← Book details Fadeelah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 22

Sashe 5

Fadeelah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahaifin Muhammad cikin damuwa ya ce"Muhammad, ka yi hak'uri ,Hafsat ta mutu ta je in da dukkan mu za mu je,dan haka dan ka auri wata ba laifi bane"

Haka alhaji Sagir da hajiya baturiya su ka yi ta yi ma Muhammad nasiha da lallashi a haka suka sa mu ya yi shiru .

D'aya daga cikin gidajan alhaji Sagir ya ba Muhammad in da za su zauna,dan acewar shi ba za'akai Maryam in da akakai Hafsat ba,itama gidanta sabo za a kaita.

Usman abokin Muhammad shi ya jagoranci komai game da d'aukar amarya aka kaita gidanta.

Usman da sauran abokan Muhammad babu yarda ba su yi ba bayan sun kai amarya sun dawo akan Muhammad ya shirya a kaishi gidan amaryar amma ya k'i.Daga k'arshe sai da su ka fad'ama alhaji Sagir.
Alhaji Sagir babu yarda bai yi da Muhammad ba akan ya tashi abokanshi su raka shi,amma ya k'i.Da suka damai ma kuka ya sa musu,hakan ya sa dole suka rabu da shi.

Usman da d'aya daga cikin abokan Muhammad d'in suka koma gidan amaryar.Lokacin ko sun samu kawayan duk sun watse sun barta ita kad'ai.

Ita ko Maryam ta yi sunanin angon ne ma ya shigo,amma sai ji ta yi Usman na cewa"Amarya,ki yi hak'uri za ki kwana ke kad'ai, Muhammad ba shi da lafiya saidai zuwa gobe in sha Allah za ki ganshi.Amma idan kina jin tsoro sai in kai ki gidansu ki kwana "Maryam murmushi ta yi ta ce"Ya jikin na shi?" Alhamdulillah, da sauk'i"Shi kenan,karka damu kanka zan iya kwana ni ka dai babu wata damuwa"

Alhaji Sagir cikin fargaba ya yi barci,duk da ya sa ma'aikatan tsaro sosai a gidan gani ya ke kamar itama Maryam din za a iya yi mata abin da a ka yi ma Hafsat.

Cikin dare alhaji Sagir ya farka a furgice sakamakon mummunan mafarkin da ya yi.
Hajiya baturiya jin tarin alhaji Sagir ne ta farka tana tambayar shi "Alhaji,lafiya kuwa? yanayinka kamar a furgice kake?"Alhaji Sagir jan numfashi ya yi,sannan ya ce kamar zai yi kuka"An kashe Maryam kamar yadda a ka yi ma Hafsa.."Hajiya baturiya katse shi ta yi da cewa"Haba,alhaji mafarki fa ba gaskiya ba ne,na san mafarki ka yi,ka kwanta da tunanin haka ne a ranka shi ne hakan ya zo maka a mafarki, amma in sha Allahhhu babu abin da zai samu Maryam."

Shiru alhaji Sagir ya yi gaba d'aya ya k'osa gari ya waye dan ya je ya dubo 'yar mutane.

Alhaji Sagir na nan zaune har a ka kira sallar asuba.Ana Kira ko ya tashi ya d'auki key d'in motar shi zai fita.
Hajiya Baturiya cikin damuwa ta ce"Alhaji,in sha Allah babu abin da ya samu Maryam,ka daure mu yi sallah sai in raka ka mu je"

Da kyar hajiya baturiya ta shawo kan alhaji Sagir ya yarda su ka yi Sallah.Suna yin Sallah suka fita gidan zuwa D'an maliki road in da aka kai Maryam.

Suna zuwa ma su gadin suka bud'e alhaji Sagir ya shige cike da tarin fargabar abin da idonshi zai gani.

Sun dad'e suna bubbugawa,amma shiru.Hakan sosai ya d'aga hankalin alhaji Sagir da hajiya baturiya. Hajiya baturiya cikin fashewa da kuka ta ce"Mun shiga uku,alhaji kar mafarkinka ya zama gaskiya!"

Alhaji Sagir ya na son ya Kira mahaifin Maryam ya ce ya ba shi numberta ya Kira ya ji,amma kuma yana ganin kamar zai d'aga mai hankali.

Alhaji Sagir ci gaba da bugun k'ofar ya yi,inda kamar daga sama sai ji ya yi an ce"Waye?"Alhaji Sagir cikin jin sanyi aranshin jin muryar Maryam d'in ya ce"My daughter daddynki ne bud'e ko"

Maryam bud'ewa ta yi tana mamakin dalilin zuwan alhaji Sagir da asuba haka.

Alhaji Sagir da hajiya baturiya haka su ka bi Maryam da kalo.

Maryam wadda cikin barci ta ji yo bugun kofar falon,cikin sanyi ta ce"Daddy Allah ya sa dai lafiya na ganku da asuba ko jin Muhammad d'in ne?" Dan ita ta d'auka ko Muhammad ne ma ba lafiya.

Alhaji Sagir cikin sauke bayyanannar ajiyar zuciya ya ce"Maryam, Wallahi wani mugun mafarki na yi hankalina ya k'i kwanciya shi ne dalilin zuwanmu muga lafiyarki"

Murmushin jin dadi Maryam ta yi ganin yarda surukan nata suka nuna kulawa sosai akanta, ta ce"Ayyah,babu komai Daddy,in sha Allah babu abin da zai faru da ni,wancan ma wani rubutaccan al'amari ne"

Alhaji Sagir kai ya jinjina ya ce"Haka ne Maryam.Shi kenan bari mu tafi"

Hajiya baturi cikin marairaicewa ta ce"Ni dai alhaji duk da Maryam ba ita kad'ai bace a gidan hankalina ya fi karka ta akan mu tafi da ita,Allah bashi sai su dawo da Muhammad tare"

Alhaji Sagir cikin gamsuwa ya ce"Haka ne,Maryam d'akko mayafinki mu tafi ,kun dawo anjima da Muhammad tare"

Haka alhaji Sagir suka tasa Maryam su ka tafi da ita.

