Sashe 46
Furar Danko Part1 Compete Hausa Novel · about 5 min read
........“Na shiga uku Uncle, ni ban shirya yin aure ba wlhy. Dan ALLAH ka faɗa mini ya zanyi?”.
“To ni Mawaddat taya zan san ya zakiyi. Yanzun ma na faɗa miki ne dan bana son a miki abinda nasan baki so. Dan Baba bazai taɓa canja ra'ayinsa ba a wannan karon kin sani na sani. Ga kuma Yaya wajen ƙoƙarin ganin ya kare ki sai ya sake wata ɓaranɓaramar wai kina da wanda kike so”.
Fuska ta kuma kwaɓewa idanunta na cika da ƙwalla. “Uncle You wlhy guduwa zanyi”.
“Guduwa kuma? A ganinki itace mafita Mawaddat?. To ai ina ganin dan kin gudu kinyi a banza, dan in dai Baba ne zai aurar da ke ɗin babu fashi ya kuma saka mijin taddaki har inda kika je ɗin ko shi yaje da kansa ya dawo da ke ya danƙama mijin. Kinga anyi ba'aiba kenan ko. Ni dai ina ganin kawai mu ɗauki kariyar da Yaya ya baki muyi amfani da ita dan ki kuɓuta gaba ɗaya”.
“Uncle wacce kenan?”.
“Samo wani matsayin wanda kike so kuma zaki aura. Sai dai ni da ke ne kawai muka san ba haka bane, bayan ƙura ta lafa shike nan sai ki cigaba da sabgarki, idan Baba yayi magana muce iyayen yaron muke jira dan sunce a ɗan jinkirta musu zai ƙarasa gininsa ko dai mu samo wani abu da zai ɗauke hankalin Baba da ga kanki gaba ɗaya”
“Hakan yayi, to amma Uncle kasan fa baba da shegen bin ƙwaƙwƙwafin abu idan kuma ya gano fa?. Sannan ma wa zamu iya samu ya mana wannan aikin batare da an samu wata matsala ba?”.
“Eh kuma fa kema kinzo da maganar dubawa gaskiya. Dan Baba kam zai ma iya sawa ai masa bincike. To amma ina ganin mizai hana shi wanda zamu samar ɗin kawai ki yarda kuyi auren contract da shi, komai mune zamu tsara masa ayi auren amma bayan wata ɗaya ya rabu da ke, sai dai da sharaɗin kada kowa ma yasan ya sake ki har sai bayan wasu shekaru.”
Shiru Lulu tai tana auna zancen Uncle ɗin nata. Sai dai da ace tana da ilimin addini da ya kamata tai hasashen yin hakan fa zai iya zama kamar ta zurma kanta ne. Amma a maimakon hakan ita wani tunani take da ban, dan tana ƙiyasta faruwar al'amarin ne cikin sauƙi kasancewar a inda ta girma cikin turawa wannan ba komai bane yin auren yarjejeniya.. ganin yanda tai nisa Uncle Yousuf ya katseta da faɗin, “Mawaddat bamu da wani isashen lokacin dogon tunani a yanzun fa”. Firgigit ta dawo hankalinta, sai kuma ta langaɓe kai cikin shagwaɓa. “Uncle You ni gaba ɗaya ma kaina ya kulle ne, dan ban san inda zan samo wanda zamuyi hakan ba”.
“To mizai hana ki yarda da batun Tajuddeen kawai, yaron nan yanada hankali da nutsuwa ga ilimi. Yana aikinsa sannan yana matuƙar sonki”.
“Uncle wlhy ni bana son sa, na tabbatar kuma bazan taɓa son shi ba. ALLAH idan aka matsamin kan na auresa zan iya halakash....”
“No! no! Kar na sake jin haka. Tunda har baki sonshi shike nan kawai abar maganarsa. Mu koma kan maganar mu kawai ta nemo wanda zai zame mana makamin kuɓuta da ga Baba.”
“Uncle bazan ɓoye maka ba wlhy na tsani duk wani abinda zai haɗa mu'mulata da wani namiji bayan ku, balle ma ace mu kasance wai ma'aurata. Impossible hakan ya kasance dan bazan taɓa aure ba.”
Har cikin rai kalmar (Bazan taɓa aure ba) ta daki Uncle Yousuf, dan a karo na farko zuciyarsa ta fara hasaso masa wani al'amari mai girma dangane da Mawaddat ɗin. Dolene akwai abinda ya kamata su sani da ke ɓoye a ƙasan zuciyarta, sanin kuma na nufin haƙurin bin matakan daya dace. Wannan tunanin ya sashi cigaba da faɗin, “Mizai hana muyi amfani da Aliyu, dan yaron nada nutsuwar da bazai taɓa iya bamu ciwon kai ba koda anan gaba”.
“Aliyu kuma? Waye shi?”.
*_“DRIVERN KI”_*
Fitar kalmar da ga bakinsa da zaburowar zuciyarta tamkar ragabzane a tsakanin jirgi da jirgi a sararin samaniya. Badan Uncle You bane, da bayan zaburar da tai abinda zai biyo baya shine lailayo masa zagi mai kawuna bakwai ta dire masa shi a tsaye sannan ta tisa da wanke fuskarsa da marin da sai ya hango yanda yaƙin duniya na uku zai kasance tun kafin lokacin faruwarsa. Sai dai kash furucin ya fito da ga bakin da ko harara bazata iya binsa da ita ba balle ɗaukar mataki. Uncle Yousuf da ya zuba mata idanu, sai dai a ƙasan ransa dariya ce ke cinsa yana dannewa da ƙyar yay mata nuni da kujera, tare da faɗin, “Sit mana kika wani zabura kamar wadda na faɗama mummunar magana. Nifa ba nace dole bane, shawarace kawai dan neman mafita. Amma idan batai miki ba muje kawai dan lokaci ma ya cika gashi ana jirana a office. Kije ki zama cikin shiri da yin sabon tunani akan wani tunda naga baki aminta da zancen shi Aliyu ba”.
Bakin data tura gaba ta buɗe zatai magana sallamar Daddy ta dakatar da ita. Alamar zip Uncle Yousuf yay mata wai kar Daddy yaji. Daddy da gaba ɗaya ya gama jin tattaunawar tasu dan tun ɗazun a laɓe yake dama sai ya sake fuskewa cikin pretending ya ce, “Wai mi ake tattaunawa ne kuka shige haka shiru?”.
Cikin ɗan ɗage kafaɗa Uncle Yousuf ya bashi amsa da “Sirri ne tsakanin baba da ƴarsa yaya”.
Dariya Daddy yayi, sai kuma ya juya hanyar fita yana faɗin, “Oh to bari nayi nan tunda ba'a buƙatar naji”.
A karan farko Lulu tai dariya tana mai kamo hannun Daddyn nata cike da shagwaɓa. A haka suka fito suna ƴar dariya.....