Sashe 110
Furar Danko Part1 Compete Hausa Novel · about 5 min read
Ba haka Ahmad yay zaton ji ba dan haka ya zuba masa idanu kawai yana kallonsa. Ɗauke kai Smart yay gefe da sake faɗin, “Ban san kallo malam kaje ka kai aunty Khadijah gida ta huta”.
Yanda Smart ɗin yayi duk sai Ahmad ya sake jin jikinsa yay sanyi. Sai dai dole suka fito dan dare yaja kusan ƙarfe biyu. Godiya Smart ya sakema aunty Khadijah tare da harar Ahmad da ke kallonsa har yanzu dan shi gani yake tamkar Smart ɗin ya shanye komai ne kawai a ransa dan ganin aunty Khadijah. Bayan wucewarsu ya rufe ko'ina da kashe komai. Ɗakin ya koma inda Lulu da aka sakama ƙarin ruwa take. Ya jima tsaye yana kallonta wasu abubuwa masu girma game da ita na sake hauhawar farashi a zuciya da ɓargonsa. Kafin ya lumshe idanunsa tare da ramƙwafawa kanta ya sumbaci goshinta da idanun nan da suka sha kuka yau da bakin tsiwar da ya tabbatar kona dare ɗaya ne dai ya mutu murus yau. “ALLAH yay miki albarka _Noorun Nisaaa_” ya ɗan ja sunan da hura mata iska akan idanunta yana murmushi mai sanyi ƙasan zuciyarsa cike da ɗunbin tausayinta...
Da ga haka ya miƙe ya nufi bedroom yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. Jikinsa ya tsaftace. Koda ya fito maimakon kwanciya sallaya ya shimfiɗa ya fiskanci alƙibla domin miƙa godiyarsa ga UBANGIJIN talikai mai rahama mai jin ƙai. Sai gabannin asuba da ya fuskanci ruwan daya saka mata na biyu da Aunty Khadijah ta bari ya ƙare ya je ya cire shi ma. Zama yay kawai ya saka hannunta cikin nasa ya zuba mata ido, yanda take barcin da sauke numfashi a hankali lokaci zuwa lokaci takan saki ajiyar zuciya. Abubuwa da yawa yake nazarta a kanta. Tun daga randa ya fara ganinta a airport da yaje ɗakkota har zuwa masifar da ya dinga ci a wajenta, aurensu da zaman sati uku da kwanaki huɗu yau cikon na biyar. Ya bata sunan HAWAINIYA da kan canja akowane lokaci da kuma kowane irin yanayi. Kai tsaye baka yanke mata hukunci akan kanta dan sanin ainahinta sai ALLAH. Wato duk bawan da kake kallo yana rayuwa akan kuskure ashe kai tsaye yanke masa hukunci da abinda idonka ya gani a kansa tamkar son zuciya ne. Duk wanda zai baka amsa a kanta zai ce maka she is bad girl ne kai tsaye, domin da wannan siffofin take bayyana kanta wa duniya. Dalilin shine haka aka raineta, haka ta tashi, da hakan kawai tai imani a matsayin gaskiya. “Lokaci yayi da zan san wacece ke Mawaddat? Wace irin turnuƙun ƙura kika tsallake a baya data gina miki rayuwa kamar haka? Wanene yaso lalata miki rayuwa? Miyasa mahaifinki ya nuna miki soyayya amma ya gagara tsayawa akan tarbiyyarki? Miyasa ahalinki sukai sakacin fuskantar rayuwarki na cikin wani ƙulli tun a gaɓar da ya dace ace sun fuskanta ɗin? Ina son sanin waɗan nan amsoshin da ga bakinki MATATA. na miki alƙawarin sake gina nagartacciyar rayuwar da zata fahimtar da ke tsakanin fari da baƙi koda sun gauraye a mazubi ɗaya da izinin ALLAH. In sha ALLAHU zan share miki dukkanin hawayenki na zuci dana bayyane da tafukan hannayena na maye gurbinsu da tarin farin ciki Mawaddatan'warahmah”. Motsawar da tai ya bama hannunsu damar sake matsewa cikin na juna tamkar mai jaddada masa ta amshi dukkan kalamansa itama. Hakan ya sakashi lumshe idanu da sakin ajiyar zuciya...........✍️
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣9️⃣
.......A ɓangaren Alh. Sulaiman Garko yana barin wajen Dada Alh Baita ya kira a waya. Wanda ya shaida masa yana gida yau kam bai fita ko'ina ba. Ya tabbatar masa yana buƙatar ganinsu su dukansu a daren nan dan magana ce mai muhimmanci da shi. Babu musu Alh. Baita ya amsa masa tare da bashi address ɗin inda zasu haɗu. Sannan yay kiran su Hon. Nakowa suma. Cikin abinda baifi awa ɗaya ba suka haɗu a gidan hutawar Hon. Misau dake anguwar Farawa. Tsaf ya zayyane musu komai da suka tattauna da Dada, su kansu sun girgiza da jin wannan ƙulli. Hon. Nakowa ya ce, “Wato su waɗan nan na kula makirci a cikin jininsu yake. Yanzu shima shegen Yousuf ɗin nan ashe tsagerane a haka kamar na ALLAH yana wani sim-sim da kai. To anya kuwa Isma'il bai sanar masa sirrin dake a tsakaninmu ba kuwa?”.
“Abinda nai tunani kenan yasa ni nemanku da gaggawa. Dan in har zai iya irin wannan ƙulle-ƙullen kamar haka dan kada yarinyar nan ta auri ɗaya daga cikin kai da Tajuddeen to inaji a raina wannan taƙamar da hura hanci da Isma'il keyi nada alaƙa da ya sanarma yaron nan komai kuwa. Dan haka nake ganin plan B dole ne mu canja labarin da ga Isma'il zuwa Yousuf, hakan zai bamu damar jifan tsuntsu ɗaya da dutse biyu, sannan zamufi gigita rayuwar Isma'il ɗin da haukatashi”.
“Su kuma yarinyar da yaron fa?”.
Cewar Hon. Nakowa cikin zumuɗi. Duk da Alh. Sulaiman ya fahimci inda ya dosa, amma sai bai nuna masa a fuska ba, sai ma murmushi da ya saki kai tsaye ya ce, “Wannan aikin Dada zata ƙarasa mana shi. Bayan ta ɗauke ta daga wajensa sai muje plan c akansu ita da yaron, dan dama akwai tawa da shi a ƙasa”.
Nan ma sun gamsu matuƙa. Daga haka suka cigaba d tattauna abinda ya shafesu, musamman game da sabuwar alaƙar da suke shirin sake ƙullawa akan business. Har gabannin asubahi sannan suka watse.....
__________★