← Book details Fatima Bintu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 14

Sashe 5

Fatima Bintu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washe gari na tashi jikin yayi sauki, saidai jikina ba karfi. Mum don muna firci da kanta ta kira Abba ta fada mishi banida lfy, aikuwa ya kirani a gigice, nace masa naji sauki, yace to Allah ya kara sauki nace amin. Wuni nayi ina bacci dake yau na fara fashin sallah , ban farka ba sai after 4, ina tashi nayi wanka nasa wasu riga da siket na wani cotton material peach color dinkin yayi kyau sosai sbd wasu sai suce a haka aka saya, bayan na murza dauri nasa sarka da dankunne kawai saina tafi guarding din gdnmu na zauna, iska me dadi tana kadani , ina zaune nayi tagumi banda tunani ba abinda nake, bansan lkcn da yazo ba kawai sai motsin shi naji, ina dagowa mukayi 4eyes saina sha kunu na kawar da kaina gefe, kawai sainaga ya fara dube-dube, ya duba aljihunsa, ya tsugunna yana leka karkashin kujerar danake zaune, sai kuma naga ya fara duba cikin flowers da naga abin yayi yawa sainace wai me kake nema ne? Juyowa yayi da cool voice dinsa yace iam looking for your smile Fatima, bansan lkcn da na saki wani lallausan murmushi ba, kawai sainaji yace yah! I got it. Zama yayi a kusa dani yace Fatima me yasa kk fushi dani? Ni bana fushi dakai, wallahi kinayi Fatima, ko wayata kin daina dauka idan na kiraki, ko ba komai ai ni brodan kine ko? Uhm haka ne, yauwa Fatima to don Allah inaso mu cigaba da zumuncin mu kamar da, sbd wallahi daga lkcn da kika fara shareni zuwa yanzu na shiga wan......is alright naji, shi kenan komai ya wuce, ka tashi daga kusa dani kaje kayi abinda ya kawo ka, karka sani a Matsala, dariya😀sanan yace me nazoyi Fatima? Nace zance kazo yi, wa ya fada miki zance Nazo? Zuwa nayi kawai na dubaki. Yaya fauze ce ta taho da saurinta, daga unguwa ta dawo ko cikin gd bata shiga ba ta ganoshi, shine ta iyo wajen. Tana zuwa yace my Prince barka da zuwa, iam sorry please, tun yaushe kake jirana? Wani Dan iskan smiling yayi yace ban Dade ba, to zo mu shiga ciki, ai tafiya ma zanyi, ko gaisawa fa bamuyi ba, eh karki damu zan dawo da daddare musha hira are you sure? Yes, to shi kenan muje na rakaka. Juyowa yayi ya min wani irin kallo, sanan yace Allah ya kara lpy Fatima, nace amin

Maman Aysha
[8/23, 10:11 AM] amina yakubu: 💖💖Fatima Bintu💖
6⃣0⃣to6⃣5⃣

Washe gari
Lecture safe ne dani, sbd haka da wuri na shiga sch, sai wajen 1:30pm na dawo gida, lkcn da na dawo mum bata nan, sallah kawai nayi ina idarwa bacci ya kwashe ni ban farka ba sai after 3 ina tashi kitchen na shiga nayi jallof din taliya da tasha kayan hadi, sanan nayi paper soup din ostel, dake a pressure cooker nayi dawuri ya dahu. Zuwa 5:30 na kammala komai, kuma har lkcn mum bata dawo ba, Daki na koma nayi wanka na shirya cikin wani maroon and cream color code lace fitted gown dinkin ya amshi jikina fiye da tunanin me krt na murza dauri na shafa powder da janbaki, na gyara dogayen gashin idona, sanan na gyara gashin girata dake inada gashin gira sosai, shiyasa ko jagira banayi saidai kawai nayi shaping dinsa. Littafina na dauko sbd Dr masari ya bamu wani assignment me dankaran wahala, muda ake gani masu kokarin class dinma nema yake ya gagareni. Yaya fauze ce ta shigo dakina taci uban kwalliya, idon nan yasha eye shadow, fuskar nan tasha foundation muna hada ido nayi dariya nace wow yaya fauze kin ganki kuwa, you look so beautiful, thank you my sis, my prince ne zaizo kinga kuwa ai ba zanyi da wasa ba, nace gaskiya ne. Muna cikin hira ya kirata a waya yace yana waje, da zumudi ta tashi ta fita, ta fita befi da 10mint ba sai gata ta dawo yace kizo Ku gaisa nace to, gyalena na dauka muka fita, muna zuwa na gaisheshi yace wato da ban nemeki da bazaki zo ki gaisheni ba ko? Wallahi wani assignment nake me wahala shiyasa, waye ya Baku ? Friend dinka OK kingama ne? Aa, dauko mu nagani nace to, ina kawo masa yace na zauna ya fara koya min ina rubuta wa har na gama, ita kuwa yaya fauze zuba ido kawai tayi tana kallon mu tashi nayi zan tafi nace nagode sosai wani mayattacen kallo ya Bini dashi ina zaki? Nasha kunu zan koma ciki ne ba zaki zauna ki taya sis dinki hira ba? Yaya fauze tace ai shine don Allah ki zauna Fatima, komawa nayi na zauna mukaci gaba da hira amma ni bana mgn sosai motar mummy ce ta sako kai tana packing ta fito da sauri batasan suraj yana nan ba ke Fatima uban me kike anan, kin dora abincin dare ma kuwa? Da sauri nace na gama, be zama dole ace ina raayin abinda kika dafa ba, idan beyimin ba sai kin kara yimin girki sbd haka ki biyo ni yanzu. Suraj ne ya mike ya karasa wajenta yace mum ina wuni, ji tayi kamar ta nutse sbd wata irin kunya data kamata jiki a sanyaye tace lpy kalau Prince, ya yallabai da mum dinka yace suna nan kalau, idan ka koma kace ina gaishe su, yace to zasu ji insha Allah. Juyowa yayi ya kalle ta dama Fatima ce take muku girki a gdn? Kame2 ta fara kawai sai yace is alright ni bari na tafi sai anjima, ko ni ta manta beyi ba a shiga motarsa ya tafi.

