← Book details Furar Danko Part1 Compete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 111

Sashe 45

Furar Danko Part1 Compete Hausa Novel · about 6 min read

    A washe gari data kasance safiyar alhamis a duka ɓangarorin huɗu kowa ya tashi da shirinsa game da abinda ya kwana da shi a rai. Ɓangaren su Hon. HD. Nakowa sun shirya tsaf da shirin zuwa neman auren Mawaddat a wajen Alhaji Sufi Ado Garko kamar yanda ya basu dama. Haka ma a ɓangaren Alh. Sulaiman da ɗansa sun gama tsara komai a daren jiya domin cikar burinsa da kuma burin ɗansa Tajuddeen da ke ƙaunar Mawaddat har cikin zuciyarsa. Ɓangare na uku shine MM Atik Kumo da shima ya tunkari iyayensa da maganar samo mata da yay, sai dai ya gagara tunkararta yana son iyayen nasa su fara zuwa masa neman izinin nemanta ga nata iyayen. Sosai mahaifinsa da Mom ɗinsa suka shiga matuƙar farin ciki, dan babban burinsu dai a rayuwa shine suga auren ɗan nasu daman. Sun samu wannan damar kam bazasuyi sakaci da itaba, musamman ma da sukaji yarinyar ta fito ne da ga zuri'ar Alhaji Sufi Ado Garko da duk wani ɗan siyasa a jihar Kano ke masa kallon uba. Hakama ƴan kasuwa domin a duk ɓangarorin biyu yana taka rawar gani da tarihi bazai iya mantawa da shi ba ko bayan ransa. Rukuni na gaba sune gidan allurar da kowa ke iyo cikin ƙaton kogin domin nema, wato _Mawaddat Isma'il Ibrahim Jiƙamshi_.
       Mawaddat da tun a daren jiya ta dawo cikin hayyacinta sam bata san duk wannan babban yaƙin basasa da ake shiri a ɓangarori uku domin ita kaɗai ba. Hasalima ita ta wayi gari ne da babban shiri akan mijin matar nan da yay ma yarinya fyaɗe. Har yanzu yarinyar na asibiti cikin mawuyacin hali. Da farko ta hana ƴan jarida yayata zancen har sai ta kama shegen, sai dai a yau wani tunani datai yasa zata bama ƴan jarida damar fitar da komai, tana ganin hakan zai taimaka musu wajen kamashin. Yau da wuri ta kammala shirinta cikin wandon jeans dark blue da milk color ɗin riga. Rigar nada ɗan tsaho musamman ta baya. Ƙaramin veil ta naɗa a kanta tare da bulbula ƙamshin nan nata. Cikin takunta na yanga da izza ta fito, babu alamar jama'ar gidan wani ya tashi, sai su Iya Tabawa dake ta aikin gyaran gidan. Gaisheta suka shigayi cikin girmamawa. Hannu ta ɗaga musu sau ɗaya tai ficewarta dan bata cikin mood ɗin yin magana yau. Karo suka kusan ci da Uncle Yousuf da ke ƙoƙarin shigowa a main falour. Tai saurin komawa baya da faɗin “Sorry Papa ban san ka taho ba”.
       “Ina zaki haka?”.
   Ya faɗa a dake maimakon amsa maganarta ta farko. Ɗan kallonsa tai da mamaki, sai dai ganin yanda shima ke kallonta babu alamar wasa a tattare da shi ya sata maida kanta ƙasa cikin tsarguwa, dan dama dauriya take kawai, amma tun a daren jiya take ƙullawa da kwancewar ta yanda zata iya haɗa ido da shi, da kuma yanda zata shukama drivern ta rashin mutunci a wannan karon tunda har ya sake bari Uncle Yousuf ɗin ya ganta a cikin wannan yanayin.....
      “Baki ji bane? Ina zaki je?”.
  Ya sake faɗa cikin katse mata tunani. Firgigit ta dawo hankalinta. Cikin in ina ta ce, “Uncle You office, amma zan fara zuwa nai magana da ƴan jarida akan case ɗin yarinyar nan shiyyasa zan fita da wuri”.
     “Shi kuma naki case ɗin kiyi yaya da shi?”.
    Da sauri ta ɗago ta dubesa. “Uncle case ɗina kuma? Ni ai babu abinda ya faru da ni”.
           “Zai farun ne ai. Biyoni”.
       Kamar wadda aka bugama guduma a kai haka Lulu ta tsinta kanta a wannan lokacin. Sai dai bata da zaɓin da ya wuce bin bayan nasa kamar yanda ya bata umarni. Duk abinda ke faruwa Daddy na kallonsu da jinsu. Ya haɗiye hawayen da ke neman zubo masa. A daren jiya ko sau ɗaya baiyi barci ba, sosai jininsa ya hau har bugun zuciyarsa ya fara canjawa. Sai da Mommy ta bashi shawarar yin karatun Alkur'ani sannan ya samu ƴar nutsuwar ganin wayewar gari lafiya. Mommy dai bata san ainahin mike faruwa ba. Amma zuciyarta na bata akan Mawaddat ne, dan a yanzu babu wata damuwa da ke neman kai mijin nata ƙasa sama da al'amarin yarinyar, bayan kuma tun farko shine yay shukar datai tsirran da ya samar da ita a haka.
       A falon baƙi da ke a garden kam babu abinda zuciyar Lulu keyi sai bugawa da sauri-sauri. Ga Uncle Yousuf yay matuƙar ɗaure fuska ta yanda bata taɓa gani da ga garesa ba. Zama tai jiki babu ƙari da faɗin, “Uncle gani”.
        “Na ganki ai”.
      Ya bata amsa shima kai tsaye yana gyara zama. Tambayar da tai matuƙar girgiza mata zuciya ya jefa mata. Babu shiri ta ɗago a firgice ta dubesa. Sake maimaitawa yay babu alamar wasa a tare da shi. “Nace wanene Hon. Haruna Dauda Nakowa a gareki? Miye alaƙarku?”.
    “B...b...bamu da wata alaƙa wlhy Uncle”. Ta faɗa cikin in ina da firgici.
         “Amma yaje neman aurenki ga Baba a daren jiya”.
    “What!! Uncle You aure fa? Ni kuma Mawaddat?!”.
           Cikin sigar harara Uncle Yousuf ya bata amsa da “K ɗin fa, bayan shi kuma Tajuddeen ma ya dawo. Dan a jiya mahaifinsa a gabanmu ya sake gabatar da zancen ku ga Baba. Nasan kuma baki manta da alwashi  Baba ba na cewar duk wanda yazo neman aurenki ko da amincewarki ko babu ko da tamu ko babu zai aura masa ke. Kinga hakan na nufin a cikin biyun nan dole ne ki zaɓi ɗaya”.
        “Wlhy Uncle You bana son kowa a cikinsu. Kuma shi tsinanne Haruna ɗin nan ni ban taɓa magana da shi ba ma balle maganar aure na rantse maka Uncle”.
     “Ni wannan ba matsalata bace Mawaddat. Dan a yanzu haka ma Baba nacan na zaman jiranmu ni da ke da Yaya akan wannan maganar dan haka ma na dakatar da ke daga fita. Idan kuma kina da wanda kike so sai ki faɗa mana yanzu mu nemosa aje da shi gaban Baba ki kuɓutar da kanki, dan hakanne kawai zai hana Baba bama ɗaya da ga cikin waɗan can ɗin aurenki kamar yanda kika san shi baya magana biyu”.........✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣6️⃣
Chapter 45 · 0% Book details