Sashe 76
Furar Danko Part1 Compete Hausa Novel · about 4 min read
Da mamaki Ammah ke kallon Umma da ke faman murmushi riƙe da basket irin na saƙar kaba ɗin nan mai ƙyau shaƙe da kulolin kayan abinci wai karin kumallo ta shirya za'a kai gidan Smart. Umma data fahimci Ammah zata iya bata matsalafa sai ta sake faɗaɗa fara'arta da katse mata tunani da faɗin, “To kodai banyi dai-dai bane Hafsatu? Dama dai ganin haka akeyi a gidan washe garin da yaro ya tare da matarsa shiyyasa, kuma kinga dai ai ba'a barki da haɗa abinci ba duk gamu cike da gida ko, sai dai kuma naga kamar hakan bai miki ba”.
Murmushi Ammah tayi da ɗan girgiza kanta. Cikin nutsuwar nan tata ta ce, “Ko ɗaya ba haka bane Umman Nasiba, naga kawai an sakaki aiki ne tunda safen nan....”
Caraf Umma ta amshe da faɗin, “Yo minene ALLAH na tuba. Ai an riga an zama ɗaya. Hydar a gidan nan kuma ai ya cancanci fiye da haka. Shi kaɗaine yaron da bai gajiyawa wajen binka har cikin ɗaki ya gaisheka kullum kuma cikin girmamawa da mutuntawa. Bari kiga Huwaila ta miƙa musu tunda tace zata gane gidan lokaci na ƙara ja”.
Murmushin ƙarfin hali kawai Ammah ta saki da faɗin, “To ALLAH ya saka da alkairi”.
Umma ta amsa da “Amin”. tana ficewa
“Anya wannan al'amarin Hafsatu ba akwai wata a ƙasa ba. Matar da tunda aka fara bikin nan ta kasa ɓoye hassadarta ce zata girka abinci akaima Babangida kuma a barta?”. Addah Rukayya ce mai maganar cikin jimantawa. Kafin Ammah tace wani abu Gwaggo Sa'adah ta fito a ɗaki ita da Addah Suwaiba. Har rige-rigen faɗin, “Wannan yaudara ce akwai wata a ƙasa” suke su biyun. Adda Suwaiba ta cigaba da faɗin, “Babu ma wani batun ai mata kawaici magana ta gaskiya fa, kawai a dakatar da su ba ga Hawwah can na musu girkin ba shi kuma ai yaya da shi?. Matar da bata taɓa ƙaunarki ba tun da jajayen sawu sai yanzu ne zata ƙaunaceki Hafsatu, ai daga ji ma kasan akwai ƙulunboton data shiryama abincin. Ita idan yaran nata sunyi auren barinku take ku girka abinci ku aika musu ko sai ke, naga Yalwati ma ta aurar da yara maza har uku a gidan nan ai batai mata hakan ba dan tasan bama yarda zatai ba sai ke sarkin kawaici”.
“Addah ni a ganina ku barta, idan ma wani sharrin take nufi ai ALLAH bazai bata nasara ba. Ballema ni sai nakega kawai dai tayi hakane saboda tujarar da malam yay mata jiya da dare”.
Gwaggo Sa'adah ta ce, “Humm Addah kenan. Yau ya fara mata tujara ne da har hakan zai sakata saduda. ALLAH ki yarda ke dai akwai wani abu a ƙasan kawai. Bakuma zamu gane hakan ba sai anje ankai musu abincin sun cutu mudawo muna dana sani”.
Duk da zuciyar Ammah ta sake raunana sai bata iya sake cewa komai ba, sai ƴan uwan natane ke cigaba da tattaunawa dan na cikin ɗaki ma duk sun fito. Gwaggo Sa'adah ce ta nufi kitchen inda Hawwah ke girka karin kumalon da za'a kai gidan Smart. Cikin sa'a ta iske ta kammala tana kan zubawa ne. “Yauwa kin haɗa ne Hauwa'u?”.
“Eh Gwaggo” cewar Hawwah. Gwaggo Sa'adah ta ce, “Yauwa to sannu, bara na turo su Asma'un suyi su tafi rana nayi”. Da ga haka ta juya ta koma. Ƙwafa Umma dake leƙarsu ta window tayi, jitake kamar ta fito ta shaƙe wuyar Gwaggo Sa'adah. Oho dai tata ƴar aiken ai harta wuce. Kafin kuma su isa ta tabbatar Hydar da matarsa sunci nata abincin. Tai wata ƴar dariyar gatsa-tsa tana barin window ɗin har ɗiyarta Ismaha na kallonta. Amma sai ta basar dan tasan wacece Ismaha da ɗan banzan jan wa'azin tsiya.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣1️⃣