Maman Aysha
[8/23, 4:23 PM] amina yakubu: 💖💖Fatima Bintu💖

6⃣5⃣to7⃣0⃣

Tunda daga wanan ranar kusan kullum yarima suraj sai yazo gdnmu, amma saina ki fita mu gaisa kullum da karyar da nake fadawa yaya fauze idan yace ta kirani, saida ya jera 1wk yana zuwa bamu hadu ba, kawai saiya dauke kafa, itama ya fauze ya daina zuwa wajenta yau wajen 2wks kenan bata sashi a idonta ba, kuma idan ta kirashi no bata shiga, hankalin ya fauze idan yayi dubu ya baci ta rasa inda zatasa kanta. Yauma muna zaune a daki muna hira, dake Abba yana gari ba Wanda ya isa ya sani aiki yaya fauze tace Fatima yau sati uku kenan banga my Prince ba, kuma ko a waya baa samun sh, karki sa bacin ran da zai damu zuciyarki ya fauze ki mika al amuranki a wajen Allah, shi zeyi miki zabin mafi alkairi....ai aurena da my Prince shine alkairi a awajena Fatima, wai ke bakya ganin zallar kyaun dayake dashi kamar aljani, ga kudi, kuma ga Uwa uba mulki, kab area Gombe ba Wanda ya kaishi kyau, ko akwai, nace babu, to kinga kuwa ai dole na soshi ko, nace gaskiya ne, ni ina ganin shirye2 bude asibitinsa ne ya hanashi kirana kinsan gobe zaayi bikin bude asibitin da dad dinshi ya gina masa nace OK, Allah yasa a bude a saa tace amin.
Washe gari
Yau ake taron bikin budu makeken asibitin da me martaba sarkin Gombe ya budewa dansa, wato me karatu kaf area Gombe, Adamawa, Bauchi, jigawa, jos da taraba ba inda suke da asibitin da yakai na suraj girma har asibitocin gwamnati, sabd shi kanshi ginin asibitin a USA aka imitating design din, sanan duk wasu injina da ake amfani dasu wajen gano wata cuta a jikin Dan Adam akwai su a asibitin, sanan duk wani lab investigation da ake a Nigeria, kai harma Wanda baa Iya yinsu a 9ja akwai kayan aikinsu a lab din asibitin, kuma sun debi kwararrun maaikata tun daga kan doctors, nurses, pharmacist, lab scientist etc sunkai mutun 500. Me krt idan nace zan baka lbrn SMK specialist private Hosp, space din wayata bazai dauka ba. Gayya sosai akayi sarkuna ne, governors ne, kai harda president of Nigeria, taro akayi sosai, bangaran media kuwa duk gidan television da gidan radio daka bude program din zagaji anayi, masu buga jarida ma ba abarsu a baya ba, masha Allah, anyi taro lpy kuma an watse lpy.
Washe garin ranar da aka bude asibitin muna zaune da yaya fauze sainaji wayata tana ringing, ina dubawa naga bakuwar no ce, a sanyaye na dauka hlo, cool voice dinshi ce ta daki dodon kunnena kin kyauta Fatima, abin alkairi ya sameni ko ki kira kiyi min murna ko? Sauri nayi na matsa gefe a razane, nace sorry na sha'afa ne congrats Allah ya taya riko, ban jira me zaice ba na kashe wayata.

Maman Aysha
[8/23, 5:25 PM] amina yakubu: 💖💖Fatima Bintu💖
7⃣0⃣to7⃣5⃣
Chapter 5 · 0% Book details