← Book details Furar Danko Part1 Compete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 111

Sashe 44

Furar Danko Part1 Compete Hausa Novel · about 7 min read

      Tun bayan wucewar Uncle Yousuf da ya maida Mawaddat ɗakinta batare da ko ɗaya a cikin ƙannenta ya ganta ba shima ya shige nasa ɗakin ya kulle kansa dan samun damar yin isasshen tunani. Ƙarar wayarsa ce ta katse masa dogon lissafin da zuciyarsa tai nisa a yi. Jawota yay cikin jan ƙaramin tsaki zai kashe yaci karo da sunan _Baba garko._ Tashi yay zaune sosai, sai dai bai ɗaga ba har sai da ta yanke shi yay kiransa. Dan haka dama yake masa. Cikin girmamawa ya gaida ogan nasa kuma surukinsa. Da kulawa Baba ya amsa. Ta re da faɗin, “Isma'il ko ka fara barci ne na tasheka amin afuwa. Na kasa haɗiye abin farin cikin nan ne shiyyasa na nemeka yanzu ɗin. Ashe baƙon da kake maganar ɗazun na gida ne.....”
       “Baba baƙo kuma?”.
    “Eh baƙo mana Isma'il. Mai auren Mawaddat mana. Dan yanzu nan suka wuce su sarakan zumuɗin ma sun kasa haƙuri har sun kawo kansu. Ko kuma ja'irar ƴar taka ce ta turosu ma dan kasanta da gaggawa”.
    Sosai ƙirjin Daddy ke lugude. Duk da shi sam yama kasa fahimtar Baba ɗin yanda ya kamata. Kasa jurewa yay dai yace, “Baba kai min afuwa. Wlhy ban gane akan wa kake magana ba. Dan inada tabbacin Mawaddat bata turo kowa ba kasancewar ma ni bamu zauna magana ba dan na sameta kwance a gida ma kanta na ciwo tun bayan ɗakkoka airport”.
          “Tofa wata sabuwa kenan? Su Alhaji Baita ne fa suka sameni a daren nan kan wai Hon. Haruna Dauda Nakowa na son Mawaddat har ma sun dai-daita kansu kaima kuma kasan maganar ma. A yanzu haka ma na basu damar dawowa a gobe idan ALLAH ya kaimu da shirins.....”
     Cikin suɓutar baki Daddy ya furta, “What! Su Alh. Ɗan-kande Baita fa kace baba?”.
        “Eh ƙwarai su ɗin fa na faɗa Isma'il. Shin akwai matsala ne?”.
    Yawune ya nema sarƙe Daddy, da ƙyar ya iya figo glass cup ɗin ruwa dake a bed side drawer ya kwankwaɗa. “Baba ni wlhy bamma san akwai wata alaƙa tsakanin Mawaddat da su Alhaji Baita ba sam. Sannan kuma bana jin ita ɗince ma ta turosu. Dan yaron da take so ɗin wanine daban”.
         “Ikon ALLAH to mi hakan ke nufi?”. Cewar baba. Daddy da takaici da damuwa suka lulluɓe a lokaci guda ya ce, “Baba wlhy ban san manufa ko dalilinsu nayin duk hakan ba. Danni nasan Mawaddat bata da wani alaƙa da su”.
     “Uhhmm to kaga ina ganin mu ajiye maganar nan to. Amma ka tabbatar gobe idan ALLAH ya kaimu a  wajen taruwar meeting ɗin nan kazo min da Mawaddat, idan ma zai yiwu harda shi wanda take so ɗin”.
      Godiya Daddy yay masa. Yayinda tuni yay jagaf da zufa. Kamar wanda ya fito a wanka. Gaba ɗaya lissafinsa ya rushe shi yanzu ma baya gane komai ma. Wayar ya ɗauka yay kiran Uncle Yousuf. Ba'a ɗaga ba sai da tai gab da tsinkewa. Ko sauraren tambayar da Uncle Yousuf ɗin ke masa bai yiba. Sai ma katsesa yay da faɗin, “Yousef akwai matsala. Tabbas akwai matsala. Amma ka jirani ina zuwa gidanka ɗin yanzu”.
    “Haba-haba yaya da kanka. Inaga ka jirani kawai gani nan zuwa”.
    “Karka damu Yousuf kai dai ka jirani kawai. Nan ɗin zaifi sirri ”.
   Babu yanda Uncle Yousuf ya iya dole yabi umarnin nashi yay zaman jiransa. Mintinan da basu wace goma sha ba sai ga Daddy ya iso..........✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣5️⃣

