Sashe 98
Furar Danko Part1 Compete Hausa Novel · about 8 min read
Sun ɗan ƙara tattaunawa akan abinda ya shafesu musamman akan Hawwah, kiran sallar isha'i ya sashi tashi ya fita. Bayan ya dawo sai da Ammah ta lallaɓa Lulu da wayo sannan ta yarda su tafi. Yanda take zubama Ammah ɗin shagwaɓa sai Smart ya zama ɗan kallo. Dan mamakin yanda tai bala'in sakin jiki da Ammahn yake yi har irin haka a ƙanƙanin lokaci. Koda tajema su Umma sallama har yanzu akwai alamar takaicin ƙyautukan data raba musu ɗazun a tattare da ita. Dan kusan ma a tashin hankali ta yini, ga surukar jiya-jiya a gida daga zuwa tana neman fara haskawa, yarinya da baƙin wayo. Ai zama bai ganta ba, dan kuwa kamar ta kashe maciji ne bata dare kansa ba kasancewar Lulu matsayin surukar gidan nan na nufin disashe tauraron ƴaƴanta da ake gani sama dana kowa. Oho Lulu ba damuwa da sabgar da ba'a sakata ba gareta, dan haka ita bata wani fahimci mi Umman ke ciki ba, dan ko kallon su Huwaila dake falon batai ba. Haka kawai jininta dana Umma baizo ɗaya ba, da ƙyar ma ta yarda ta biyo Smart ɗin suka shigo da tace yaje ita zata je ɗakin Aunty Amarya ya sameta ya nuna mata dole ta shiga ko'ina suyi musu sallama. Ganin babu wasa a tattare da shi yasata bin nasa badan taso ba. Daga wajen Umma sai ɗakin Mama. Nan ma basu jimaba suka fito, nan ko Mama ta bata alawar madara da Hannatu keyi ta saidawa. Hakama aunty amarya ta bata farar data soya mata da rana har kwano biyu. Aiko taji daɗi tanata godiya. Abba ma sunyo masa sallama ya haɗa Lulu da tsarabar zuma da mazarƙwaila kasancewar sa masoyinsu yana ajiyewa. Sai da zasu shiga napep Maryam ta ajiye mata ledar tsarabar Ammah. Duk sai Lulu taji ƙaunar bayin ALLAHN nan na sake ratsata. Shi kansa Smart yaji daɗin wannan karamci da sukai mata. Kasancewar mai Napep ɗin ɗan anguwarsu ne zai kaisu har gida da inda ma zasuje kai tsaye ya nufi Nasarawa G.R.A dan Smart ya riga ya sanar masa tun kan Lulu ta fito. Ganin inda suka nufo ya sata jin farin ciki, a Napep ɗin suka bar kayan suka shiga cikin gidan na Alhaji Sufi Ado Garko. Sun sami yaran gidan da jikoki da yawa, inda kowa yay musu ca aga yaya Lulun ta koma. Sai kuma suka ganta fes har wani ƴar ƙiba kamar ta ƙara musu ma su a ido. Alhaji Garko dake kallonsu da murmushi ya nunama Aliyu kusa da shi. Maimakon hakan sai ya zauna a ƙasa kusa da ƙafafunsa ya gaidashi cikin girmamawa da tambayar yaya jiki. Da kulawa ya amsa masa da sanya albarka. Dada kam sama-sama ta amsa masa tana masa hararar ƙasan ido Lulu na jikinta lafe. Ya gaisa da sauran wanda suke ɗakin suma, daga haka yaja bakinsa yay shiru sai Baba ya takalesa da magana ko tsokana ne yake ɗan murmushi koya bada amsa a taƙaice. Kusan awansu biyu sukai shirin wucewa, anan ne Dada ke cema Lulun “Ku bari sai anjima mana tunda dai mota ce kuma daga nan guda kukai”. Batare da Lulu ta kawo komai a ranta ba ta ce, “Dada a Napep muke fa, babu daɗi mun barsa a waje kusan awa biyu. Kuyi haƙuri zan dawo gobe in sha ALLAHU”.
A zafafe Dada ta ce, “Napep kuma? To ina motocin naki? Kodan shi baida motar hawan dan bakin ciki irin na talaka kema bazaki hau ba? Kamarki jikar Garko family a garin nan da hawa Napep...”
Yanda Dadan ke maganar a zafafe da ɗaga murya kowa naji ya saka Lulu duban inda Smart yake, sai kuma ta dubi Dada zatayi magana cikin ɓata fuska amma ta dakatar da ita........✍️
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣8️⃣
.......Itama dakatar da itan abinda tai niyyar sake faɗan da tai tana duban Smart da yay kamar baima san akansa ake maganar ba Baba yayi rai ɓace. “Wai miye haka kuma ban son ƙaranta fa. Ke Mawaddat tashi ku wuce gida.”
Miƙewa Lulu tayi kamar yanda Smart ya miƙe babu alamar komai da zaka iya fahimta a fuskarsa. Sai ma kallon Baban yay cikin girmamawa yay masa sallama tare da sauran jama'ar ɗakin. Wasu sun amsa masa wasu ko nata faman taɓe baki ƙasa-ƙasa yanda Baba bazai gani ba. Koda yayma Dada sallama bata kulashi ba, shima kuma bai nuna ya damu ba yay ficewarsa. Suna fita cikin ƙarfin halin rashin jin daɗin jiki Baba ya balbale Dada da faɗa, ta inda yake shiga batanan yake fita ba har sai da ta koma bashi hakuri duk da dai fa ta ciki na ciki.....
