← Book details Fatima Bintu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 14

Sashe 12

Fatima Bintu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

4pm
Aunty sakina ta kira yaya fauze a waya tace ki sauri ki kawo abincin sun kusa zuwa tace to. Lkcn da taje gd ya cika da yan Uwa da abokan arziki. Taje befi da 10 mint ba sukaji algaita ta cika gida nan take fadawa suka fara shiga da wasu lafiyyayun akwatina da ban taba ganin irinsu ba, set uku ne ko wanne da kalarsu. Bayan an gaisa aka kawo musu abinci da abinsha sukaci, daga nan aka fara bude akwatuna wato me krt duk wani kalar kaya daka sani, daban aka ware masa akwatinsa misali akwatin Hilton da Sheraton daban, laces ma daban, gown, English wear's etc kowanne daban. Wato zamu Iya kiran lefen da simple but very expensive. Tunda aka fara ganin kayan yan Uwa suka fara guda ana shewa ana son barka har suka gama, saida waje yayi tsit kamar daga sama sai suka ji muryar mum tana cewa aikin banza wanan ai albagazaranci ne talakawa nacan suna Neman taimako amma anzo ana kashe kudi a banza, bayan yar da aka kawowa lefen ma barauniya ce, fauze tayi karaf tace haba mum don Allah wanan wane irin abin kunya ne haka? Ai kyabari bakin su tafi ko, why mum don Allah ta karashe mgnr tana kuka bakin ubanki marar sanin ciwon kai kawai, zo ki fice kona tsine miki, da gudu fauze ta fice tana wani irin kuka. Aunty sakina ce ta kalli bakin tace don Allah kiyi hakuri tanada Dan tabin hankali ne,,,,,bura uba nice me tabin hankalin Dan kutumar ubanki wasu cousin dinta ta kalla don Allah Ku kamata Ku fita da ita, haka suka jata sukayi daki da ita tanata dure duren ashar, sanan ta juyo Dan Allah kuyi hakuri kunsan indai akace kai ya tabu to sai a hankali, sorry for the disturbances pliba 🙏 gyatimar cikin su tace ba Matsala Allah ya bata lpy, mu zamu tafi, 200k aunty sakina ta basu tukici sukayi godiya suka tafi. Suna tafiya Aunty sakina ta shiga dakina ta tattara duk wani Abu da tasan me amfani ne ta hada da kayan lefen ta zuba a motar ta data aminiyarta aunty Halima suka fice suka bar gdn

Maman Aysha
[9/2, 12:49 PM] amina yakubu: 💖💖Fatima Bantu💖
1⃣8⃣5⃣to1⃣9⃣0⃣

Muna zaune nida Dan baffancy da Hajar yayan Aunty sakina suna tamin shirme ina dariya kawai saina ji shigowar su aunty sakina zama sukayi sunata zabga dariya, kawai sai muka zuba musu ido muna kallon su, sai bayan sun gama ta kalle ni tace Fatima munsha drama yau da babarki bakiga haukan da tayi ba, nandai ta debe lbrn komai ta bani. Nima dariya nayi nace Allah ya shiyi mum sukace amin. Na debo miki kayanki, tunda bazan koma Abuja ba sai bayan biki zakici gaba da zama anan na shirya ki, keda ki koma gdn sai ranar da zaa kaiki, don na fahimci wanan matar zata Iya kashe ki idan aka barki a wajenta, nace to shikenan saidai zanyi missing din yaya fauze, tace gaskiya fauze da jafar suna da kirki, Allah ya temakesu basuyi halin uwar ba, saita ringa zuwa nan tana ganin ki ai, tunda ana gari daya
Tun daga ranar Aunty sakina take shirya ni babanmu miliyan Dari ya ware ta hidimar biki wasu mata ta dauko har mutun uku, kowacce da irin gyaran da take min, bunke bunke maganin mata kam nasha harna gaji. Maganar furniture's kuwa dama andade da gamata, sbd Abba yace shine uwata kuma shine ubana, ko nawane zai kashe akaina

