← Book details Fadeelah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 22

Sashe 20

Fadeelah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fadila da bata yi tunanin ma zai d'aga ba take ta rikice , haka dai ta daidaita natsuwarta ta fara magana kamar haka " Assalamu alaikum . Ina wuni " Muhammad adak'ike ya amsa da " Lafiya , bangane wake magana ba ? " Sunana Fadila daga nan Kaduna , ni ce wadda ranar da ka zo taron anniversary namu na haihu ka yi min theater , tom yanzu nan na cikaro da wani posting da abokinka ya yi akan mutuwar matanka , Allah sarki Allah ya yi musu rahama Allah ya sa maka juriya na rashinsu , Allah ya kuma tona ma wanda yake aikata maka haka asiri "

Muhammad sosai ya ji dad'in addu'ar Fadila , cikin jin dadi addu'ar tata ya ce " Ameen ya Allah . Ina yaronki fa ? " Ahmad yana nan ya fara wayo watan shi hudu kenan " Ok ki tura min photonsa ingansa " Fadila cikin jin dad'i ta ce " Tom "

Daga haka Muhammad ya kashe wayarshi.

Fadila kuma take tahau WhatsApp ta tura ma Muhammad pics din Ahmad kala uku .

Muhammad koda ya hau online ya ga pics din Ahmad da Fadila ta tura mai sosai ya yaba mata kyan yaran , dan har yana tonanta da cewe " Za ki ban shi ko ? " Fadila da hawanta Online kenan ta ci karo da sak'on Muhammad, dariya ta yi ta ce " Eh , zan baka , amma kuma ai baka da matar da zata rik'e maka shi " Amma kuma ai ina da mama kinga mamana zata rik'emin saidai in kina min wasa ne ba bani zaki ba " Cewar Muhammad da ya biye ma Fadila .

Fadila ta maida mai amsa da cewa " Kai ma wasa kake ba amsa za kai ba "

"Hmmm, ki bani ki gani " Daga nan Muhammad ya sauka .

BAYAN WATA D'AYA

Fadila watanta d'aya kenan da daina zuwa aiki , inda MD ya dakatar da ita ya ce sai Ahmad ya yi kwari . Saidai kullum sai ya aiko ma Fadila dubu d'ayar da yake bata , yanzu kuma acewarshi ta saima Ahmad Pampers .

Ahmad yanzu watan shi biyar kenan .

Fadila 'yan kwana kan nan jiri take fama da shi da yawan ciwan kai . Dan ma sauk'inta mahaifiyarta da Aisha suke rainon Ahmad .

Fadila yau gaba d'aya kwance ta wuni kuma kusan bata ci komai ba .Mahaifiyar Fadila da shigowarta d'akin kenan ta ce " Fadila , kinga yaron nan kuka yake d nono bai isheshi ba , gashi kin k'i tashi ko wani abun ma ki ci " Fadila cikin murya irin ta mara lafiya ta ce " Mama, jiri nake gani ga ciwan kai dake damuna Allah ji nake ko zama bana iya yi " Tom ki tashi ko chamise d'in kusa damu din nan ku je Aisha ta rakaki a baki magani mana " Tom bari Aishar ta dawo "

Bayan Aisha ta dawo ne ta raka Fadila chamise .

Lokacin da suka je za su shiga chamise din kenan Aisha ta had'u da wata k'awarta hakan ya sa Fadila kad'ai ta shiga . Fadila ba yani ta yi ma mai chamise d'in na yadda take ji . Kallanta ya yi ya ce " Madan anya ko ba ciki gareki ba ? " Fadila a furgice ta d'ago dara-daran idanunta tana kallan shi a furgice ta ce " Ciki kuma ! ? " Tabbas , amma zaki iya zuwa Asibiti dan tabbatarw..." Tom shi kenan na gode sai anjima " Fadila ta ce haka sakamakon Aisha da ta shigo.

Aisha kallan Fadila ta yi yadda ta fita da sauri kuma yanayinta gaba d'aya a furgice take . Aisha da mamaki ta k'ara sauri ta iddo Fadila tana cewa " Aunty Fadila , Wai lafiya ? " Eh ce min ya yi ciwan kaine da jiri ke damuna " Aisha da mamaki ta ce " Dama ai akan abun da muka je kenan yana damunki ina ? " Eh ,haka suka ce " Aisha da mamaki ta bi Fadila da kallo dan gaba d'aya ta rud'e maganar ma kamar bata san me take cewa ba .

Aisha da bata kawo komai a ranta ba , haka suka tafi ba tare da ta k'ara magana ba .

Koda suka shiga gida mahaifiyar Fadila tambayar Fadila ta yi ta ce " Me ke damunki ne ? " Jiri ne da ciwan kai kawai " Fadila ta fad'i maganar a furgice dan ta rud'e sosai da jin cewa tana da ciki.

Mahaifiyar Fadila ta ce " Sun baki magani ko ? " Eh, cewa sukai jiri ne da ciwan kai " Mahaifiyar Fadila da mamaki ta bi Fadila da kallo jin tambayar da ta yi mata daban da amsar da ta bata , haka dai ta kuma cewa " Fadila ! Cewa na yi sun baki magana ni ? " Mama , Allah ciwan kai ne " Fadila ta fad'i maganar tana goge hawayan da ya fara zubar mata .

