← Book details Fadeelah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 22

Sashe 9

Fadeelah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muhammad shiru ya yi baitanka musu ba.
Alhaji Sagir ya ce "Muhammad, ka yi shiru?" Muhammad cikin gatse dan ya san babu ma wanda za su k'ara ba shi aure ya ce"Daddy, idan an samu wadda zata iya aure na shi kenan babu damuwa na amince"

Jibirin kallan Muhammad ya yi ya ce"Amma kasan Laila na sonka? "

Muhammad da ya tabbatar ma kanshi babu wata wadda zata aure shi ya ce"Idan ta amince babu damuwa Jibirin"

Alhaji Sagir kallan Jibirin ya yi ya ce"Wacece ita yarinyar? " Yarinyar Mansur Inuwa ce" Shiru mahaifin Muhammad ya yi sannan ya ce"Shi kenan ka yi min magana da yarinyar tukun idan ta amince"

Da daddre Jibirin ya je wajan Laila ya sanar da ita abin da ke tafe da shi.Bud'ar bakinta sai cewa ta yi "Allah ya tsareni, wato in je nima a tsotse jinina kamar yadda aka yi ma wa in can" Haka dai ta yayyab'a ma Jibirin magana ta tafi ta bar shi anan.

Jibirin cikin damuwa ya sanar da Alhaji Sagir yadda su ka yi da Lailar.

Muhammad ko ko da ya ji basu k'ara tada mai maganar ba ya san sun je ba a dace ba.

Tun daga ranar mahaifin Muhammad bai kuma yi ma Muhammad zancan aure ba.

KADUNA GARIN GWAMNA

Fadila kullum tana so ta sanar da MD akan ya aiko gidansu kafin mahaifinta ya kuma yi mata maganar, amma zuciyarta ta k'i aminta da shi a matsayin miji a gareta.

Yau dai Fadila ta yi alk'awarin sanar da MD d'in ganin saura sati biyu wa'adin da mahaifinta ya bata ya cika, duk da yanzu taga gaba d'aya MD d'in ya fara jan baya da ita ba kamar da ba.

Yau ne ranar da Fadila ta yi k'udirin sanar da MD ya aiko gidansu.Saidai ko da taje aiki yau da ta gaida shi sama-sama ya amsa gaisuwarta daga nan bai kuma saurarta ba ya ci gaba da abin da yake.Hakan sosai ya ba Fadila mamaki, amma saita bar hakan akan k'ila jamai ran da take yi ne kullum tace mai yau tace gobe.

Fadila cikin sanyi da yanayin yarda ya yi mata ta ce"Na san ni mai laifice a wajanka, amma ya wuce, ina mai yi maka albishir d'in duk lokacin da ka shirya koda ko yaune ka aiko wajan mahaifina"

MD ya dad'e yana kallan Fadila bayan ta kai bayananta, sannan ya kauda kan shi ya ce"Fadila, ina miki fatan Alkairi Allah ya baki miji na gari, babu maganar aure yanzu tsakanina da ke sai zumuminci"

Fadila cikin tsananin mamakin take kallan shi, so take ta yi magana ma amma ta kasa. Sai da ya furta mata haka fargaba ta ci kata idan mahaifinta ya b'ullo mata wuta ya za ta yi.

Fadila cikin murmushin yak'e ta ce"Sir, ko na yi maka wani laifin ne?" Kallanta ta ya yi ya ce"A'a, biki min komai ba, son ne kawai ya fita araina, amma zumincinmu na..."

Fadila bata saurareshi ba ta yi tafiyarta.

Fadila cikin sanyi ta shiga Office dinsu. Jamilu da kallo d'aya ya yi ma Fadila ya fahimci tana cikin damuwa, dan ita Allah ya halicce ta cikin wa inda ba sa iya b'oye damuwarsu.

Jamilu cikin tsokanar Fadila, ya ce"Kowattab'aki zo ki gaya min, in dai a kanki ne ba a iya min, nasha aradu kanki nasha Yasin, akanki zana aika mutum yanzu ko da ko MD ne" Fadila murmushi ta yi ta ce"MD ne ya tab'a ni Jamilu, bana son MD amma abun mamaki wai dan MD yace ya fasa aurena ka ji yarda na ji kuwa?" Jamilu cike da mamaki da al'ajabi ya ke bin Fadila da kallo ya ce"Fadila, ban fahimta ba? Na ji kin zo min da wata sabuwar tatsuniya ne"

Shiru Fadila ta yi tana kallan Jamilu ,sannan ta ce"Na yi mamaki sosai da jin furicin MD dama kuma kwana biyu ya fara sauya min" Jamilu shiru ya yi sannan ya ce " Tabbas wannan abun mamaki ne, da ace bansan halinki ba da sai in ce k'ila ya samu abin da yake so ne, to amma ni d'in nasan wacece Fadila" Cewar Jamilu da al'ajabi ya isai.

Atak'aice dai Fadila haka ta koma gida tana jinta duk babu dad'i. Abu d'aya yake damunta shi ne mahaifinta yana gaf da ya yi mata magana ga shi ta gama sakin jiki da MD d'in akan shi zata aura duk da ba wai dan tana son shi ba.

BAYAN SATI D'AYA

Fadila ta tashi yau bata jin dad'in jikinta haka nan dai taje aiki.Koda ta je bayan sun gama gabatar da Shirin da take ne ta kalli Jamilu ta ce"Jamilu, bari in yi ma MD magana gida zani bani da lafiya" Fadila tana fad'in maganar ta tashi da sunan tafiya, saidai sakamakon jirrin da take gani tana tashi ta yanke jiki ta fad'i✍🏻

📚 FADEELAH 📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

Naga
Fadila Sani Bakori.

