← Book details Fatima Bintu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 14

Sashe 9

Fatima Bintu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau kemanin wata guda kenan bansa yaya suraj a idona ba kallo daya zakayi min kagane ina cikin tashin hankali, ga mum ta sakoni a gaba zagin yau daban na gobe daban, tana ta Yawo dani wai nabi bokaye da malamai nayiwa yar uwata kwacen saurayi, wasu sun yarda wasu kuma basu yarda ba. Posting dinmu na NYSC ya fito, ankaini jigawa state, shine Abba da me martaba sarki suka yanke hukuncin zasu sa a dawo dani Gombe, kuma duk da baa posting dinmu private ma'aikata amma su zasuyi magn akaini asibitin yaya nayi service din acan. Sun nemi alfarmar, kuma anyi musu, saidai ance dole sainaje nayi signing, kuma akwai takardun da zan cike. Yaya jafar Abba yasa ya kaini, ana gobe zamu tafi daddare yaya jafar da yaya suraj suna zaune a emir place suna hira saiga text ya fado wayar yaya jafar daga FCT minister cewa yayi approving contract din da ya nema ta gina wasu gidaje guda 12 a metama Abuja, tsalle yaya jafar ya farayi yace alhmdl suraj yace meya faru? Contract din da kasa me martaba ya nemo min a wajen FCT minister ce ta samu, suraj nagode Allah yasaka maka da alkairi, don Allah katayani godiya wajen me martaba, Allah barku da Fatimnka wani lallausan murmushi suraj yayi yace amin, yaya jafar yace au ni na manta ma, kasan kuwa da gobe zankai Fatima jigawa NYSC camp sbd akwai takardun da zata cike, kuma ga tfy Abuja ta tasomin bansan ya zaayi ba, suraj yace ba Matsala, Allah ya kaimu goben ni saina kaita ya jafar yace nagode sosai my Prince.

Maman Aysha
[8/26, 12:53 PM] amina yakubu: 💖💖Fatima Bintu💖
1⃣0⃣0⃣to1⃣0⃣5⃣

7:00am
Na gama shirina tsaf cikin wani lafiyyayen filtex lace jikinsa light pink ne, zanen kuma dark pink,) 100k Abba ya sayomin Riga da siket ne dinkin yayi min kyau sosai kamar a sace ni a gudu na soka dauri, nasa haddadun costume, nayi wanka da turare na dauko dark pink gyale na Dora, sanan shoe&bag suma pink, nan take na fito a pinky lady 😝 sanan na fara dialing no yaya jafar yana picking nace na shirya tun dazu ina shagwaba yace sorry my sis, give me 2 mint nace aha. Muna gama waya ya kira Prince yace friend ta shirya fa yace ina kofar gdn, yace OK bari na fadamata, Allah ya kiyaye yace amin, kirana yayi yace na fito dama munyi sallama da Abba tun jiya kawai saina fice ina zuwa naga wata shegiyar new design din Mercedes Benz 450 fara Sol gashi tasha wanki har daukar ido take, ga tinted glass ne baka ganin na cikin motar saida na Dan Dade ina nazari, sanan na nufi motar ina budewa kamshin designer turaren shi ya daki hancina, sanyi Ac kuma ya biyo baya wani shegen boyel yasa da Ku dinsa zaikai 150k sky blue, anyi mishi lafiyyayen dinki fadin kyaun da yarima yayi ma bata lkc ne, nidai kawai nace tabarakkala masha Allah. Kina batamin lkc husky voice nasa ya daki kunnena, shiga nayi na zauna ina rufe kofar yayiwa mota key muka fara tafiy shiru ba Wanda yayi mgn nace ina kwana lpy kawai yace dani, daga nan shiru ya kara biyo baya sai wakar kabhi kush kabhi gam ce kawai take tashi a motar shiru nayi ina tunani" oh yaya suraj gabadaya ya canja kmr bashi ba, tabbas yanzu ya daina sona, sbd gashi ya fara nuna min halin ko in kula da yake yiwa sauran yan mata, nasha jin mutane suna cewa bashida mutunci, kuma yanada miskilanci da jiji dakai irin na sarauta amma bai taba nuna min ba sai yanzu. Nisawa nayi nace to waima meya hana yaya jafar ya kaini ne? Ashe bansani ba a fili na fada, juyowa yayi yace min meya hanaki ki tambayeshi? Dagowa nayi muka hada ido a zuciyata nace ya salam suraj akwai kyau, gashi Dan dadewar da nayi ban Ganshi ba ya kara kyau ya Kara haske, wato shi hnklnsa a kwance yake ma, ni kuwa ya barni acikin wahala, kodan lefina ne,,,,,dena kallona naji yace, kawai saina sunkuyar da kaina ban kara bi ta kanshi ba har muka isa dutse babban birnin jihar jigawa. Daga cikin garin dutse zuwa camp din ma saida mukayi tafiya me nisa, dake dad din suraj yayi musu waya komai shaf-shaf mukayi ga wani respect da ake bawa yaya suraj kamar shine sarkin kodan sarki me jiran gado ne😀 befi 2hrs mukayi a camp ba muka kammala komai, muna fitowa daga camp warshi ta fara ringing hlo prince Affan gani ina fitowa daga camp yanzu, nanda 15minutes zaka ganni insha Allah, ko me prince Affan din yace sainaji yayi dariya har saida fararen hakoransa suka bayyana, sanan yace is alright angon suhailat saina karaso. Wata haddadiyar unguwa muka shiga me suna area 7 anan dutse, unguwar ta hadu sosai sbd ba karamin gd a unguwar, wani tafkeken gida muka nufa da fadawa sunkai mutun goma a bakin gate din,wani saiyace nan ne gidan sarkin ma, muna shiga Prince Affan ya fito rike da hannun suhailat yana dauke da wata yar krmr baby da ba tafi 6 months ba sai wani smiling suke, gaskiya Sundance da juna sosai, hugging din yaya suraj yayi yace friend sainaga kmr a mafarki, rabonka da garin nan tun bikinmu, shima dariya yayi yace wallahi kuwa friend, banzo naga me sunan Fulani ba suka sa dariya gabadaya, suhailat ce ta kama hannuna muka shiga ciki salla na farayi, sanan muka fito dining cin abinci da baby Fatima a hannuna . mun kwashi girki kam kunsan suhailat itama ba baya bace wajen Iya girki, munsha hira da ita sosai har mukayi exchanging no, ba yanda beyi mu kwana ba, yaya yaki da zamu tafi da kyar aka banbare little faty a jikina suhailat ta bani kyautar lafiyyayun turaruka da Ku dinsu zaikai 50k, mukayi musu godiya muka dau hanya.

