Sashe 107
Furar Danko Part1 Compete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar bazata tanka masa ba sai kuma tai murmushi. “Sai dai idan yau zaka aurota ko gobe kafin cikar jibi da zan ƙara gaba maybe wasu su kalleta a matsayin hakan”.
Murmushi kawai ya saki, maimakon cewa wani abu akan batun nata sai cewa yay “Bani furar da Ahmad ya kawo Please dan yunwa nake ji”. Kamar bazata je ɗin ba sai kuma ta miƙe. Babu jimawa ta dawo da furan da kofi ta ajiye masa ta koma inda ta tashi. Television ta kunna shi kuma ya zuba furar ya fara sha.
“K mi kika ci?”.
“Ba buƙata”.
Ta faɗa a takaice.
“Okay amma da kinsha furan da ga gidan Ammah ya amso ta”.
Ɗagowa tai ta kallesa. Sai ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa.
“Gama ka bani kofin bana jin sake tashi”. Ta faɗa tana maida kanta ga wayarta. Bai sake magana ba har ya gama ɗin ya zuba mata, sai dai bata da yawa dan haka ya miƙe da kansa yaje kitchen ya sake ɗakko wata ya ƙarasa cika kofin ya miƙa mata. Hankalinta nakan waya take shan furar harta shanye, sake ƙarawa tai. Sai da ta shanye ta biyun yay ƙaramar dariya da faɗin, “Babu wata furar Ammah da kika sha yarinya a titi ya sayota”. Da sauri ta kallesa tana yamutsa fuska, ya sake sakin dariya da nuna mata 8-10. Filo ta ɗauka ta jefa masa da yin ƙwafa tana harararsa, sai kuma ta fara ƙaƙarin amai shiko ya cigaba da dariyarsa. Kofin takai kitchen ta wanke dan bata ƙaunar ƙazanta, duk da kuwa aikin na cimata rai dan ma yana ƙoƙarin taya ta ne, tun tana ƙorafin mai aiki har ma ta bari tunda dai taga kwanakin sun ƙare mata a gidan. Falon ta dawo ta cigaba da ɗan kallon abubuwa a TikTok. Shiko yana kwance shiru ya zuba mata ido ta ƙasa kawai yana kallonta. Kiran sallar magrib ne ya tadasu su duka. Smart ya wuce massalaci ita kuma ta tafi ɗaki. Bai jimaba ya dawo gidan saboda abinda ke damunsa ba wai ya gama sakinsa bane gaba ɗaya, jarumtar da ya saba ce kawai ta dannewa. Bai samu Lulu a ɗakin ba dan itama tana nata ɗakin a cikin makamancin irin nasa yanayin koma ace wanda yafi nasan. Dan wani abu ne ke faman ratsa mata jiki mai ban mamaki. Ga tsigar jikinta sai faman tashi take kamar mai jin sanyi. Al'amarin kamar wasa sai ya fara neman fin ƙarfin Lulu, dan da ƙyar ta iya tashi tai sallar isha'i........✍️
😵💫Lulun mu muya hwaru kuma🥲?
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣6️⃣
........Tana idar da salla falo ta koma a daddafe, a ganinta ko zata samu sassaucin abinda takeji ɗin, sai dai kamar ma ana ƙara iza mata wutar masifa ne a cikin jininta. Saman 3sitter ta haye tare da dunƙule jikinta waje ɗaya tana jin hawaye na ciki mata ido. Ta rasa wannan wace irin masifa ce haka mara daɗin kwatance.
Ana idar da salla shima Smart gidan ya nufo, dan har yanzu ba wani ƙarfin jikinsa yake ji ba, tunda ya shigo falon idanunsa suka sauka a kanta, ya ɗan yi jimm yana kallonta kafin ya ƙaraso ciki sosai yana ambatar sunanta. Bata motsa ba, hakan ya sashi fahimtar babu lafiya. Har inda take ya ƙarasa, ya kai zaune a kujerar da take yana mai leƙa fuskarta. Hankalinsa ne ya tashi ganin tana hawaye.