Maman Aysha
[9/2, 1:43 PM] amina yakubu: 💖💖Fatima Bintu💖
1⃣9⃣0⃣to1⃣9⃣5⃣

Yau satina guda kenan ban fita ko ina ba suraj ma aunty ta hanashi zuwa saidai a waya. Nayi wani irin kyau na kara fari, skin dina tayi laushi har wani shining din kyau nake. Munyi waya da Abba yace gube zasu taho, sabd rana ya tayo ne daurin auran.
Yauma kamar kullum muna waya da suraj a daki yace Fatima na zama abin tausayi fa yanzu haka ina kan hanyar zuwa Faruk qtrs, yau duk abin aunty saina ganki wallahi, ki tram maxi zuwana nanda 15 minutes kawai ya kashe wayar. Murmushi nayi, sai kuma na mike nayi make up wata English guwn ce ajikina 2 in 1 ta cikin body hug me dogon hannuce blue, saita saman kuma armless red color doguwace har kasa, saina dauki blue gyale na yafa wayyo Allah wato kyaun danayi baa mgn. Ina cikin fesa turare naji sallamarshi bayan sun gaisa da aunty tace wato na hanaka zuwa amma kaki ji ko? Marairaicewa yayi don Allah aunty ki temaka min nayi tozali da ita, yaufa I WK kenan harna fara zama blind dariya tayi to marka Dade yace to aunty nagode. A falon baki ya zauna ina shiga ya taso ya kama hannuna muka zauna waw this is beautiful, Fatima kece kuwa? Uhmmm! Shiyasa aunty take yimin rowarki? Gaskiya kinyi kyau bana wasa ba. Murmushi nayi nace kaima kayi kyaun ai, oh noo Dan dai kin Dade baki ganni ba ne. Mikewa nayi bari na kawo maka....ban karsaba ya katseni basshi bana bukata, ni yau ganinki ya fiye min komai, kafin nazo nan inajin yunwa, amma ina ganin ki naji na koshi, wallahi Fatima na matsu ayi a daura auran nan, murmushi nayi nace ai ankusa gaskiya, wane gari kk so muje honey moon? 😂 duk inda kace, wani lallausan murmushi yayi wai ni yau rowar magn kk min ne? Ko kin fara Jan ajin amarcin ne tun yanzu? Dariya nayi au har akwai wani Jan aji da ake na amarci? Yesss, ahh to ina ganin shi na fara. Jan hancina yayi sily girl, daidai nan wayar shi ta fara kara, hlo mum OK to ina zuwa nanda 15 mint insha Allah. Wani kallo ya watso min zan tafi Fatima, sai munyi waya, wai dad ne yskeson mgn dani yanzu, is alright muje na rakaka saida mukaje yayiwa aunty sallama, sanan na rakashi bakin mota da kyar muka rabu

Maman Aysha
[9/2, 4:28 PM] amina yakubu: 💖💖Fatima Bintu💖
1⃣9⃣5⃣to2⃣0⃣0⃣

Washe gari
Yau da farin ciki na tashi, sbd munyi waya dasu Abba sunce sun taho, wajen 3 months kenan rabonmu dasu sabd nine ma yake danxuwa, amma da sbd mum ne ba abinda zai kawo shi sabd ya tsaneta.

6pm
Ina zaune a daki naga bakuwar no tana kirana, da bazan dauka ba sai wata zuciyar tace na dauka hlo Fatima sis dinki ce takeso tayi miki magana, wai idan kina tare da auntynku ki Matsa, go ahead ni kadaice a dakin, OK gata to tana karba naji ta fashe da kuka fatima bansan wacce irin Uwa na hadu da ita ba, yau kwana Tara bansaki a idona ba, nace zanzo mu shirya events din bikin tace idan na taka kafata a gdn aunty bata yafemin ba, sanan ta karbe wayat, ta hanani zuwa ko ina yanzu ma dakyar na samu na fito, don Allah Fatima ya zaayi mu hadu? Kina ina yanzu? Ina kan hanyar zuwa gdn wata friend dina, ki fito saina daukeki a hanya,OK bari zanzo na sameki yanzu, to amma don Allah karki fadawa aunty wajena zaki, to, Da sauri na dauki baga dina aunty don Allah zanje na karbo sako a wajen wata friend dina, to amma karki Dade Fatima, bazan Dade ba aunty, .
Chapter 12 · 0% Book details