Juwairiyya tace'' ke dai muje in baki labarinyadda muka yi'' daman lokacin tashi daga prepyayi duka dalibai sun dungumo daga ajijuwansu sun doshi dakunansu. Don haka juwairiyya dasalaha nura sai suka nufi hostel a hanya ta zaiyanamata duk yadda suka yi da uncle mai kyau watohaisam. washegari talata da sassafe bakwai da rabia lokacin dalibai suke firfitowa daga dakunansuzuwa ajijuwansu domin daukar darussa. Uncle haisam a tsaye yake kem a bakin get din hostelyana kallon masu fitowa daga ciki, mamaki yakama dalibai ganin sabon al'amari meye unclehaisam yazo ya tsaya anan da sassafe haka bashine da duty ba, ba ranar inspection ba kuma.Kowacce idan ta ganshi sai ta duka ta mika gaisuwa ta wuce'' good morning sir'' can ya hangorauda da nusaiba da pamella suna tahowa daganesa ya dauka hannah ce sai da suka karaso yagababu hannah a cikinsu. Bayan sun gaisheshi ya ce''yau kuma ina hannah ko jikin ne ? Rauda ta waigagaba da baya taga babu kowa sai ta matso kusa dashi tace'' hannah ba lafiya tana clinic a kwanceacan ta kwana'' gabansa ya yanke ya fadi ya ce''zazzabin ne ya rufeta ? Nusaiba tace'' wannan yafizazzabi yaya'' rauda tace'' su senior juwairiyya nesuka yi mata duka da tsakar dare kusan dukkan s.s3 sai da kowacce ta doki hannah jiya ina ji a sume ta fadi da kyar matron suka zo suka hana su. Mumabamu san me tayi musu ba. Kuka mu ma mukakwana muna nan da nan haisam ya canja ido yakada yayi jawur gashin jikinsa ya mimmike kai kacemuku mukun sanyi ake amma duk da sanyin safiyazufa yake yi. . Ba tare daya ce tak ba ya juya ya nufi clinic inda hannah take a kwance ya same ta rikkicifbata sanma inda hayyacinta yake ba. Abinka dafarar fata sai sabun bulalan suka mata jawur a jiki ,har wuyanta da fuskarta shatin bulala ne lambar.Ya dade a tsaye yana kallonta kawai yasa hannu yacire mata wani ganyen maina daya makale mata a wuya a sanadiyar duka sai yaji jikinta zafi kaukamar wuta, yaja mayafin dake kan gadon yalullubeta. Babu kowa a clinic din nurse din ma batanan. Ya juya ya fita a fusace ya nufi ofishin principal.Ya shiga ofishin gami da yin sallama ya sami wajeya zauna bayan sun gaisa ta dubi haisam tace''haisam lafiya yau na ganka ranka a bace dukwannan fara'ar taka ? Ya ce''dole raina ya bacisaboda kusan kashe wata yarinya akayi a daren jiya a makarantar nan 'yan aji shida ne suka dakiwata yar aji hudu da tsakar dare kamar zasukasheta tana clinic a kwance'' principal ta zaburatace'' subhanallah'' ta danna kararrawa masinja yashigo tace maza yaje aji shida ya kira matajuwairiyya. Haisam da principal na zaune sunyi jugun kowa yana tunani a zuciyarsa. Can saigajuwairiyya ta karaso ita da wani malami mai sunasahabi tazo ta dutkusa a kasa ta gaishe daprincipal. Principal ko amsawa bata yiba ta rufejuwairiyya da fada tana cewa'' in har ba zaki iyahana a aikata laifi ba a makarantata banga amfaninki ba a matsayinki na shugabar dalibai''haisam yace'' madam ai itace ta gaiyato sauran yanaji shidan suka hadu sukayi dukan'' principal tace''oh har da ke head girl kuka hadu aka kusa kasheyarinya, kiyi kneel down yau sai kun yabawa ayazakinta'' uncle sahabi yayi carab ya ce'' madam tsaya kiji, juwairiyya ta fadamun duk abunda yafaru daman zamu taho wajenki muka hadu damasinja a hanya a gaskiya yarinyar ce bata dakunya wai cewa tayi zata yi dambe da head girlshine juwairiyya ta danyi mata bulala uku labourprefecr tayi mata biyu. Ga yarinyar can ma a aji tana daukar darasi babu wani zancen kisa'' haisam yafusata yayi kan sahabi da fada yana cewa'' karyazanyi