“Ya Salam kuka kuma? Baki da lafiya ne?”. Yay maganar yana riƙo hannunta data dafe cikinta, gaba ɗayanta ya ɗago zuwa jikinsa, sake shige masa tai cikin yanayin kamar mai rawar sanyi. Hakan sai ya bashi mamaki dan ba halinta bane hakan sam kusanta kanta da shi, sannan bai manta da gargaɗinta na ɗazun akan karya sake taɓata ba. Jin yanda tama kanannaɗe masa a jiki tana shashshekar kukan da ke ratsa masa zuciya ya sashi kasa iya cewa komai. Kusan mintina uku suna a haka kafin ya ɗago fuskarta dake kwance saman ƙirjinsa hawayenta na sauka masa, itama ɗagowa tai a hankali suka zubama juna ido cikin wani yanayi mai wahalar fassara. Hannunsa ya ɗaura saman fuskarta cikin ɗan lumshe idanu da buɗewa ya furta, “Mawaddatan'warahmah!”.
“Uhhmyim”.
Ta amsa shi acan ƙasan maƙoshi tana lumshe idanunta hawayen da suka sake cikashi suka zubo. Jiyay gaba ɗaya hankalinsa ya sake tashi, cike da damuwa ya ce, “Har yanzu kina fushi da ni akan abinda ya faru shiyyasa kike kuka ko?”.
Idanunta da sukai mugun canja launi ta sake buɗewa sosai a kansa, fuskarta a ɗan taɓe kamar mai son sakin kukan shagwaɓa ta girgiza masa kai.
“To mike damunki? Ko baki da lafiya?”.
Maimakon bashi amsa sai ta kamo hanunsa ta ɗaura a saman cikinta. Kallon cikin yay da sauri, sai kuma ya dubeta da faɗin, “Yana miki ciwo ne”. Kamar ba Lulun nan da ya sani masifaffiya ba, ta ƙara manna hannunsa akan cikin nata muryarta data koma can ƙasan maƙoshi na ƴar rawa-rawa ta ce, “Hydar yan....” sai kuma ta kasa ƙarasawa kawai ta sakar masa kuka. A karo na farko gabansa ya faɗi, ya kamata zai tayar yana faɗin, “Kinga tashi muje asibiti”. Girgiza masa kai tayi da sake nannaɗewa a jikinsa tare da kai hannunta saman gashin da ke kwance a fuskarsa luf-luf ta zubawa lips ɗinsa idanunta da sukai matuƙar juyewa fiye da yanda idan tasha kayayyakin ta sukeyi. Sororo yake kallonta, dan wannan kam shi shaida ne ba ɗabi'a ce ta ta ba. Yanda ta motsa ƴan yatsunta cikin gashin sajensa ya saka tashi tsigar jikin yamutsawa, tare da harbawar zuciya, abinda ke ƙoƙarin lafawa da ya girgiza ƴan maza a yinin na yau na ƙoƙarin zaburowa. (Anya ba wani abu daya fi ƙarfin kan yarinyar nan ta sha ba?) wani sashe na zuciyarsa ya ayyana masa, sai kuma yaji hakan bai kama hankali ba... (To mike faruwa?) Ya sake ayyanawa, sake ji yay zuciyarsa ta motsa, dan kuwa kalaman Ahmad na daren jiya ne suka shiga maimaita kansu a kwakwalwar sa, sai kuma furar da suka sha, tabbas akwai alamar tambaya... Saukar lips dinta saman nasa a bazata ya katse tunaninsa, sai riƙon da tai masa mai lafiya daya sakashi yin baya gaba ɗayansa ya zube a kujerar.....
Dama mai neman kuka ne aka jefa da kashin awaki, kuma kamar Lulu ta kawo kuka ne gidan mutuwa. Sai ya kasance ita da aka saka a tarko ma ya fita rikicewa. Ganinfa ƙurar yaƙi na neman fara tashi a muhalin da bai kamata ba bai ma san lokacin da ya bar falon da ita ba zuwa bedroom ɗinta ba.....
Sai da ya gama tabbatar da ta shiga hannu fiye da yanda yake buƙata, duk da harga ALLAH bada saninsa ta sha abinda ya kaita ga miƙa wuyar ba cikin sauƙi. Gashinta da ke cikin ribbon ya wargaza tare da duƙo fuskarsa gab da tata suna kallon juna, murya can ƙasa kamar zai saki kuka ya furta, “Kin yarda Aliyu Hydar ya zama Mawaddat? Mawaddat ta zama Aliyu?”.