Lulu tata satar kallon Smart da tunanin zaice wani abu akan abinda Dadar ta masa amma har sukazo gida baida alamar cewa komai. Bayan ya sallami mai napep ya buɗe musu suka shiga, gaba ɗaya kayan na'a hannunsa har handbag ɗinta ma. Har ɗaki yakai mata kayan sannan ya fita zuwa nashi ya barta da binsa da kallo. Harga ALLAH bataji daɗin abinda Dada tai masa ba. Dan koba komai ita ai daga gidansu take. An kuma girmamata an mutuntata kamar a goyata. Kuma fa duk ta bama Dadan labari a taƙaice amma ta aikata masa hakan. ALLAH ya kaimu gobe zataje sai tai mata magana dan bata son haka. Duk da bata son shi bata kuma tunanin zama da shi bayan na wata ɗayan nan bazata so a wulaƙantashi ba dan itama dai da taje gidansu ba'a wulaƙantatan ba ai. Da wannan tunanin ta shiga wanka.
Shima a can wankan ya shiga, sai dai duk da ya danne abinda Dadan ta masa yay masa ciwo sosai. Sai dai ya zaɓi shanyewa dan koba komai taci darajar Baba. Sannan bazai taɓa wulaƙantata ba kasancewarta kaka ga Lulu. Bayan yay wankan ya fito shafa'i da wutri yayi sannan ya fito. Shayi ya haɗa a kofi biyu ya nufi ɗakin Lulu da su. Kwance ya sameta rigingine ta ƙurama fanka ido da alamun damuwa tattare da ita. Dan ko sallamar sa bataji ba sam. Zama yay a bakin gadon da yin gyaran murya sannan ta dawo firgigit, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya da tashi zaune. Idanunsa ya janye daga kallon ta yana haɗiyar busashen yawun daya tokare maƙoshinsa dan shi yasan abinda idonsa ya gani kasancewar rigar jikinta ta barci ce mai santsi. Itama sai ta jawo ƴar saman rigar data ajiye gefe ta ɗora akan wadda ke jikinta dan ƙarama ce ma da kaɗan ta wuce mata cinya. Taji kunyar ganin nata a hakan amma dai ta basar. Shayin ya miƙa mata shima cikin basarwar, amsa tai idanunta a kansa, ganin babu dai damuwar da take tunanin gani ya sata jan ajiyar zuciya da faɗin, “Thanks.” kansa kawai ya ɗan jinjina mata. Numfashi ta sauke a hankali sai kuma ta sake dubansa da faɗin, “Kayi haƙuri da abinda Dada tayi, ni ban faɗa mata da wani manufa ba. Ita haka take tana da faɗa ne sosai”.
Murmushi yay a karo na farko, sai kuma ya ɗan kafeta da idanunsa da suka canja launi kaɗan. cikin tsokana ya ce, “Wajenta kika koyi faɗa kenan?“. Hararsa tayi da ɗan murguɗa baki. Ya sake sakin murmushi da kai shayinsa baki. “Karki damu ai nima kakatace. Ni ban ɗauki abinda tai ɗin komai ba. Yanzu ma magana nazo muyi”. Bai bata damar sake cewa komai ba akan Dadan ya shiga bata bayanan daya ɗan tattara mata game da case ɗin yarinyar can dake a asibiti, sai kawai ji yay ta rungumesa a bazata. Wani irin mahaukacin bugawa zuciyar Smart tayi, jinin jikinsa ya shiga yamutsawa tsigar jikinsa duk ta mimmiƙe. Lulu da bata kawo komai da wata manufa ba game da abinda tai ɗin ba ta ɗago tare da lakace masa hanci tana kallonsa da murmushi ta kashe masa ido ɗaya. Sai ya samu kansa da sakin murmushi yana mai lumshe idanunsa.
Komawa tai ta zauna da faɗin, “Ashe kana da kirki wani lokacin”. Shi dariya ma ta bashi, sai dai baice komai ba kan hakan ya sake yin murmushi kawai da ɗakko maganar fitarta aiki gobe idan ALLAH ya kaimu ko zai samu daidaiton abinda ke tsikarinsa. Nasiha ya fara mata cikin kwantar da kai da muryarsa data koma ƙasan maƙoshi, tare da faɗa mata dokokinsa akan yanda yake buƙatar ta dinga fita”. Da farko taso daurewa, sai dai jin dokar fita da hijjab har ƙasa ya sata dubansa cikin tura baki ta ce.
“Hijjab har ƙasa? Ni ce zan saka hijjab har ƙasa, impossible hakan ta kasance, idan mafarki kake ka farka. Wai miyasa kai baka so a zauna lafiya ga son nuna ma mutane gadara akan rayuwarsu? Ka mance wannan auren ba aure bane balle ka dinga tursasani yin abubuwan nan. To ni ko auren gaskiya ace nakeyi bazan zama a ƙarƙashin takalmin namiji ya takani ba, idan zamuyi rayuwa cikin kowa yanada freedom fine, balle wannan auren. Please ka bari kwanakin nan su cika muna masu mutunta juna. Ni harka ma ɓatamin rai na”.
Kallonta kawai yake yi batare daya fahimci mima take nufi ba, sai dai baice komai ba harta gama. (karku manta Smart bai san da tsarin auren yarjejeniya ba, Uncle Yousuf Daddy da Lulu kawai ya shuka a haka). Tashi tai ta bar masa wajen ta shige toilet dan bata buƙatar abinda zai ɓata mata farin cikin data samu yau a wajen ƴan uwansa, shima sai ya mike ya fita a ransa yana faɗin (akwai ƙura kenan kuwa gobe. Dan shikam wannan tsarinsa ne, ko yau ma ya barta ta fitane da gyalen dan kawai tare zasu fitan, ya kuma san daga gida sai gida kawai....