← Book details Furar Danko Part1 Compete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 111

Sashe 47

Furar Danko Part1 Compete Hausa Novel · about 5 min read

      Fitowarsu tayi dai-dai da shigowarsa gidan. Kamar ko yaushe sanye yake cikin ƙananun kaya da sukai matuƙar amsar jikinsa. Ƴar ramar da yay ta ciwo ta sashi zama wani fayau da shi a idon mai kallo. Cikin girmama juna ya gaisa da su baba maigadi sannan ya ƙaraso inda suke tsaye. Anan ɗin ma da girmamawa ya gaisa da Daddy da Uncle Yousuf. Lulu da ke gefensu tana danna waya tai jiran jin ya gaisheta amma sai taji shiru. Karo na farko ta ɗago idanunta ta kallesa tana mai sake tsuke fuska. Ƙoƙarin barin ma wajen yake alamar ita bazai gaisheta ba kenan. Wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ne da takaici ya shaƙure mata wuya har taji tama kasa yin magana, sai dai yanda take binsa da wani mugun kallo ya sa Daddy farga da ita. Ya kuma fahimci miya fusatata ɗin.
      “Aliyu!”.
  Yay kiran sunan Smart da ke ƙoƙarin komawa inda su baba maigadi suke. Cikin girmamawa ya amsa yana mai juyowa garesu. Uncle Yousuf da ya sha jinjin jikinsa da tunanin ɓaranɓaramar da Yayan nasa ke shirin yine yay saurin faɗin “Am yaya inaga muje na ajiyekan tunda malam Zaidun bai dawo ba, in yaso daga can sai ya sameka Office ɗin. Aliyu zuwa 1:30 ku samemu a Nasarawa G.R.A please karku makara”.
        “In sha ALLAH Alhaji”.
     Smart ya faɗa cikin gyaɗa kai abubuwa da yawa na masa kai kawo a rai musamman da Uncle Yousuf ɗin ya ambaci Nasarawa G.R.A. Huci ya ɗan furzar kaɗan, a yanzun ma dai bai kalla inda taken ba ya nufi motar da mai wanki keta faman gogewa alamar ita zasu shiga. Baya ya buɗe mata, batare da ya jira tazo ta shiga ba ya koma mazaunin driver ya shiga yana karanto addu'ar shiga abin hawa. Harta ƙudiri aniyar ƙin shiga, sai kuma mita tuna oho mata ta tako cike da yauƙin nan nata da yanga ta shiga. Mai wanki ya maida motar ya rufe yana jera mata addu'ar dawowa lafiya. Motar yaja suka fice, zuciyarsa cike taf da abubuwan da suka faru jiya a waya tsakaninsa da Uncle Yousuf....
       A daren jiya bayan ajiye motar Mawaddat da ya kai sakatariyarta Zainab gida shima gida ya koma abinsa. Kai tsaye wajen Abba ya nufa suka gaisa, sun ɗan taɓa hira da Abban sai dai hirar batai masa daɗi ba sosai kasancewar da ga maganar Hawwah ta juye maganar aurensa. Sosai Abba ya dinga zuba masa faɗa akan infa har bai nemo matar aure ba a cikin watannan tofa shi zai nemo masa da kansa duk da ba aƙidarsa bace yima ƴaƴansa auren dole. Haƙuri shi dai yayta bashi da tabbatar masa cewa in sha ALLAHU zai kawo matar auren nan kusa. Kamar Abba ya gamsu da hakan sai kuma shigowar Umma ta sake saka Abban hayewa sama. Dan kamar wadda dama take a laɓe tana saurarensu tana shigowa sai kawai ta shiga assasa wutar kan cewar shi dai baiyi niyyar yin auren bane kawai. Inba haka ba baga yarinyar maƙwaftansu ba nan Nazifa yarinyar na matuƙar sonshi amma yaƙi saurarenta. Kallonta yay da mamaki, dan kowa dai yasan wacece Nazifa a anguwar. Yarinya ce mara jin magana dan tsabar bleaching fuskarta har yellow takeyi. Tabbas Nazifa ta jima tana nuna masa soyayya, sai dai shi bai taɓa nuna yasan mi takeyi ba. Kai shi ko magana tai masa ma da ga gaisuwa bai sake kulata. Wannan halin watsar da ita ɗin da yake yi yasa tun tana juriyar bibiyarsa har tai fushi ta daina kulashi. Amma da har abubuwa take saye ta aikoma Ammah ko ta bama su Asma'u. Nan ɗin ma dai bata samu nasarar ba dan Ammah tace ita babu ruwanta, idan yaga zai aureta bazata hana ba, za kuma ta bisu da addu'a dan koba komai yayi jihadin raba Nazifa da rayuwar banza da kowa ya shaida tanayi. Yanajin Ammah ta bada goyon baya ya samu Nazifa yay mata gargaɗi na ƙarshen ƙarni ya kuma yima Yayanta magana akan ta fita sabgarsa, shi kuma Yayan yaji haushi ya gaggaya masa magana  bai kulashi ba shi dai dan ya yanke magana. Da ga ranar bai san miya faru ba bai sake ganin Nazifa ba. Amma shine dan tsabar sharri Umma ke tisa zancen a yanzu bayan shekara kusan uku kenan da ajiyesa gefe. Tuni Abba ya ƙara tujaresa da faɗa amma baice komai ba akan Nazifa, hasalima ya fahimci kamar faɗan nasa na son zama zargi ne ko minene bai dai fahimta ba. Jiki a sanyaye ya baro wajen Abba, ɗakinsa ya nufa dan bai buƙatar zuwama Amma a wannan yanayin. Ya gama cire kayansa kenan zai shiga wanka kira ya shigo masa. Yayi mamakin ganin Uncle Yousuf, sai da ya kalli agogo ƙarfe kusan sha ɗaya da rabi fa. Haka dai ya daure ya ɗaga cikin taraddadi.........✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣7️⃣
Chapter 47 · 0% Book details