KADUNA GARIN GWAMNA

A yau jama'ar gasuwar magani ta Kaduna suka tashi cikin tashin hankali saboda rusan kasuwa da a ka yi musu,wanda abin ya had'a harda shagon mahaifin Fadila da ke saida kayan gwari.

Sosai rayuwa ta fara sauya wa su Fadila,inda dama kullum sai an fita kasuwa an nemo suke samun abin da su yi cefane.

Yanzu rayuwa ta fara tsananta wa su Fadila,Yanzu haka yau sun tashi babu abin da za su ci,ga shi kasuwar da aka dogara da ita wadda kullum sai an fita ake samo kudin cefanan abin da za su ci, gashi an rushe kasuwar.

Mahaifin Fadila kwance yana tunanin abin da za su ci,kallan mahaifiyar Fadila ya yi ya ce"Maman Fadila,na ce ko shinkafan nan za a auna a saida a samu kud'in cefanan abin da za mu ci?"
Shiru mahaifiyar Fadila ta yi,sannan ta ce "To,shinkafar ita kasan ta kare saura mudu uku ta rage mana,idan an saida mudu d'aya kaga saura mudu biyu kenan?" Tom,Ya za a yi haka nan za a saida in da za a zauna da yunwa ne?"

Mahaifiyar Fadila ba dan ta so ba haka nan taba yaro ya je ya saida mata mudu daya daga cikin shinkafar da ta yi ragowa,bayan yaron ya dawo ne su ka yi cefanan kayan mahad'in girkin shinkafar.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya,inda ya kasance komai nasu Fadila ya kare,duk wata dabara ta kare.

Yanzu haka tun safe har dare ba su ci komai ba.Mahaifiyar Fadila cikin taushin murya ta fara yi ma mahaifin Fadila magana kamar haka"Baban Fadila,dama cewa na yi inda dai ka ga in rushe maka hanyar da muka dogara da ita,wadda muke ci da sha a cikinta,me zai hana ka yi hak'uri Fadila ta koma aikinta kodan mu samu abin da za mu rik'a ci"

Shiru mahaifin Fadila ya yi kamar ba zai tanka ba sannan ya ce"Shi kenan zan yi tunani akan hakan ✍🏻

📚 FADEELAH 📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

Na
Fadila Sani Bakori

SANARWA: Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban-daban da zan kawo muku na gyaran jiki a cikin wannan littafi mai suna FADEELAH .

Page 4

Yau sati d'aya kenan da maganar komawar aiki da mahaifiyar Fadila ta yi ma mahaifin Fadila , ya ce zai yi shawara amma har yanzu shiru kuma har yanzu da kyar suke samin abin da suke ci.

Mahaifiyar Fadila bayan ta idar da sallah, fadila ta zo ta same ta ta ce"Mama, dama nace ko za ki ma Baba magana in koma aiki Kafin Allah ya kawo mai wata hanyar "

Mahaifiyar Fadila d'ago kai ta yi tana kallan Fadila ta ce"Nima tunanina kenan har magana na yi mai amma ya ce min in saurare shi zai yi tunani, yau sati d'aya kenan amma kin ji shiru sai ka ce baya ganin halin da muke ciki, amma ki bari anjima zan kuma yi mai magana "

Da daddare mahaifin Fadila na zaune yana lazimi ,har lokacin tun kokan da suka sha na safe ne ke cikinsu , Mahaifiyar Fadila ta zo ta zauna gefan abun sallar tashi , sannan zuwa can ganin lazimin nashi ba na kare bane ta ce "Baban Fadila, dan Allah ka bar Fadila ta koma aikinta mana ko dan mu samu abin da za mu rik'a ci, idan kace zaka biye ma maganar mutane Allah mutum ba zai yi abun kirki ba , shi ya sa ka yi abun da ke gabanka kawai , yanzu su mutanan da ke kawo ma maganganin k'arya akanta halinnan da muke ciki cikinsu waya taimaka maka? kuma babu wanda bai san an rushe kasuwarku ba.Wallahi ka toshe kunanka daga maganganun mutane ka barta ta koma ta ci gaba da aikinta mu kuma mu dage mu rakata da addu'a "

Mahaifin Fadila d'ago kai ya yi yana kallan mahaifiyar Fadila kamar ba zai tanka ba sai zuwa can ya ce"Shi kenan ta koma aikin"
Daga jin yarda ya yi maganar kasan dole ce ta sashi furta hakan.

Mahaifiyar Fadia zuwa ta yi ta sanar da Fadila mahaifinta ya amince ta koma bakin aikinta.

Allah sarki Fadila take ta Kira Jamilu abokin aikinta ta sanar da shi gobe zata dawo aiki ,ta k'ara da cewa"Amma Jamilu kana ganin wannan Karan MD zai yarda kuwa? Dan ya kikkira wayata ban d'auka ba, kuma kaga ban tab'a dad'ewa irin na wannan Karan ba ? "

Jamilu dariya ya yi ya ce"Fadila , kema dai kina tonona ne , amma kinsan ko shekara za ki yi biki zo aiki ba kema dai kinsan MD hannu bibbiyu zai amshek ba tare da wani k'orafi ba "

Haka dai su ka yi sallama bacin Fadila ta sanar da shi dawowarta aiki gobe .
Chapter 5 · 0% Book details