Shiru kamar bazatace komai ba, sai kuma ta ɗan buɗe idanunta data lumshe a kansa itama, so take tai nazari akan maganar tasa amma ta gagara samun kowace irin dama daga gangar jikinta zuwa ƙwaƙwalwa, sai ma hannunta ta ɗaura akan nasa tana girgiza masa kanta. Itama acan ƙasan maƙoshi ta ce, “Ina jin shakku”.
“Kar kiji shakkar komai, Aliyu na *_SONKI_*, yana kuma buƙatar ki matsayin uwar ƴaƴansa abokiyar rayuwa ta har abadan Mawaddatan'warahmah. Na miki alƙawarin bazaki taɓa dana sanin zama mallakin Aliyu ba, in sha ALLAH sai na nunama duniya Mawaddatan'warahmah ba Lulu da suke kallo kawai bace akwai wani babbar nagarta tattare da ita”.
Murmushi ta saki mai ɗan sauti ta buɗe idanunta data sake rufewa suka zubama juna ido. “Mi kake nufi Aliyu?”.
“Baki LABARI kawai zai baki, amma gangar jiki tabbatar wa zatai kafin zuciya ta amayar da sirrin da ke cikinta. Alƙalamin ƙaddara ya jima da bushewa Mawaddat, hakama takardu sun daɗe da ɗaguwa. Miya rage garemu? ƙarasa zuwa filin yaƙin da zai bayyana Aliyu mijin Mawaddat ne kawai domin hutar da zukata masu farautar igiyar da UBANGIJI ya riga ya gama ƙadarta ƙulluwarta tun kafin haihuwar mu.....”
“Bana gane zance a curkuɗe ka buɗemin kawai Aliyu, kana saka ni a duhu da dogon nazari a duk sanda ka ɗauki wannan tsagin na curarrun kalamai”.
Goshinsa ya kai saman nata, hancinsa na gogar nata suna shaƙar numfashin juna. Ya saki murmushi mai sauti. “Ki bani damar baki gaba ɗayan kundin curarrun kalamai na, ni kuma zan kasance miki malami mai fassara miki su feji bayan feji a mabanbanta zangunan da masu neman ilimin kan jima basu cimmawa ba Please Mawaddatan'warahmah, na fara gazawa, ni kuma bana buƙatar shiga makarantar da babu shaidar samun damar ɗaukar darasi a cikinta, dan zata kasance min tamkar ɗan yawon buɗe ido ne kawai”.
“Mi kake buƙata da ga gareni?”.
“Yarda”.
“Karka zama bahagon malami”.
“Ki zama ɗaliba mai kaifin basirar ƙarɓa da haddacewa, domin ranar amsar sakamakon jarabawa ki ɗauki first class”.
“Jarumta da kaifin basira a jinina suke”.
“Ni mai yarjewa ne ga dukkanin furucinki, domin tabbatar miki da hakan muje matakin farko na tabbatarwa *_ALJANNAR DUNIYA TA_*”.
Saukar lips ɗinsa akan nata ya hanata damar furta abinda ta so faɗar, hannu biyu ta amshesa kasancewar ita a karan kanta bata sana wacece ita a wannan fagen yaƙin ba. Abinda kawai ta sani gangar jiki da zuciya duka sun karɓa saboda hakan ne mafi ƙololiwar miradinsu a wannan gaɓar bisa tirsasawar abinda tasha batare da sani ba. Al'amari fa kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba, dan su duk biyun cikin mata kai kowa ya fara kaima ɗan uwansa hari irin na ƙasa da ƙasa. Kafin kace mi sun birkice ma juna daga haka fa labarin ya canja a yanda su duka ba haka sukai tunanin rubutuwarsa ba, dan kuwa dai tabbas wannan daren yazo ne a bisa rubutun alƙalamin ƙaddarar da basu isa canjata ba koda ace sun so hakan. Lokacin da al'amari yay nisan zango Lulu ta fara dawowa a hayyacinta da fahimtar mike shirin faruwa. Sai dai me, Smart ya kai matakin da _Uranium_ ya ke shirin jefawa fa a ƙasarta ba nuclear bomb kawai ba.