← Book details Furar Danko Part1 Compete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 111

Sashe 99

Furar Danko Part1 Compete Hausa Novel · about 6 min read

WASHE GARI ta tashi da ɗokin fita aikinta, musamman zancen shiga kotu da zasu fara yau akan case ɗin nan. Tsaf ta gama shirinta, sai uban ƙamshi take zubawa dan ta baza turaren nata. Tana ƙoƙarin ɗaura igiyar takalmanta ya shigo ɗakin. Sanye yake da jallabiya ash da bata kai masa har ƙasa ba sosai, sannan gajeren hannu ne da ita. A jikin ƙofar ya jingina tare da harɗe hannayensa a ƙirji ya zuba mata idanu kawai. Ƙin ɗagowa tai duk da taji shigowar tasa har sai da ta kammala. Koda ta ɗago ɗin ma kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta tana miƙewa. Da ga sama har ƙasa ya sake ƙare mata kallo. Yayinda ita kuma ta ƙarasa tattare kayanta ta nufo ƙofar kanta tsaye. Kallonsa tai kamar yanda shima yake kallon nata, a dake ta ce, “Ina kwana bani hanya”.

Maimakon amsa mata sai ya ɗan kauda idanun nasa a kanta ka ɗan batare da ya motsa ba ko ya tanka. Ta fahimci so yake su maimaita na waccan ranar, ita kuma ba haka take buƙata ba. Dan haka ta danne abinda ke taso mata da ɗan kwantar da murya ta ce, “Please Hydar 9:30 ne shiga court fa, kuma ka sani”.

Cikin husky voice ya ce, “Idan baƙyason rasa shari'ar ko makarar go and change your dresses. Na faɗa miki duk abinda bakina ya furta shine nake buƙata kuma bana canjawa da ga ra'ayina akan duk abinda na riga na tsara.”

Cikin ɓacin ran da ya fara yunƙuro mata ta ce, “Aliyu!!...”

Hannu ya ɗaga mata babu alamar wasa a tattare da shi. Muryarsa vary deep and vary clear ya ce, “Na yanke kuma na zartar, bi kawai shine masalaha Mawaddat. Ke matata ce, nace bana buƙata to bana buƙatar. Kiyi kawai kodan kuma ki sami yanda kike so mu kuma zauna lafiya”.

Jitai jiri ma na neman kamar ɗibarta. Amma sai batace komai ba tai masa wani irin kallo mai ƙunshe da abubuwa masu yawa ta juya kawai ta ajiye kayan hannunta a saman gadon. Komawa tai wadrobe ta ɗakko hijjab zata saka kawai, amma sai ta tsinkayi muryarsa yana faɗin, “Kayan duk zaki canja zuwa wasu, bana son wannan turaren kuma idan zaki fita, idan zaki saka a gida fine ko zakiyi wanka da shine ba babu damuwa a gareni. Sakawa a fita ne dai bana so dan haramunne ma a gareki ba faɗa ta bace.” bata tanka masa ba, sai kayan data ɗauka ta nufi toilet dan taga baida alamar fita, ita kuma taci alwashin bazata kulashi ba a yanzu saboda abinda ke a gabanta. Tsaf ta sake shiryawa cikin wasu kayan ta saka hijjab ɗin ta fito, sai ya samu kansa da kafeta da ido. Dan tayi ƙyau matuƙa a cikin hijjab ɗin fiye da waccan ranar. Shi da kansa ya ɗibar mata kayan yay gaba tabisa a baya tana taunar lips na danne masifar dake cimata zuciya. Baya ya ajiye mata kayan tare da miƙa mata hannu alamar ta bashi key ɗin motar dake hanunta.

Rai a ɓace ta ce, “Bana buƙata”.

“Kema kin san aikina ne ai hakan”. Ya faɗa babu wasa shima a tattare da shi. “Aina faɗa maka na kore ka”.