[10/14, 9:39 PM] ‪+234 814 518 6542‬: [8/29, 8:24 PM] amina yakubu: 💖💖Fatima Bintu💖
1⃣5⃣0⃣to1⃣5⃣5⃣

10pm
Ina kwance akan gado tunani ya hanani bacci, zuciyata banda zafi ba abinda take, har yanzu na kasa gane Wanda suke kulla min makirci, mahaifiyata ce kawai ta fado min a rai, gaskiya duk duniya baka da kamar Uwa, da ace inada Uwa da ban tsinci kaina a wanan yana yin da nake ciki ba hawaye ne ya fara gudu a kuma tuna, kuka nake sosai kawai sainaji wayata tana ringing ina dubawa naga suraj, ina kallonta har ta tsinke banyi picking ba, tana katsewa ya kara kira da kyar na saita kaina na dauka nace hlo, iam expecting dis Fatima, jikina ya bani kuka kike, ni ba kuka nake ba, kuka kike mana Fatima iam very sure ko abinci baki ci ba don Allah ki daina kukan nan kinji, ai saiki dorawa kanki rashin lpy, dole nayi kuka yaya suraj, idan ka dauke kai da Abba, da yaya jafar ba Wanda ya damu dani, rayuwar da nake acikin gdnmu marar dadi ce suraj, kuma tun ina yar karamata a haka na taso cikin tsangwama da kyara, tun ina jaririya ta bansamu kulawa ta Uwa ba suraj, akwai matsaloli da yawa da suke damun zuciyata Wanda Uwa kadai ya kamata a fadawa, ni kuma banida ita, nasan Abba yana tsananin sona amma ba komai ya kamata na fada masa ba, ko kadan bansan dadin Uwa ba wani sabon kukan ne ya kamani, kuka nake sosai, kawai sainaji ya kashe wayar.
Mikewa yayi daga kwanciyar da yayi, ya dauki farar jallabiya yasa ya kara feshe jikinshi da turare ya fito cikin sadda dan kar mum dinshi ta ganshi, har yaje bakin kofa yaji ance ina zaka da daddaren nan? Yana juyowa yaga me martaba, wallahi dad fatima ce bata jin dadi, gashi Abba baya gari, kuma kasan wanan matar bata kula da ita, to meyasa ba zaka bari zuwa sfy ba, Allah dad idan ban ganta a Daren nan ba bazan Iya bacci ba, murmushi dad yayi yace to angon Fatima Amma karka tafi kai kadai, ka kira su musa dogari su rakaka yace to Allah ya dawomin da yarima lpy, dariya yayi yace amin dad. Saida ya biya ta bakery ya sayo min kaza da ice cream. Waya yayi min yace fito gani a kofar gdnku, hijabi nasa na fito, a falo na hadu da yaya fauze tana zaune tana chtn, Fatima ina zuwa? Prince ne yazo, da tsohon Daren nan? Uhm sai kin dawo. Mini falo muka shiga dashi, yace kinyi mamakin zuwana ko Fatima? Wallahi maganganunki ne sukayi tasiri a zuciyata, tabbas Uwa itace jigon rayuwar da, shiyasa nake masifar tausayinki, amma ki ringa hakuri, Allah ba don baya sonki bane ya karbe rayuwar mahaifiyarki a lkcn da kike tsananin bukatar ta, shi yasan me yake nufi dake, ina ganin shiyasa ya kawo ni cikin rayue nayi miki alkawari zan rikeki a bisa amana insha Allah idan na aureki bazaki kara kukan rashin Uwa ba. Kamo hannuna yayi na zauna a kusa dashi ya bude min ledar naman yace bismilla nace to muci mana yayi murmushi yace ni na koshi, ko saina baki a baki nima 😀 nayi nace aa. Zama nayi naci na koshi ina cikin shan ice cream me martaba ya kirashi a waya da sauri ya dauka yace muna hanya dad, sanan yayi min lallausan murmushin sa me tsada yace zan tafi Fatima nace to, a tare muka mike saida mukaje bakin kofa ya ya tallafo ni jikinsa ya manna min kiss, sanan yace I Luv you, a hankl nace I Luv you too sanan ya juya ya tafi yana dariyar da take kara mishi kyau

Maman Aysha
[8/30, 8:35 AM] amina yakubu: 💖💖Fatima Bintu
1⃣5⃣5⃣to1⃣6⃣0⃣
Chapter 9 · 0% Book details