musu? Yarinyar da duk makarantar nan babumai shirunta da ladabi yaushe zata ce zatayi fada dahead girl ? Kawai baza ka tsaya kayi bincike ba donsun gaya maka karya da gaskiya shine zaka yarda, kaje clinic kaga jikinta a farfashe bata san ma indahaiyacinta yake ba . Sahabi ya ce '' madam donallah ki raba mana rigima ki aika clinic a dubo idanakwai wata marar lafiya. Babu kowa ta warke tamike ba'a gabanmu hannah tazo ta wuce ba dazuko ba hannah ba ce wacce kake cewa an kusa kasheta ? Kuma kai duk wannan hakilon da kakecewa akan hannah saboda kai saurayinta ne fa shiyasa kake wannan sauran da ake duka ka tabamagana ? Principal ta lura maganar babba ce saimanya sai tace da juwairiyya ta tashi ta tafi zata aikoayi kiranta. Fuskar juwairiyya cike da murmushi ta fice principal ta kalli haisam tace'' kwarai tun ba yauba ansha fada mun kana soyayya da hannah.Dokar makarantar nan an hana daliba da malamiyin soyayya . Yanxu na gane manufarka don andaki budurwarka shi yasa kayi magana ko? Dagayau zan sa c.i.d kada ka kuskura in sake jin ance kana soyayya'' haisam ya fusata, ransa ya bacizuciyarsa ta hau tafarfasa. Ya dakawa sahabi tsawayaje har gabansa yana nuna shi da hannu ya ce''kai sahabi karya kake yi ni nafi karfin ka yi minsharri kai da juwairiyya zaku gane kuranku amakarabtar nan. Ni kake cewa ina son hannah ko ? Bayan da bakinka kazo ka sameni kana rokona inhadaka da kanwata hannah kana sonta naki nacekabarta tayi karatu ashe kana kullace dani kasaaka yi mata wannan dukkan ko ? Ke kumaprincipak kin goyi bayansu sun daki yar mutabe abanza ko ? To ni sai na daukarwa hannah fansa da kaina'' ya kada kai ya fice. Sahabi ya juya ya kalliprincipal yace'' kinji kuma inda ya lauya maganako ?tace ''kyaleshi bayan kai ma mr.ojo ya fadamun cewa son hannah yake don haka kaci gabada kula dasu. Haisam ya nufi staff qurters ya shigagidansa ya zauna a falon yana huci kamar ya kashe kansa yake ji saboda tsananin bakin ciki yau kodarasi ba zai je yayi ba. Yini yayi cur a gida ya kudiriniyyar zai dauki fansa akan duk mai hannu a cikinwannan al'amari , wai sahabi ne zaiyi masa hakasahabin da ke zuwa har gida yace ya taimakeshi yashawo masa kan hannah wai juwairiyya da kanta take cewa rashin kunya hanna tayi mata zata yidambe da ita wai shine tayi mata bulala uku itakuma principal da kanta take bin bayansu bayantasan hannah tasan halinta tasha yin kwatance daita a wajen assembly akan tafi kowa da'a da ladabishine har ta yarda da kintsin da suka yi mata ko da kyau, haka haisam ta dinga nanatawa a zuciyarsa .Haisam ya dinga nanatawa a zuciyarsa. Haisam baifita daga gida ba sai da yamma misalin karfe biyarya shigo cikin makaranta a lokacin dalibai sunaprep din yamma ya wuce kai tsaye ajinsa don yagajikin hannah, a zaune ya ganta a kan kujerarta ba laifi jikin burdin bulalan ya dan warware zazzabinya sauka sai dai bata iya bude idanuwanta sosai. Yace da ita'' hannah ya jikinki ? Cikin sanyin muryatace'' da sauki'' yace kinsha magungunan naki?Tace eh nasha'' wani masinja ya leko ajin yacemalam haisam kazo inji principal. A fusace haisam yace meye kuma? Dan aiken ya ce'' waya aka bugomaka zaka dauka a ofishinta'' ya ce gani nan zuwahaisam ya juyo ya dubi rauda da nusaiba ya ce'' kudinga kula da hannah ku tabbatar tana cin abincikunji ko ? Suka amsa da'' to zamu kula da ita.Sannan ya fita daga ajin ya nufi ofishin principal yana isa ofishin yayi sallama ya shiga ya gaisheta amurtike. Tace'' yayanka ne habibu yake son yayimagana dakai nace ya kira nan da
Chapter 17 · 0% Book details