“Ban koru ba, dan bake kika ɗauke ni aiki ba ai ko”. Ya sake bata amsa a dake yana zare key ɗin tare da jan hanunta ya tura ta kujerar kusa da driver ya maida ya rufe. Zagayawa yay shima mazaunin drivern. Koda yaje gaban gate sai da ya fita ya buɗe sannan ya zo ya fita da motar ya sake komawa ya rufe gidan sannan. Tunda suka ɗauki hanya babu wanda ya tankama wani, gara shi ma ya miƙa mata ƙaramin flaks da ya haɗa mata tea a ciki. Kamar bazata amsa ba sai kuma ta amsa tana harararsa. Murmushi kawai yay batare da yace komai ba ya maida hankalinsa ga tuƙinsa. Kai tsaye office ya kaita, inda suka samu abokan aikinta suna tsaiwar jiranta duk da safiya ce sosai. Motar na shigowa suka shiga mata marhabun su Zainab na mata spry da ƙyalkyali mai ƙamshi da ga shi har ita. A take aka shiga musu murnar auren. Kamar yanda ya dake yana amsawa itama sai ta dake tana amsawa. Sunci kusan mintina goma a wajen kafin Zainab ta kwashi kayanta suka wuce office, shi kuma sai ya fito bayan sun ɗan yi magana da security ɗin nan da a yanzu suka saba sosai ya samu napep ya shiga ya koma gida.........✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣9️⃣

.......Alhamdullah yau Lulu zata ce kasancewar abubuwa sun tafi mata yanda take so. Dan duk da zaman shari'ar yau aka fara Alhmdllh tana hango nasara a cikinta. Bayan barin kotu da Hassan yazo ya kaita da kansa office ya sake maidata, ta ɗan taɓa aiki bayan sallar azhar ta fito. Tana jan mota ta fita Security ɗin nan ya dannama Smart waya ya sanar masa. Godiya yay masa sannan shima yay kiran wanda ya saka ya dinga bibiyar masa ita akan yabi bayanta da napep ɗin. Kai tsaye anguwar da mijin Hawwah yake ta nufa, da tambaya ta isa gidansu Sa'id. Mai Napep da ke binta ya kirasa ya sanar masa. Sosai Smart yay mamakin abinda ya kaita, har ya dinga jin son yazo amma dai ya dake da ƙyar dan son ganin iya gudun ruwanta. Sama-sama ta gaishe da maigadin tare da tambayarsa ko hajiyar gidan na nan? Amsa mata yay da eh cikin washe haƙora. Fuska ta yamutse cike da izzarta ta ce, “Sanar mata tana da baƙuwa”. Babu musu ya amsa mata da to yana nufar cikin gidan. Mintinan baifi uku ba sai gashi ya dawo ya ce ance ta shiga.

Kallon gidan ta dingayi side by side tana taɓe baki, a irin dukiya ta gidansu gidan su Sa'id ɗin ba komai bane ba, sai dai ba laifi suma dai da gani akwai kuɗin sai dai ko kama ƙafarsu basu isa yi ba. Ƙofar da take ƙyautata zaton falon gidan kenan ta nufa, cikin sa'a ma sai ta hango wata yarinya tsaye kamar tana kuka da alama mai aiki ce, isowarta kusa da ita ya sata daina kukan ta risina ta gaisheta. Sau ɗaya ta amsa mata ta ɗauke kanta. Yarinyar ce ta mata iso cikin falon, babbane sosai ya kumaji ɗirka-ɗirkan kujeru kamar bana dattijuwa ba. Kallo ɗaya taima matar dake zaune a falon ta fahimci itace mamar mijin Hawwah ɗin, dan ko'a ido ka kalleta kasan za'a zuba da ita kam. Zama tai kanta tsaye tun kan ma ace ta zauna, maman Sa'id dai kallonta take alamar rashin sani, duk da Lulu ta fahimci hakan sai ta basar, cikin ɗaukar kan nan nata na isa da ƙasaita ta ce, “Hajiya barka da rana. Sunana Barrister Mawaddat Isma'il Jiƙamshi.”

Sai da zuciyar maman Sa'id ta motsa jin ƴar waye, sannan sunan kansa na Mawaddat ɗin duk mai bibiyar harkokin mata a fanin fyaɗe dole zai santa, ita kanta dama tunanin ina tasan wannan fuskar takeyi. Lulu data lura da hakan ta cigaba da faɗin, “A yanzu haka matar Aliyu M. Idris Mawashi yayan matar ɗanki dan bana tunanin kin halarci bikin sati ɗaya daya shige”.

Gaba ɗaya Mama duk sai ma taji ta daburce, dan tabbas Sa'id yata roƙarta zuwa bikin amma tace bazataje ba dan ba'a gayyaceta ba, koma an gayyacetan bazataje bikin matsiyata ba dan tasan dai bai wuce tuwo da waina da zoɓo ba. Harga ALLAH bata san ɗiyar wa Aliyun ya aura ba. Da ɗan jimami ta ce, “Da gaske kece matar Aliyun?”.
Chapter 99 · 0% Book details