Mahaifiyar Fadila da mamaki ta kalli Aisha ta ce " Ikon Allah , Aisha wai me ke damun Fadila ne ? "

Fadila da sauri ta amshe zance ta kuma cewa " mama , Allah ciwan kai ne da jiri " Daga Mahaifiyar Fadila har Aisha da kallo suka bi Fadila . Sai zuwa can mahaifiyar Fadila ta ce cikin sanyi " Aisha , lafiya wai ? " Aisha kallan mahaifiyarta ta yi ta ce " Mama tunda muka fito chamise din gaba d'aya Aunty Fadika ta rud'e " Tom , ko wani abun ya ce mata ne ? " Mahaifiyar Fadila ta tambaya .

" Da yake ba tare muka shiga ba , na gamu da Aunty zee muna gaisawa ita kad'ai ta shiga "

Mahaifiyar Fadila batare da ta kuma cewa komai ba ta d'akko hijab dinta a daki ta fita . Daga Fadila har Aisha da kallo suka bi ta .

Mahaifiyar Fadila chamise din da su Fadila suka je ta je . Bayan sun gaisa da mai chamise din ne ta tambayeshi abun da ke damun Fadila . Ya bata amsa kamar haka " Mama , gaskiya abisa alamomin yadda ta sanar da ni ciki ne , amma na sanar da ita ta je Asibiti a dubata ta gani "

Mahaifiyar Fadila a rud'e ta dawo gida dan tabbas idan bata manta ba cikin Ahmad ma haka Fadila ta yi , sannan yana yin laulayin nata yana kama da na mai cikin .

Mahaifiyar Fadila lokacin da ta isa gida jikinta ko ina rawa yake . Su Aisha na zaune ita da Fadila da itama har yanzu a rud'e take , ba kamar da mahaifiyarta ta fita ba dake ta k'ara rud'ewa dan tasan chamise din da suka je mahaifiyarta zata .

Mahaifiyar Fadila nuna Fadila ta yi tana cewa " Fadila , gwanne za ki a haihuwar shegen ? Ciki fa aka ce kina da shi , dan babu wata tantama alamun ki gaba d'aya ya nuna na masu ciki , nima so kike ki kasheni kamar yadda kika kashe mahaifinki ? Fadila , mu zaki tozarta a idan duniya ? Tom Ina rok'on Allah ya tsaida wannan tozarcin da kike kok'arin yi mana akan ki ke kad... " Aisha da sauri ta rufe bakin mahaifiyarsu tana kuka ta ce " Mama , dan Allah duk abin da zaki mata ki yi mata amma karki mata baki dan Allah "

Mahaifiyar Fadila kallan Aisha ta yi tana kuka ta ce " Aisha , shi kenan ba zan yi mata baki ba , amma Wallahi idan duniya zata taru akaina bazan zauna da Fadila ba , kodai tabar gidan nan ko kuma ni in bar muku gidan . Aisha , tun yanzu shiga mutane yana naiman gagarata duk in da na yi nunani ake , naga alamar so take ta maida mu abun kwatance a idon duniya gwanne fa Aisha ! Watan Ahmad nawa Aduniya ? "

Usaini wanda ke bima Aisha ma kuka ya sa cikin kukan yana cewa " Wallahi Mama rannan da mu kai fad'a da abokina gori ya yi min wai su gidansu ba a aje abun kunya ba , gaskiya Aunty Fadila , gara ki tafi kawai da ki maida mu abin kwatance a unguwa "

Fadila ko badan kuka ta kasa cewa komai .

Mahaifiyar Fadila ko da yake irin iyayannan ce masu zafi ta ce cikin hargagi " Fadila , ki fita nace ke ba mai son shiryuwa ba ce gwanne acikin shege ? Wallahi ba zan zauna da ke ba ki zo ki fita in bar ganinki ! "

Fadila tashi ta yi jikinta na rawa kota ina ta ce " Mama , ki yi hak'uri ba da sanina ba ne amma zan sanar da ke iya abun da na sani " Bana buk'ar jin komai daga gareki ki ! ki fita kafin in miki illah "

Mahaifiyar Fadila da yake bata iya bacin rai ba ganin Fadila har yanzu bata fita ba , da sauri ta fita sai gata da wata sanda ta shigo , tana shigowa kuma ta yi kan Fadila da ita .

Aisha cikin tsoro da gigita ta rik'e sandar katakam tana kuka ta ce " Mama , dan Allah ki daure ki saurareta ki ji abun da zata ce " Aisha ki sakar min sandata kafin ranki ya b'ace " Fadila ko ta d'are can k'arshen gadonsu tana kuka jikinta ko'ina kakkarwa yake kamar mai jin sanyi .

Aisha cikin kuka ta kuma cewa " Mama , dan Allah ki yi hak'uri kar ki buga mata za ki mata illah fa "

"Shi kenan , na hak'ura amma ta d'auki Ahmad su fita bana son ganinsu duka " Cewar mahaifiyarsu Fadila .

Aisha cikin sanyi ta ce " Mama , dare ne fa idan kika koreta ina zata ? "

Mahaifiyar Fadila cikin b'acin rai ta wanka ma Aisha mari ta ce " Dan ubanki ba zaki sakeni ba , Duk in da zata ta je, ana tattalin abun da bai riga ya lallace bane , wanda kuma ya riga lallace me ye amfanin ? me ye abun tsoro dan ta fita cikin daran ? "
Chapter 20 · 0% Book details