.......A harabar gidan ya sami Uncle Yousuf ɗin tsaye da alama shi yake jira shima. Ciki suka shiga har falonsa. Tsaf daddy ya kwashe ya sanar masa da duk abinda surukinsa kuma ogansa ya kira shi yanzu nan. Karan farko shima Uncle Yousuf ya girgiza. Duk da sam bai gane ainahin manufar shiga Daddy a ruɗani ba. Kwantar masa da hankali Uncle Yousuf ya shiga ƙoƙarin yi, amma sai Daddy ya dakatar da faɗin, “Yousuf bamu da wani lokaci isashe. Minene mafita. Dan wlhy wlhy kaji na rantse maka. Suma da wata manufa sukaje ga baba, kuma lallai dole akwai wata a ƙasa ...”
      “A ƙasa kamar ya?. Nifa yaya ƙara dilmiyar dani kake wlhy akan al'amarin nan, sannan ka fara bani tsoro. Dan ALLAH ka bani abuɗe mana ko zanfi sanin makamar riƙewa ta ƙwarai”.
         “Zan baka amma ba yanzu ba Yousuf. Yanzu hanyar kuɓutar da Mawaddat da mu kammu gaba ɗaya kawai ya kamata mu nema dan ALLAH. Idan ba haka ba komai zai canja da ga yanda muka sanshi zuwa a yanda bamuyi zato ko tsammaninsa ba. Miye mafita? Wa zamu kai matsayin miji ga Mawaddat? Dan fa dole ne mu samar da wannan mijin saboda Baba baya magana biyu. Sannan duk waɗan nan mutanen suna da tasirin da zai iya zartar da hukuncin basu Mawaddat ko ina so ko bana so musamman akan abinda ya faru a baya da kuma gargaɗi da sharaɗin daya shimfiɗa mata kan duk wanda yazo neman aurenta zai bashi kota yarda ko bata yarda ba”.
      “Hakane yaya, sai dai yanzu mu a ina zamu iya samo miji? Sai nake ga ya kamata itama Mawaddat ɗin mu tuntuɓeta ko?”.
         “Tuntuɓar tata yana da amfani, sai dai kuma zuciyata na raya min wani abu. Mizai hana mu jefa tsuntsu biyu da dutse ɗaya ne”.
    “Okay yaya kamar ya kenan?”.
“Yauwa abinda nake nufi anan itama mu barta a rufen kawai mu samar da mijin amma na bogi dan fatana kawai mu nunasa ga Baba dan abar zancen, ita kuma mu nuna mata hukuncinta kenan akan wannan halayyar tata, sai ta gama wajiguwa matuƙa sannan mu faɗa mata gaskiya mu kuma bata damar fidda mijin da take so. Amma yaya ka gani kai?”.
          Uncle Yousuf da shima ya gama tsara nasa tunanin tun fara maganar yayan nasa yay wani shegen murmushi da faɗin, “Tabbas hakan yayi, kuma ina ganin mutum ɗaya ne zai iya mana wannan aikin, sai dai maganar riƙe hakan matsayin hukunci gareta ko barazana bazai taɓa canja abinda muke fatan canjuwarsa ba da ga gareta. A halin da Mawaddat ke ciki canjata na nufin bin wasu matakai daki-daki dan tayi nisan da ƙyamatar ta ko mata hargagi bazai kasance hanyar gyarata ba”.
    “Na yarda da kai auta, shiyyasa akoda yaushe nake kasancewa a farin ciki da ƙwarin gwiwa idan kana a kusa da ni. Amma wanene shi ɗin?”.
       “Aliyu drivern ta Yaya”.
     Da sauri Daddy ya ce, “Haba Yousuf driver fa? Ina mudai samar da wani mai darajar da tafi tashi ko cikin yaran abokaina haka ko a cikin ma abokanka”.
          “Yaya kenan, amma karka manta fa cewa dai ba auren za'ai ba. Zamu samar da mijin ne kawai dan ai mata kurari sannan mu toshe waccan damuwar da aka kasa a teburin Baba. To indai hakane ai kuwa shi wannan da kake ganin bai kai ba ne dai-dai da wannan shirin namu. Amma waɗan can zasu iya zamar mana ƙarfen ƙafa, shi kaɗai ne makamin da zamu riƙe, inada yaƙinin zai taimake mu wajen yakin nan har muci nasara”.
       “Eh kuma fa haka ne gaskiya Yousuf na fahimceka kuma. Yanzu minene mafita?”.
        “Karka damu bar komai a hannuna. Kai dai ka zama cikin shiri kawai itama Mawaddat ɗin ka barni da ita, ka koma kawai gefe ka zama ɗan kallo”.
     Sosai daddy yaji nutsuwa da kwanciyar hankali. Yanata jerama ɗan ƙanin nasa addu'a da fatan gamawa lafiya kafin su ɗan ƙara tattaunawa yay masa sallama ya tafi. Uncle Yousuf ɗin ne dai yay masa rakkiya kusan har gida. Dan sai da ya ga shigarsa sannan ya juya ya koma yanata sakin murmushinsa da shi jaɗai ya san dalilin kayansa sai kuma UBANGIJI da ke kallon dukkanin motsin zuciyarsa. Koda ya koma gidan maimakon kwanciya sai yay alwala ya nutsu wajen miƙa kukansa da buƙatar neman zaɓin alkairi ga abinda yake ƙudirtawar duk da ba yau ne dama ya fara irin wannan addu'a ɗin ba......

     Tofa Uncle You mi kake ƙullawa haka kaima😂🥱?.

        ★....★
Chapter 44 · 0% Book details