SANARWA : Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban-daban da zan kawo muku na gyaran jiki acikin wannan littafi mai suna FADEELAH .

Page 6

Fadila ta tashi yau bata jin dadin jikinta, hakan nan dai ta je aiki, koda ta je bayan sun gama gabatar da Shirin da suke yi ne ta kalli Jamilu ta ce"Jamilu, zan yi ma MD magana gida zani ba ni da lafiya. " Fadila tana fad'in haka ta tashi da sunan tafiya , saidai sakamakon jirin da take gani tana tashi ta yanke jiki ta fad'i"

Jamilu da sauran abokan aikinsu cikin rud'ewa su ka yi kan Fadila da ke kwance a k'asa a sume.

Jamilu fita ya yi ya je ya yi ma MD magana ya sanar da shi halin da Fadila take ciki.
MD Cikin mamaki ya kalli Jamilu ya ce"Jamilu, bata da lafiya ne dama?" Tom, ni dai ban sani ba, sai yau bayan mun gama aiki take sanar da ni bata jin dad'in jikinta za tafi gida, tom ta tashi ne ma da niyyar zuwa ta sanar da kai ta yanke jiki ta fad'i " MD cikin damuwa da halin da aka fad'a mai Fadila na ciki ya ce " Mu je akaita Asibiti a duba lafiyarta"

Da taimakon Firdausi da Ummi aka Fadila a mota, wa inda suma ma'aikata ne a gidan TV , suka tafi Asibitin.

Suna tafiya kafin su isa Asibitin Fadila ta farka , kallan Ummi ta yi wadda take kwance ajikinta, cikin k'asa da murya irin ta marasa lafiya Fadila ta ce" Ummi , Lafiya ? Ina Zamu? " Ummi cikin kwantar ma Fadila da hankali ta ce " Ba ki da lafiya ne shi ne za mu kaiki Asibiti a duba lafiyarki " Fadila shiru ta yi tana mamakin yadda akai haka , Sannan ta ce " Na ji sauk'i MD mu juya "

Ba tare da ya juyo ya kalleta ba ya ce" Ki bari mu je a duba lafiyarki hakan na da kyau"

Koda suka shiga cikin Asibitin Fadila saida ta dafa Ummi saboda tsananin jirin da take ji . MD Ummi ya ba kud'i ta sayi katin Asibitin sannan suka shiga wani Office. Likitar kallo d'aya ta yi ma Fadila ta gano abun da ke damunta, amma sai cewa ta yi" Me ke damunki ? " Jirine kawai sai rashin k'arfin jiki da ke damuna " Cewar Fadila. Kai likitar da jinjina sannan ta ce" Tun yaushe kike jin hakan ? " Tsakanin jiya da yau ne na fara jin hakan " Likitar laboratory Lab ta tura su Fadila blood test.

Cikin kankanin lokaci aka yi ma Fadila awon ta kawo ma likitar sakamakon .

Likitar na dubawa murmushi ta yi ta kalli Fadila ta ce " Kira min mai gidanki shi zan fad'ima ma wannan sakamakon " Fadila murmushi ta yi ta ce" Ba mujina bane Ogana ne , ki fad'in kawai "

Shiru likitar ta yi tana kallan Fadila, Sannan ta ce" Kina d'auke da cikin wata d'aya da kwana kai " Fadila zaro mayan-manyan idanunta ta yi tana kallan likitar ta ce" Likita ciki kuma ? , Kuma ni ? Kai ! ki sake bincikata dai ki gani , budurwa ce ni fa ba ni da aure ! " Likitar kara kallan Fadila ta yi da kyau sannan ta ce " 'Yan mata kina zuwa kallo d'aya na yi miki na gano abun da ke damunki "

Fadila tashi ta yi ta ce" Ina ban yarda ba Wallahi , ciki fa ? Kuma ni ?, to ,ta ya ya?"

MD jin alamun kamar hayaniya tsakanin Fadila da likitar , ya shigo office d'in yana tambayar Fadila Lafiya.

Fadila tsabar takaici kasa ba MD amsa ta yi , sai likitar ce ta ce " Ciki take d'auke da shi, shi ne ta tsaya tana gaddama wai in sake bincike , bacin tunda ta shigo kallo d'aya na yi mata na fahimci abun da ke damunta "

MD rasa abun cewa ya yi ya tsaya yana kallan Fadila kamar wani sakarai , Fadila kuma tsabar takaici kawai sai ta fashe da kuka ba wai dan ta yarda da maganar kikitar ba ne , tana kukan shairin da ta yi mata ne.

Likitar ko ganin haka kallan Fadila ta yi ta ce" Yi hak'uri 'yan mata share hawayanki idan biki yarda ba ko kina ganin shairi na yi miki za ki iya zuwa wani Asibitin a dubaki" Tana fadin haka ta kalli MD ta ce za ku iya tafiya "

Haka suka fito ba wanda ya tanka ma kowa. Ummi ko wadda ta ji duk abun da ke faruwa ita kanta ba k'aramin mamaki ta yi ba.

Fadila da har yanzu jiri take gani rik'e Ummi ta yi da sauri . MD kuma ganin haka ya ce " Kinga ma ko magani ba mu tsaya amsa ba , mu je wani Asibitin a dubaki a baki magani "

Innalillahi wa inna ilaihir raj'un , hankalin Fadila ba k'aramin tashi ya yi ba , lokacin da aka maimaita mata tana d'auke da ciki kamar yadda waccan likitar ta fad'a mata. Abun ka da mai ganin jiri Fadila yanje jiki ta yi ta fad'i wajan asume.
Chapter 9 · 0% Book details