← Book details Furar Danko Part1 Compete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 111

Sashe 11

Furar Danko Part1 Compete Hausa Novel · about 5 min read

      Ammah na zaune su Maryam a gefensa suna cin abinci da kallo film ya shiga da sallama. A tare suka amsa masa da gaishesa cikin girmamawa. Ya amsa musu da kulawa yana kaiwa zaune. Ammah ya gaida da bata haƙurin rashin shigowarsa da safe. Dai-dai nan Maryam ta ajiye masa abinci da fure weter. Ɗakinsu suka shige da abincin dan sun san akwai magana a bakin Ammah. Suna shigewa kuwa ta dubesa da ɗauke kai ta ce, “Lafiya ka fita tunda safe?”.
       Samun kansa yay da faɗin, “Lafiya lau Ammah naje wajen aiki ne”.
        A hankali ta sauke numfashi. “Nasan ba son aikin nan kake ba Hydar. Sai dai mai haƙuri yakan dafa dutse har yasha romonsa. Kafi kowa sanin yanda gidan nan ya koma yanzu, miyasa bazaka sakama kanka haƙuri da mutane ba ka karɓi rayuwa a duk yanda tazo maka. Kowane bawa daka gani akwai irin tashi ƙaddarar, amsarta da haƙuri kuma shine mizanin imani. Zuwa yanzu yakamata ace kun bar mahaifinku ya huta dako ciyar da kune, shekarunsa yaja yana buƙatar hutu na rayuwa dana jiki. Yasha matuƙar ɗawainiya da ku tun kuna ƙanana har girmanku, bai tauye kowannenku ga ilimi ba da ci da sha da kula da lafiyarku har girmanku. A yanzu kune ya kamata ace kun rungumesa shima tare da ƙannenku da suka rage a gabanmu, dan wataran kune zaku maye gurbinmu garesu a yayin da ƙasa ta rufe idanunmu”.
        Gaba ɗaya jikinsa ya ƙarayin sanyi da nasihar mahaifiyar tasa. Idanunsa sun kada sunyi ja, cikin gyaɗa kai da tausasa harshe ya ce, “Inasha ALLAHU Ammah zaki sameni fiye da yanda kike buƙata. Kuyita haƙuri damu kuma kuci gaba da mana addu'a”.
    “Addu'a kullum cikin yimuku muke babu fashi”.
    Sun cigaba da hira da mahaifiyarsa da ƙanensa da suka fito ya nuna musu assagment har zuwa ƙarfe tara da kusan rabi sannan ya fito. Ɗakinsa ya koma dan yasan yanzu Abba ya riga ya kwanta. Sai da yay shafa'i da wutiri ya samu kwantawa, abinda ya faru a yinin ya shiga dawo masa dalla-dalla. Envelope ɗin nan ya ɗakko ya fara dubawa. Takarda ce kawai a cikinsa ɗauke da rubutu mai ɗan tsaho, abubuwan da aka rubuta ɗin ya matuƙar bashi mamaki harma ya rasa wane kalar tunani zaiyi a kai. Shi dai har yanzu babu abinda zai iya ƙaraswa akan Jiƙamshi family na ƙwarai ko akasinsa. In ma akwai abinda zai iya faɗa to maybe akan wannan ballagazar yarinyar ne ta jiya, siririn tsaki yaja saboda tunota da yayi. Takardar ya yasar gefe ya kwanta yana mai lumshe idanunsa dake cike da barci......

    _______________________★

        Washe gari da abubuwa da yawa ya tashi a cikin rai. Mafi girman jagorantar ƙarfin gwiwar sa nasihar Ammah, sai kuma wani dalili nasa akan mutumin jiya da son sanin manufarsa ta haƙiƙa, dan yasan in ma bai amshi aikin ba zai iya saka wani yay masa, shiko duk da bai gama sanin suwaye Uncle Yousuf ɗin ba sai yaji bazai iya sakacin barin ƙofar da za'a cuta musu ba har sai yasan gaskiya a kansu. ƙarfe bakwai da kwata a gidan Uncle Yousuf ɗin yay masa. Yana zaune a gate wajen maigadinsu suna ƴar hira kasancewar mutumin Dattijo ne nutsatstse mai aikinsu ta kawo breakfast. Cikin girmamawa ta gaidashi shi da maigadin. Hannu kawai ya ɗaga mata ya ɗauke kansa. Harta juya zata koma maigadi ya tsayar da ita da tambayar Alhaji ya fito ne?.
      “A'a nadai ji aunty na batun tadoshi an kirata a waya wannan masifaffiyar aunty Lu suke kiranta ko ta gidan Alhaji Babba bata da lafiy.....”
    Bata gama rufe baki ba sai gashi ya fito kamar a ɗan rikice. Tun daga nesa ya ƙwalama maigadi kiran ya buɗe masa gate. Miƙewa maigadin yay da hanzarinsa, hakan yasa Uncle Smart ɗin shima miƙewar ya nufesa. Ganin yanda ya daburce yama kasa tantance motar da ya ɗakkoma key yay masa sallama. Juyowa yay ya ɗan kallesa, har ya ɗauke kai sai kuma ya sake jiyowa.
      “Alhamdullah” ya faɗa yana miƙo masa key ɗin batare daya tuna cewa yanzu fa ba ƙarƙashin su yake ba. Babu musu ya amsa key ɗin, dannawa yay motar tai ƙara, dan haka ya nufeta. Sai da ya dai-daita ta sannan, yana batun fitowa ya buɗe masa yaga ya buɗe gaban motar ya shiga yana faɗin, “Yi sauri Please da alama abun babbane, dan duk ciwon Mawaddat da zai iya saka Aunty Kareema ruɗewa irin haka ba ƙarami bane ba”.
         Gudu kawai ya ƙara batare da yace komai ba dan ba fahimtar akan wa ake maganar yay ba shi dai. Bawani nisane tsakaninsu ba, dan layinne kawai ba ɗaya ba.........✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 🔟

........Ko parking bai gama yi da ƙyau ba Uncle Yousuf ɗin ya fice, ba'a rufe mintuna biyar cikakku ba sai gashi ya fito ɗauke da Lulu yaran gidan biye da shi cikin tashin hankali. Shi ya buɗe masa motar, sai lokacin ma yasan itace. Wani iri yaji a ransa musamman tuna abinda akace game da ita a takardar jiya da Alhajin nan ya bashi. Da wannan tunanin yaja motar suka fice a gidan. Kai tsaye wani babban p-hospital mai suna *_SHIRA'S HOSPITAL_* suka nufa. Yanda aka tarbesu zai tabbatar maka da an san da su. Har yay zamansa a mota sai kuma ya fita yabi bayansu, dai-dai nan suma ƴan gidansu da suka biyo bayan su motarsu ta iso cikin asibitin.
Chapter 11 · 0% Book details